MU SHA DARIYA

Akasi Wani mutum ne yana cikin otel, sai ya duba dakin da ya sauka, sai ya ga akwai kwamfuta. Saboda haka sai ya hau domin ya mika sako ga matarsa ta I-mel. To ashe ya yi kuskuren shigar da sakon zuwa ga wani adireshin, wanda ba na matarsa ba ne, na wata matar ce daban, […]

MU SHA DARIYA

Akasi

Wani mutum ne yana cikin otel, sai ya duba dakin da ya sauka, sai ya ga akwai kwamfuta. Saboda haka sai ya hau domin ya mika sako ga matarsa ta I-mel. To ashe ya yi kuskuren shigar da sakon zuwa ga wani adireshin, wanda ba na matarsa ba ne, na wata matar ce daban, wacce mijinta ya mutu a daidai lokacin, domin a lokacin ma ba a fi awa biyu da kai shi makwancinsa ba. To sai matar nan ta hau kwamfuta domin ganin sakonnin ta’aziyyar da aka aiko mata. Tana gama karanta sako na farko sai masu amsar gaisuwa da ke tare da ita suka ga ta fadi a some. Suna duba fuskar kwamfuta, sai suka ga sako kamar haka: “Zuwa ga matata. Na san za ki yi mamakin ganin wannan sakon nawa. To, ba abin mamaki ba ne, domin gaskiya wurin yana da kyau saboda akwai duk wani abin more rayuwa, har da kwamfuta da kayan alatu. Saboda haka ke ma na gama shirya miki komai, saboda gobe za ki biyo ni, domin mu ci gaba da zama tare…” Su ma masu ta’aziyya suna gama karantawa sai gudu.

Daga Umar Adamu Isah, 08064385252

 

Shirmen makiyayi

Wani Bafulatani ne ya yo canjin kudi na tsaba, yana cikin tafiya sai daya ta fado daga aljihunsa. Koda ya ga haka sai ya ce: “Oyyo, dama kuna tafiya kuke ba ni wahala?” Sai  ya watsar da sauran, ya ce: “Ku tarar da ni a ruga.”

Daga Hafizu Wanka Kano, 09030400620

 

Hawan rakumi

Wani Bahadeje ne ya je wurin wani malami domin a yi masa fassarar mafarki, ya ce: “Malam na yi mafarkin na hau rakumi.” Sai malam ya ce masa: “Za ka shiga Aljanna.” Bahadeje ya ji dadi, sai ya ci gaba da cewa: “Ai malam in gaya maka, har ga tozonsa na je.” Jin haka sai malam ya ce: “Ka wucee Aljanna, ka shiga wuta.” Sai ya ce: “To, ai da na je sai na zamo kasa.”

Daga Musa Uke Karu, 08051702591

 

dan kamasho

Wani dan hayis ne idan ya je tashar mota, kullum aka loda masa fasonja, ba ya ba ’yan kamasho hasafi, kamar yadda sauran direbobi ke yi. Wata rana ya cika motarsa da fasinja, har ma ya fara shirin tafiya, sai dan kamasho ya zo motar ya yi wa fasinjojin sallama, bayan sun amsa, sai ya ce musu: “Dama wani dan jawabi ne nake son yi maku, saboda duk abin da ya faru da ku a hanya, wajenmu za a dawo, don haka ina sanar da ku cewa direban motar nan yana da cutar farfadiya, don haka duk wanda ya ga zai amince ya hau, ruwansa, duk abin da ya faru kada a yi kuka da mu!” Rufe bakinsa ke da wuya sai fasinjoji suka yi ta fita daga motar, kafin ka ce wani abu, kowa ya kama gabansa.