Mu Sha Dariya: Babu shaida

Wani Bahadejen dan sanda ne ya kama wani a dakin bahayar wani otel, ya same shi da kullin tabar wiwi guda uku. Ga yadda ta kwashe a tsakaninsu: Mashayi: “Ba ni da laifi, a kullum na zo dakin bahayar nan, idan na nemi kore su sai kawai in ga sun fada aljihuna. Abin kamar na […]

Mu Sha Dariya: Babu shaida

Jami’in dan sanda

Wani Bahadejen dan sanda ne ya kama wani a dakin bahayar wani otel, ya same shi da kullin tabar wiwi guda uku.

Ga yadda ta kwashe a tsakaninsu:

Mashayi: “Ba ni da laifi, a kullum na zo dakin bahayar nan, idan na nemi kore su sai kawai in ga sun fada aljihuna. Abin kamar na jinnu.”

Bahadeje: “Ka dauke ni wawa ne, kana son in amince da wannan karyar?”

Mashayi: “Bari in tabbatar maka da gaskiyata.”

Bahadeje ya mika wa Mai Laifi wiwin da ya kwace daga wurinsa, ya ce masa: “To tabbatar mani, in gani.”

Koda ya amsa sai ya zuba su a tukunyar kora kashi, ya danna ruwa suka bace.

Ganin haka sai Bahadeje dan sanda ya ce: “To, nuna mani aljihunka in ga yadda wiwi ta koma.

Shi kuwa mai laifi ya ce: “Wace wiwi kuma?”

Daga nan ne sai dan sandan ya fahimta ashe wayau ya yi masa.

Ga shi yanzu bai da damar kama shi, tun da babu shaida.

Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos