Mu tsaftace sana’armu ta yin gaskiya – dan kasuwa Junaidu Shehu
Wani dan, Alhaji Junaidu Shehu Sakkwato ya shawarci daukacin mahauta ’yan uwansa masu sana’ar yanka da sayar da nama da cewa su kula da sana’ar kuma su rika yin gaskiya, domin a cewarsa sana’ar halaltacciya ce kuma tana da tushe, idan aka tsaftace ta za a samu albarka da rufin asiri a ciki.Ya yi wannan […]
Wani dan, Alhaji Junaidu Shehu Sakkwato ya shawarci daukacin mahauta ’yan uwansa masu sana’ar yanka da sayar da nama da cewa su kula da sana’ar kuma su rika yin gaskiya, domin a cewarsa sana’ar halaltacciya ce kuma tana da tushe, idan aka tsaftace ta za a samu albarka da rufin asiri a ciki.
Ya yi wannan furucin ne a wata hira da Aminya, a inda yake gudanar da sana’arsa ta sayar da nama a kasuwar Ni’ima, Sabongari Edokpar, karamar Hukumar Uhonmwode, Jihar Edo.
“Wannan sana’ar tana da muhimmanci kwarai da gaske domin samar da tsaftataccen nama ba karamin taimako ba ne ga kasa kuma idan aka yi la’akari da kudin shiga da gwamnati take samu a bangaren sana’ar ba kadan ba ne, wanda yana taimaka wa tattalin arzikn kasa.” Inji shi.
Ya kara da da cewa: “Dalilin haka nake kira ga gwamnatin Jihar Edo da ta Tarayya a kan tallafa wa masu wannan sana’ar, domin ci gaban kasa baki daya; domin ina ganin muddin suna samun tallafi daga gwamnati to lallai sana’ar za ta bunkasa kuma za a daina bukatar shigo da rubabbun nama daga waje.”
Ga ’yan uwansa mahauta kuwa, dan kasuwar ya shawarce su da su rika kwatanta gaskiya da biyan basussuka da suke dora wa kansu.