MU SHA DARIYA
Baturen dalibi Wani dalibi ne ya je makaranta a makare, da ya isa ajinsu sai ya iske malamin Ingilishi ne ke ciki yana koyarwa. A ka’idarsa, ya ce idan yana aji duk wanda zai yi magana sai dai ya yi da Ingilishi, idan ya yi da wani harshe za a hukunta shi. Malamin sai […]
Baturen dalibi
Wani dalibi ne ya je makaranta a makare, da ya isa ajinsu sai ya iske malamin Ingilishi ne ke ciki yana koyarwa. A ka’idarsa, ya ce idan yana aji duk wanda zai yi magana sai dai ya yi da Ingilishi, idan ya yi da wani harshe za a hukunta shi. Malamin sai ya tambaye shi da Ingilishi: “What is your name?” (Yaya sunanka). Sunansa na ainihi Sabo Sule, don haka sai ya amsa da cewa: “My name is New Ten Kobo.” Malamin ya sake tambayarsa: “From where are you?” (Daga ina kake)? Daga Karamar Hukumar Kura yake, sai ya amsa da cewa: “I’m from Hyena Local Gobernment.
Daga Khalil Muhammad, 08031908918
Fadan miji da mata
Wani magidanci ne ya samu matsala da matarsa, ta kai fagen ba su ko yin magana da juna. Sun dauki dogon lokaci a haka sai ran nan bukata ta kama mijin, a ma’aikatarsu za a yi musu intabiyu domin karin girma. An nemi su isa ofis da wuri, aka ce duk wanda bai je ofis da karfe shida ba, to ya fadi, ba za a kara masa girma ba. Saboda haka, mutumin nan yana son ya tashi da karfe biyar na asuba, domin ya shirya, kuma ga shi yana son ya gaya wa matarsa ta taimaka ta tashe shi a lokacin. Maimakon ya nemi sasanci da matar tasa sai girman kai ya hana shi. Ya samu takarda ya rubuta cewa: “Don Allah ki tashe ni da karfe biyar na asuba.” Lokacin da ya farka daga barci da safe, ya duba agogo sai ya ga har karfe tara ta yi. Ya buga wani uban tsaki, ya tashi da fushi zai je ya ci zarafin matar tasa, sai ya ga wata takarda kusa da matashin kansa. Da ya dauka ya bude, sai ya ga ashe matarsa ce ta rubuta ta da karfe biyar na asuba. Abin da ta rubuta shi ne: “Ka tashi, yanzu karfe biyar daidai.”
Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011
Dan boko
Wani matashi ne dan karya kuma dan boko, ya kammala karatunsa amma ba aiki; ya yi ta kokarin neman aiki bai samu ba. Wata rana wani manajan kamfani ya ce ya je ya yi masa intabiyu, domin daukarsa aiki. Da ya je, ga abin da ya wakana a tsakaninsu:
Manaja: Mene ne sunanka?
Dan boko: KF.
Manaja: Mene ne KF?
Dan boko: Kabir Faruk.
Manaja: Wane gari kake?
Dan boko: KF.
Manaja: Mene ne KF?
Dan boko: Kwanar Farakwai.
Manaja: Wace unguwa kake?
Dan boko: Ni fa komai KF ne.
Manaja: Mene ne KF?
Dan boko: Kofar Fada.
Manaja: Wace makaranta ka yi?
Dan boko: KF.
Manaja: Me ke nan?
Dan boko: Kwalejin Fasaha.
Manaja: Me ke sana’arka?
Dan boko: KF.
Manaja: Mene ne KF?
Dan boko: Kota da Fartanya.
Dan boko: To yaya labarin KF?
Manaja: Mene ne KF?
Dan boko Labarin Kokarina Fa?
Manaja: To kai ma KF.
Danboko: Ah! Manaja, mene ne kuma KF? Manaja: Ka Fadi.
Daga Buhari Liman
Mai Danwake
Wani Basakkwace ne ya je Kano bakunta sai ya sauka a wani gida mai samari da yawa. Da dare sai aka kawo masu danwake. Samarin sai suka rika hada biyu-biyu, kafin a ankara danwake ya kare, sai wani daga cikin samarin ya tambayi dan Sakkwato cewa: “Ko ka koshi? Ka san danwake sai a hankali.” Sai shi kuma ya ce: “Na aza dambu na, damka dai nakai.”
Daga Abdul’aziz M. Fagge Kano 08034412272