MU SHA DARIYA

Matar Babarbare Wani Babarbare ne ya kai matarsa haihuwa asibiti, ta yi yunkurin haihuwa ta kasa; sai likita ya ce wa mijin ya kawo kudi za a yi mata tiyata, a cire dan. Babarbare ba ya da kudi, ya rasa yadda zai samu kudi, sai ya ce wa likita yana so ya yi magana da […]

MU SHA DARIYA

Mu sha dariya

Matar Babarbare

Wani Babarbare ne ya kai matarsa haihuwa asibiti, ta yi yunkurin haihuwa ta kasa; sai likita ya ce wa mijin ya kawo kudi za a yi mata tiyata, a cire dan. Babarbare ba ya da kudi, ya rasa yadda zai samu kudi, sai ya ce wa likita yana so ya yi magana da matarsa. Da ya shiga sai ya yi mata magana a kunne. Fitowarsa waje ke nan sai ta yunkura ta haihu. Likita ya tambaye shi cewa: “Me ka fada wa matarka ne?” Sai ya ce: “Na fada mata cewa, kina haihuwa zan kara aure!”

Daga M. Maishayi, 0816913939

 

Tsoro nake ba ki

Wata rana gari ya yi zafi, wani magidanci talauci ya yi masa zobe; ya rasa inda zai shiga ya samu kudin cefanen rana, balantana na yamma. Ya zaga gari bai samu ba. Ya kama hanya ya dawo gida fuja-fuja, ya kwanta, ya rasa abin da zai ce wa iyalinsa. Jim kadan sai ga matarsa ta kawo masa dambu. Ta ce: “Ga naka.” Ya ce: “Me zan yi da wannan jagwalgwalon naku? Ni ba zan ci ba.” Sai ta ajiye ta yi tafiyarta. Can sai ya mika hannunsa ya damki dambu, ya tura a baka. Yana turawa sai ga matarsa, sai ya yi kokari don ya hadiye amma ina, dambu ya shake masa makogwaro, idanuwansa suka yi turu-turu. Wai don kada ta gane abin da yake ciki, sai ya kara dallo ido, yana cewa: “Tsoro nake ba ki!”

Daga 08034208356

 

Asirin Bahadeje

Wani Bahadeje ne yana zaune da matarsa suna hira, sai ta ce: “Bari in kawo maka abinci ka ci, na ga yanzu ka dawo daga kasuwa. Sai ya ce: “To, uwargida me aka dafa ne yau? Sai ta ce masa shinkafa da miya, sai ya ce: “In ce dai ba a gidan makwabcinmu kika sayo tumatir din ba ko?” Sai ta ce: “Kamar ka sani kuwa, a can na sayo, yaya zan yi?” Sai ya ce: “Ina tsoron ko ya sa guba a cikin tumatir din.” Sai ta ce: “Ai sai da na ba karen gidan nan tukunna na kawo maka maigida. Ya fara cin abincin ke nan sai ’yar aikin gidan ta shigo ta yi sallama ta ce: “Alhaji, maigadi ya ce a fada maka wai karen gidan nan ya mutu.” Nan take Alhaji ya karaya, sai ya ce wa matarsa: “Kafin in mutu zan roki gafararki domin na yi miki laifi, mun haifi yara biyu da ’yar aikin gidan nan.” Sai matar ta ce: “Ni ma ka yi mini gafara, a cikin yaranka 6, guda 4 na maigadi ne, 2 ne kawai naka.” Ana haka sai ga maigadi ya shigo ya ce: “Alhaji, wani ne ya yi sallama a waje yanzu, shi ne yake gaya mini cewa wai a ba ka hakuri, shi ne ya buge karen nan da mota har ya mutu.

Daga, 08169139393

 

Za a yi sanyi

Wani Bahadeje ne ya je wurin budurwarsa, suna cikin hira sai kawai hadari ya taso. Kafin ka ce me, an fara ruwan sama mai karfin gaske. Ganin haka sai baban yarinyar ya fito daga gida, ya ce mata: “Da alamu wannan ruwan ba mai tsagaitawa ba ne, watakila a kwana ana yi. Ki shiga ki gyara masa dakin baki, da safe sai ya tafi.” Nan da nan ta shiga gida ta fara gyara daki, tana gamawa sai suka fito ba su ga Bahadeje ba. Can sai ga shi nan ya shigo a guje, ya jike jagaf. Sai baban ya tambaye shi cewa: “Daga ina haka?” Sai saurayin ya ce: “Gidanmu na je na dauko bargona saboda na san za a yi sanyi cikin dare.”

Daga Nura Suleja, 09027377656