MU SHA DARIYA

Shirmen makiyayi Wani Bafulatani ne ya yiwo canjin tsabar kudi, yana cikin tafiya sai daya ta fado daga aljihunsa. Koda ya ga haka sai ya ce: “Oya, dama kuna tafiya kuke ba ni wahala?” Sai  ya watsar da sauran, ya ce: “Ku tarar da ni a ruga.” Daga Hafizu Wanka Kano, 09030400620     Gadin […]

MU SHA DARIYA

Mu sha dariya

Shirmen makiyayi

Wani Bafulatani ne ya yiwo canjin tsabar kudi, yana cikin tafiya sai daya ta fado daga aljihunsa. Koda ya ga haka sai ya ce: “Oya, dama kuna tafiya kuke ba ni wahala?” Sai  ya watsar da sauran, ya ce: “Ku tarar da ni a ruga.”

Daga Hafizu Wanka Kano, 09030400620

 

 

Gadin gawa

Wani mai gadin makabarta ne  aka kawo gawarwaki  uku aka aje dakin ajiye gawa. Da aka zo daukar gawa daya daga cikin ukun, sai ya shi ga ya bude masu kofa suka dauka.  Shi kuma sai ya koma ciki, domin ya gyara sauran, a wurin fitowa sai kofa ta rike masa riga. Maimakon ya juya ya ga abin da ya kama rigar, sai ya yi tsammanin ko gawa ce ta rike masa riga. Nan sai ya kama ihu da kururuwa kuma ya ki waigawa ya ga abin da ya kama masa rigar.

Daga Hussaini Sunshine Birnin Gwari, 08032824939

 

 

Hawan rakumi

Wani Bahadeje ne ya je wurin wani malami domin a yi masa fassarar mafarki, ya ce: “Malam na yi mafarkin na hau rakumi.” Sai Malam ya ce masa: “Za ka shiga Aljanna.” Bahadeje ya ji dadi, sai ya ci gaba da cewa: “Ai Malam in gaya maka, har ga tozonsa na je.” Jin haka sai Malam ya ce: “Ka wucee Aljanna, ka shiga wuta.” Sai ya ce: “To, ai da na je sai na zamo kasa.”

Daga Musa Uke Karu, 08051702591

 

 

Dan baiwa

Wani mahaukaci ne ana duba tsayuwar watan Azumi, babu wanda ya gani, sai ya ce: “La, ga wata!” Sai aka ce: “Kai, lallai wannan mutumin dan baiwa ne.” Shi kuma da ya ji an yabe shi sai ya ce: “Ku duba nan, ga wani watan can ma, har yau ma ga wani can!”

Daga Sani Ibrahim, 08076231488

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos