MU SHA DARIYA
Kowa zai samu Wani marokin Babarbare ne ya tashi da safe, sai ya ga ashe ya makara kuma ga shi an gayyace shi radin suna. A garin ya yi sauri don kada wani ya riga shi amsar raba goro sai ya sanya jallabiya, ya mance ya saka wando. Yana isa aka ba shi goro domin […]
Kowa zai samu
Wani marokin Babarbare ne ya tashi da safe, sai ya ga ashe ya makara kuma ga shi an gayyace shi radin suna. A garin ya yi sauri don kada wani ya riga shi amsar raba goro sai ya sanya jallabiya, ya mance ya saka wando. Yana isa aka ba shi goro domin ya raba wa jama’a. Ga shi babu farantin zuba goron, sai ya tarba jallabiyarsa aka zuba masa goro, alhali bai san babu wando a jikinsa ba. Duk inda ya mika goro sai a rika ce masa: “Malam gabanka fa!” Sai shi kuma ya rika cewa: “Ku yi hakuri, kowa zai samu!” Su kuma mutane na nufin rufe al’aurarsa.
Daga Nasir Ibrahim Buhari, Katsina
Rainin wayo
Wani dan tasi ne ya dauko wani Bature daga ofis, suna cikin tafiya sai suka biyo ta wani dogon bene kerarre, ginin ya yi kyau sosai. Baturen dama ya iya Hausa, sai ya ce da direban: “Kai! Ginin nan ya yi kyau, a kwana nawa aka gina shi? Sai direban ya gyara zama, ya ji an yabi abin kasarsu, ya ce: “Ai benen a shekara biyu kacal aka yi aka kammala shi.” Bature ya yi tsaki ya ce: “A Amurka a wata shida za a gina wannan. Ku dai Afirka komai sai a hankali.” Dan tasi ashe ya ji haushin Bature, suna biyo wani titi sai ga wani katafaren filin kwallon kafa na zamani, sai Bature ya kara tambayar lokacin da aka diba wajen gina shi. Sai dan tasi sai ya ce: “To ni dai dazu da na wuce babu wannan sitadiyum amma yanzu ga shi har an gina shi. Ina ganin dazu da safe aka gina shi.” Sai Bature ya juyo da dan Turancinsa a fusace ya ce: “Hey! Ka ga malam, kada ka raina mini hankali. Yaya za ka ce a rana daya aka gina sitadiyum? To ko mu a can Turai ana daukar kamar shekara biyu ko uku kafin a gina!”
Daga Buhari Liman Kudan
Gasar gudu
Wani matashi ne ya saba da gudu a babur, ran nan ya tafi wurin aiki mai nisan kilomita 25. Ya yi tafiyar da ta kai kilomita 23, saura kilomita biyu ya isa, kawai sai suka yi kiliya da wani matashi yana tika gudu a nasa babur. Yana ganin wannan matashi da ke gudu sai ya yi kwana ya bi shi. Da wancan ya waigo ya ga an biyo shi da gudu, sai ya kara wuta, domin bai son a wuce shi. Nan fa suka runtuma, suka yi ta gasar tsere a tsakaninsu. Sai da suka ci kilomita 20, sannan ya samu wuce shi, daga nan ya juyo domin tafiya wajen aikinsa. Ya ce: “Haba, ai da ban wuce shi ba, sai ya yi ta kurin shi mai gudu ne!”
Sunusi Uban Kulob Garko Kano 07038766018
Keken Banufe
Wani manomi Banufe ne da yake tare da dansa, suna aikin gona. Da ya ga gyadarsa ta yi kyau sosai, sai ya ce wa babban dan nasa: “Bana zan sayi keke.” Dan nasa sai ya ce: “Ni kuwa zan kada karaurawa ke nan.” Jin haka sai baban ya kai masa mari, ya ce masa: “Kana son ka bata mini keken ne?”
Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011