MU SHA DARIYA
Babarbare a Makka Wani Babarbare ne ya je jifar Shaidan sai ya koma gefe yana ta kuka. Sai wani Bafillatani ya tambaye shi cewa: “Danborno kukan me kake yi?” Sai ya ce masa: “Wallahi Shaidan ne, na jefe shi, na jefe shi, amma ya ki yin kuka. Don haka jifar tawa ba ta yi ba!” […]
Babarbare a Makka
Wani Babarbare ne ya je jifar Shaidan sai ya koma gefe yana ta kuka. Sai wani Bafillatani ya tambaye shi cewa: “Danborno kukan me kake yi?” Sai ya ce masa: “Wallahi Shaidan ne, na jefe shi, na jefe shi, amma ya ki yin kuka. Don haka jifar tawa ba ta yi ba!”
Daga Musa Kaliyos Kofar Yamma, Dambatta.
Aradu sai na shi biyu
Wani Bafulatani ne kullum matarsa ta je gari tallar nono, idan za ta dawo sai ta sayo kosai, idan ta zo sai ta raba guda daya ta mika masa rabi. Bai taba cin kosai daya ba shi kadai, sai dai rabi. Ran nan sai ya yi zuciya ya kama karsana ya kai kasuwa ya sayar. Yana amsar kudin, sai ya kai wa mai tuyar kosai kudi saniyar gaba daya, ya dauki kosai biyu ya zura a guje yana cewa: “Aradu yau sai na ci biyu.” Ana ta kiransa cewa ya zo ya amshi kudinsa, shi kuwa sai cewa yake “Aradu yau sai na shi biyu!”
Daga Isma’il Mai Shadda Legas, 07032775928
Buhari ya ruwaito
Wani Badaheje ne yana zuwa wajen malaminsa daukar karatun Hadisi, sai ya je ranar farko aka yi karatu ya ji an ce Buhari ne ya ruwaito. A rana ta biyu ma haka, da ya je a rana ta uku, sai ya ji an kara cewa Buhari ne ya ruwaito. Sai ya ce wa malamin: “Shin wai shi Atiku ba ya ruwaito Hadisi ne?”
Daga Musa Baban Amina Gala
Raba gardama
Wadansu Nufawa ne su biyu da ba su taba zuwa birni ba, ran nan sai dalili ya sanya suka ziyarci cikin gari. Suna cikin tafiya a birni sai wani bawan Allah ya ba su ledar fiya-wata daya mai sanyi, sai suka rasa yadda za su yi su raba ruwan. Sai daya daga cikinsu ya zaro wuka ya ce da abokinsa: “Rike gefe daya nan ka ga ni.” Da ya rike, sai shi ma ya rike gefe daya, ya sanya wukar da ke hannunsa ya yanka ledar, kawai sai ruwan ya zube.
Daga Garba Sabiyola Gashuwa, 07061636664
Markade na kawo!
Wani barawo ne da ya shahara a sata, wata rana ya auka wani gida da misalin karfe biyu na dare da nufin yin sata. Ga duhu ko’ina. Da shigarsa, sai ya nufi can cikin gidan, bayan shigarsa, sai ya ga ko tafin hannunsa ba ya gani. Sai ya fara laluben bangon gidan. Can sai ya ji makunnin wutar lantarki, sai ya fara murna. Da kunnawarsa sai injin markade ya fara kara, sai masu gidan suka tashi a fusace suka ce: “Wane ne?” Sai barawo ya gigice ya ce: “Markade na kawo!”
Daga Abdulbasir Abubakar Tingilin Malumfashi, 08099025522