MU SHA DARIYA

In ta zo kan mai Naira 100 ki min magana! Wata budurwa ce ’yar karya ta shiga motar haya da kawarta, suna cikin tafiya, sai ta ce, ita mijin da take so shi ne wanda ya mallaki Naira biliyan daya. Sai kawar ta ce in ba ki samu ba fa? Sai ta ce sai mai […]

MU SHA DARIYA

Mu sha dariya

In ta zo kan mai Naira 100 ki min magana!

Wata budurwa ce ’yar karya ta shiga motar haya da kawarta, suna cikin tafiya, sai ta ce, ita mijin da take so shi ne wanda ya mallaki Naira biliyan daya. Sai kawar ta ce in ba ki samu ba fa? Sai ta ce sai mai miliyan 500. Kawar tana cewa in ba ta samu ba fa, ita kuma tana ragewa. To a kusa akwai wani saurayi, da ya ji ta dawo Naira dubu 500, a ransa sai ya ce wannan fa za ta iya zuwa har gejin kudin da ke jikina tunda rage kudin take ta yi. Sai ya tabo kawarta ya ce: “Kanwata na ji tana ta rage kudin, don Allah idan ta zo kan mai Naira 100, ki yi min magana!”

Haska min in dau takalmina!

Wani Bagobiri ne fada ya hada su da wani Bakatsine dan damben boksin. Bagobiri ya ja baya ya yi tsayuwa irin ta ’yan damben gargajiya, shi kuma Bakatsine ya yi tsayuwa irin tasu. Suna haduwa sai kakau-kau-kau. Da Bagobiri ya ji duka ya yi masa yawa, sai ya ce da abokinsa. “Almu wai cikin masu buguna ba ka rika min guda!” Sai Almu ya ce “Ai mutum guda ka bugunka!” Sai Bagobiri ya ce “Yanzu wannan bugu, bugun mutum gudana?” Almu ya ce “Awo shi na!”

Bagobiri ya ce “To haska min in dau takalmina!” Almu ya ce “Ho aiki ya baci, ai rana ce ba dare ba!”

 

Ka gama kawai ka ba ni kwanona!

Wadansu samari ne suka je wajen taro suka kwana, da gari ya waye aka kawo shayi don su karya kumallo, kowa ya dauki kofi aka zuba masa. Sai dayansu ya rage bai samu kofi ba. Ga shi yana jin yunwa ba zai iya jira wani ya gama ya ba shi kofi ba. Sai ya hango wani kwano a wanke ya dauko ya bayar aka zuba masa, ya koma gefe yana sha. Har ya yi kusan gamawa sai ya dago kansa ya ga wani kuturu a gefensa. Ya kalli kuturun cike da kyama ya yamutse fuska, ya ce don Allah Malam a kara gaba! Kun san kuna da irin wannan cutar sai ku rika rabar jama’a. Sai kuturu ya ce masa “Aikin banza ni ba shayinka zan sha ba, jira nake ka gama kawai ka ba ni kwanona!”

Labarai daga 09099886988

 

Su Baba an iya loma amma ba a iya kai nika ba!

Wani yaro ne ya dawo gida ya samu mahaifinsa yana cin abinci. Sai ya dubi mahaifin ya ce, “Su Baba an iya loma amma ba a iya kai nika ba!”

Daga Ummu Safiyya, 08105657565

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos