MU SHA DARIYA
Ciwo ko yunwa? Wani Bakano ne mai makon tsiya, ya dauki hajarsa ya tafi cikin gari talla. Tunda safe har zuwa La’asar bai ci komai ba. Ya yi ciniki mai yawa kuma ya samu riba, amma ya dawo gida haka nan. Yana zuwa yunwa ta buge shi ya fadi, aka yi ta ba shi magani, […]
Ciwo ko yunwa?
Wani Bakano ne mai makon tsiya, ya dauki hajarsa ya tafi cikin gari talla. Tunda safe har zuwa La’asar bai ci komai ba. Ya yi ciniki mai yawa kuma ya samu riba, amma ya dawo gida haka nan. Yana zuwa yunwa ta buge shi ya fadi, aka yi ta ba shi magani, amma da ya sha sai ya amayar. Can sai wani Bazamfare ya ankara cewa yunwa ce ke damunsa, sai ya ce wa iyalin Bakano: “Kun ba shi fura kuwa?” Sai Bakano da ke kwance cikin ciwo ya daga kai ya ce: “Yo sun yi wannan dabarar kuwa?”
Daga Amina Umar Gummi, 08060322272
Sabon malami da dalibansa
Wani sabon malami ne aka kawo shi wata makarantar sakandare, domin ya koyar da Tarihi. Shigarsa aji ke da wuya sai ya ce da wani dalibi: “Tashi tsaye, shin wa ya kashe Murtala Ramat Mohammed?” Dalibin ya ce: “Malam, ban sani ba wallahi.” Sai ya tambayi dalibi na biyu, shi kuma sai ya ce: “Malam, ranar da aka kashe shi ban zo makaranta ba.” Dalibi na uku kuma ya ce: “Wallahi ni sabon zuwa ne makaranta ne.” Malamin ransa ya baci, sai ya kira shugaban makaranta, ya gaya masa abin da ya faru, sai shugaban makaranta ya tambayi ’yan ajin baki dayansu, suka ce ba su sani ba. Sai shugaban makaranta ya juyo, ya ce da malamin: “Kai malam, ka tabbata da gaske a nan ajin aka kashe Murtala Ramat Mohammed?”
Mu koma gobe mu dawo!
Wadasu mahaukata ne ake jinyarsu a asibitinsu. Ran nan sai suka hada kai suka ce idan dare ya yi, za su yi wa maigadin kofar asibitin dukan tsiya, su dauke mabudin su gudu. Da lokacin ya yi, sai suka sadado zuwa bakin kofa da nufin shammatar maigadin. Abin mamaki sai suka iske kofar a bude fayau, kuma babu maigadi. Sai daya daga cikin mahaukatan ya ce da sauran: “Aikin banza, shirinmu ya lalace, ga shi maigadin ma ba ya nan, kuma kofar a bude. Mu koma ciki, gobe ma dawo mu aiwatar da shirinmu na guduwa, idan maigadin ya dawo.”
Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011
Tashi ka bi su!
Wani Bakano ne ya kira dansa da ke karatu a jami’a. Ga yadda hirarsu takasance: Baba: Musa, kana ina ne yanzu haka? Yaro: Baba, ina dakin makaranta a kwance. Baba: Madalla! Na ji ana ce dalibai suna ta zanga-zanga da kone-kone a makarantarku, to wallahi kada ka kuskura ka bi su ka san dai irin tarbiyyar gidanku. Yaro: Idan Allah Ya yarda ba zan bi su ba baba.” Baba: Yauwa dan arziki sai an jima. Bayan minti 15, ya sake kiran yaron ya ce da shi: “Wai mene ne dalilin yin zanga-zangar? Yaro: Wai saboda hukumar makaranta ta kara mana kudin makaranta daga Naira dubu 30 zuwa Naira dubu 300. Baba: Iye! Yanzu kai kana ina? Yaro: Ina kwance a daki. Baba: Ashe kai mahaukaci ne? Tashi ka bi su!
Daga Malam Babaji Na-Ummi Hadeja, 08108484300