Mu Sha Dariya: Kyautar mota
Shi ma kalangun an ba shi mota.
Wani mahaukaci ne ya sha shadda mai kyau kamar mai hankali, ya je daurin aure sai ya ga wani mai kalangu yana yi wa mutane kirari ana ba shi kudi.
Ya ce wa mai kalangu: “Ni ma jinin sarauta ne, ya kamata ka yi mini kida.”
Mai kalangu da yaransa hankalinsu ya koma kan maukacin nan, suka rude da kida suna cewa: “Dan sarki jikan sarki.”
Mahaukaci ya ce wa mai kalangu: “An ba ka mota, yaranka su ma an ba su mota.”
Mai kalangu ya ce: “Yaushe za mu je mu amso?”
Ya ce musu sai ranar da kalangu ya fashe.
Nan take mai kalangu ya sa wuka duk ya fasa kalangunansa.
Mahaukaci ya ce: “Shi ma kalangu an ba shi mota.”
Mai kalangu ya ce: “Amma Malam ba ka da hakali ko?”
Mahaukaci ya ce: “Hankali shi ma an ba shi mota.”
Mai kalangu ya ce: “Malam Allah ba ka lafiya.”
Mahaukaci ya ce: “Lafiya ita ma an ba ta mota.”
Daga Ahmad Muhammad Amoeba, Kano