Mu Sha Dariya: Uwargida da amarya
Wallahi ba ni nake ba ta ba amma kada ki damu, zan dauki mataki.
Wata mata ce da kishiyarta, kullum idan kwananta ya zo ta shiga dakin mijinta sai ta fito da kudi tana kirgawa a gaban uwargida, ta ce mijin ne ya ba ta.
Wannan abin ya ishi uwargida, sai ta kai korafi ga mijinsu, ta ce masa “Ni fa ban gane ba, kullum idan amarya ta fito daga dakinka sai in ga ta fito da kudi amma ni ranar girkina ba ka ba ni.
“Mene ne dalilin haka?”
Sai mijin ya ce mata, “Wallahi ba ni nake ba ta ba amma kada ki damu, zan dauki mataki.”
Bayan kwana biyu, girkin amarya ya zagayo, ta fito daga dakin mijin, kamar yadda ta saba tana yanga tana kirga kudi a gaban uwargida.
Daidai lokacin sai mijin ya leko ta tagar dakinsa ya ce, “Uwargida ga kudi nan na ba amarya, ku raba.”
Nan take idon amarya ya raina fata, ashe kudin adashi ne da aka ba ta ajiya take kirgawa don ta bai wa uwargida haushi.
Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011