MU SHA DARIYA
Natsuwa ta zo? Wani mutum ne kullum ya je gidan giya sai ya sha kwalba uku, wata rana sai mai gidan giyar yake tambayarsa: “Wai me ya sa kowa yana shan daya amma kai kake shan uku?” Sai ya ce ai sun yi alkawari shi da abokansa biyu, daya yana kasar Indiya, dayan kuma a […]
Natsuwa ta zo?
Wani mutum ne kullum ya je gidan giya sai ya sha kwalba uku, wata rana sai mai gidan giyar yake tambayarsa: “Wai me ya sa kowa yana shan daya amma kai kake shan uku?” Sai ya ce ai sun yi alkawari shi da abokansa biyu, daya yana kasar Indiya, dayan kuma a kasar Rasha, duk wanda zai sha giya sai ya sha wa ’yan uwansa. A kwana a tashi, rannan sai ya zo ya sha kwalba biyu, sai mai gidan giyan ya tambaye shi cewa a cikin abokan nasa wanne ne ya mutu? Sai ya ce: “Ba kowa, ni ne dai Allah Ya shirye ni, ta su kawai nake sha.”
Tsuntsuwar gida
Wani yaro ne da mahaifiyarsa suke tattaunawa, kamar haka:
Yaro: Mama ina da tambaya. Mama: Mece ce tambayarka? Yaro: Wai Ladi ’yar aikin gidan nan tana da fiffike? Mama: (Dariya), me ka gani? Yaro: Jiya da baki nan sai na ji Baba yana ce mata “Ladi tsuntsuwar zuciyata.” Yana ta zuga ta, ita kuma tana dariya. Mama: kwarai da gaske tana da fiffike, domin yau-yau din nan za ta tashi ta koma kauyensu.
Labarai daga Mudassir Mai Shayi Ningi, 09025297045
Darasi a mota
Wata rana wani mutum ya sayo sabuwar mota kirar Jeep, an rubuta 4d4 a jikin motar. Wani malamin makaranta mai tabin hankali sai ya zo wucewa ya gani, kawai sai ya ce: “Kai wadannan wadanne irin tsofaffin dakikai ne, har yanzu ba su gane amsar nan ba?” Sai ya dauko kusa ya rubuta 16 a jikin motar. Da mai mota ya gani sai ya yi ta fada, ya je ya sa aka goge, aka gyara wurin. Wata rana mahaukacin ya dawo ya ga an gyara, sai ya sa kusa ya sake rubuta 16. Mai mota ya ga haka sai ya canja shawara, ya je wurin masu zane aka rubuta 16 da kyawun rubutu don kar a sake bata masa mota. Sai mahaukacin ya dawo ya ga an rubuta amsa daidai sai ya dauko kusa ya ce: “Ya ce ashe sun gane.” Sai kawai ya rubuta bery Good a jikin motar.
Kadan-kadan
Wata rana ne aka hada baki da mai sayar da shayi aka ba wani kurma shayi mai zafi. Da ya yi kurbar farko, sai ya watsar, cikin dimautar zafi sai ya ce: “A fafi (Da zafi).” Mutanen da ke wurin wadanda kuma da su aka shirya wa kurman nan shakiyanci, suka kama baki don mamaki, suka kalle shi baki bude, suka tambaye shi cewa: “Ashe da ma kana magana?” A take sai kurman ya zaro idanu yana kallonsu, ya ba su amsa da cewa: “Kadan-kadan!”
Labarai daga Nasiru Kainuwa Hadeja, 08100229688