MU SHA DARIYA
An sayar kamar yadda ka sayo! Wata rana wani barawo ya sato kaya sai ya ba matarsa ta kai kasuwa ta sayar. Da ta je kasuwa sai aka sace kayan, ta dawo gida ta samu mijinta a cikin jama’a suna hira. Ya ce mata: “An sayar da kayan?” Sai ta ce: “An sayar kamar yadda […]
An sayar kamar yadda ka sayo!
Wata rana wani barawo ya sato kaya sai ya ba matarsa ta kai kasuwa ta sayar. Da ta je kasuwa sai aka sace kayan, ta dawo gida ta samu mijinta a cikin jama’a suna hira. Ya ce mata: “An sayar da kayan?” Sai ta ce: “An sayar kamar yadda ka sayo.” Sai ya ce: “Babu riba ke nan.”
Daga Barde Gidan Gebi, Zango Bauchi
Tsaka-mai-wuya
Wata budurwa ce za ta shiga wanka, daga ita sai zane daurin kirji a jikinta. Ta dauki bokiti ta nufi bayi, kafin ta shiga sai ta ji ana ta hayaniya a kofar gidansu. Sai ta ajiye bokitin ta leka waje, sai ta ga ashe yayarta ce, wacce aka yi aurenta shekara daya da rabi da suka wuce, amma ba ta zo ganin gida ba sai yau. Nan take murna ta kama budurwar, ta mance halin da take ciki na daurin kirji, ta fita ta tarbi yayarta kuma ta karbi danta jariri; ta fara wasa da shi. To, irin wasan da mata suke yi wa yara, sai ta wulla yaron sama, kafin ya dawo ta cafke shi sai zanenta ya kwance. Nan fa ta rude, shin ta zanenta za ta yi ta rufe jikinta ko ta yaron da ta jefa sama?
Daga Umar Adamu Isah, 08064385252
Hikimar ango
Wani ango ne ana walimar bikinsa, ’yan uwa da abokan arziki duk sun taru. Bayan an kammala sai aka ce ango ya tashi ya yi jawabin godiya. Ango ya ce: “Godiya ta musamman ga Malam Sani Tudun Kaure Dillalin Gidaje, wanda ya ba mu aron inda za mu zauna, kafin mu samu haya. Ba zan taba mantawa da Hajiya Shafale Mai’adashi ba, wadda ta ba ni daukar farko na kai kudin aure. Godiya ga Asabe Dillaliya, wadda ta ba mu bashin atamfofi da shaddoji da muka sa a lefe. Allah Ya saka wa kanwata Habiba da taimakonta ne na fita kunya don kuwa ita ce ta ba ni aron akwatunan lefenta, aka sa kayan a ciki. Allah Ya bar zumunci, Ya ba mu ikon cika alkawuran da muka dauka. Haka kuma ba zan manta da Atiku Mai-Wanki-da-Guga ba, shi ya ba ni aron kaya har na fita kunya. Mun gode, Allah Ya maida kowa gidansa lafiya.”
Daga Jibrin M.D. Lafiya, 08133477778
Ta nawa kuma yaro?
Wani kuturu ne yana tafiya dingis-dingis, sai ya ture kwanon tallar wani yaro kayan talla suka zube a kasa. Kuturu ya wuce bai ce da yaro komai ba. Sai yaron ya waigo ya ce: “Kuturu Allah Ya tsine maka!” Sai kuturun ya masa da cewa: “Yaro tsinuwa kuma ta nawa?” Wato tunda aka yiwo shi kuturu ai an gama tsine masa.
Ba shanshani ya yanka ba! Wani Sarkin Fawa ne yana gyara ragon layyar wani Sarki, sai aka turo Jakadiya cewa idan Sarkin Fawa ya gama gyaran a kai wa Yarima karfata daya, Galadima daya, Madaki daya, kafin ta karasa sai Sarkin Fawa ya ce, “Ke ki je ki gaya wa Sarki ba shanshani ya yanka ba.
Daga Salihu Makera 07086866165