Mu waiwayi Wakar Bawa Direba ta marigayi Mamman Shata

A kwanakin baya ne fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Sadik Sani Sadik ya gudanar da bikin murnar lashe kyautar Gwarzon Jarumi na Kannywood Awards.Bikin wanda ya samu halartar daruruwan masu ruwa da tsaki a masana’antar fina-finan Hausa, an gudanar da shi ne a dakin taro na Ellies Multipurpose Hall da ke unguwar Rayfield a Jos.An fara […]

Mu waiwayi Wakar Bawa Direba ta marigayi Mamman Shata
Mu waiwayi Wakar Bawa Direba ta marigayi Mamman Shata

A kwanakin baya ne fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Sadik Sani Sadik ya gudanar da bikin murnar lashe kyautar Gwarzon Jarumi na Kannywood Awards.
Bikin wanda ya samu halartar daruruwan masu ruwa da tsaki a masana’antar fina-finan Hausa, an gudanar da shi ne a dakin taro na Ellies Multipurpose Hall da ke unguwar Rayfield a Jos.
An fara bikin ne ta hanyar buga wasan kwallo tsakanin ’yan fim din Kano da kuma na Jos a filin wasa na Rwang Pam Stadium da ke Jos, inda ’yan fim din Jos suka casa na Kano da ci 1 da 0.
Jarumi Sadik ya buga wa ’yan fim na Kano, inda Jamila Nagudu ta kasance kocin kulob din, yayin da kuma jarumi Hamza Talle Maifata ya kasance kocin ’yan fim na Jos.
’Yan fim da suka buga wasan sun hada da Bashir Lawandi Datti da Haruna Talle Maifata da Ibrahim Isa da Bello Muhammad BMB da Kamilu Jankasa da sauransu.
A daren ranar ne aka yi dina a dakin taro na Ellies, inda daruruwan ’yan fim suka halarta. Mawaka irin Ahmad Maishanawa da Fati Nijar da Ado Gwanja da sauransu suka nishadantar da taro.
A yayin bikin, jarumi Sadik Sani Sadik ya rika taka rawa da fitattun jarumai mata irin su Nafisa Abdullahi da Jamila Nagudu da sauransu inda aka rika yi musu liki.
A lokacin da jarumin yake bayani a wurin taron, ya bayyana cewa ya shirya taron ne don ya nuna godiyarsa ga Allah (SWT) da Ya ba shi damar zama gwarzon jarumi sau biyu a jere.
“Na shirya wannan gagarumin baki ne don in gana da masoyana don kuma in nuna farin ciki da godiyata ga Allah (SWT) da Ya ba ni damar zama Gwarzon Jarumi na gasar Kannywood Awards sau biyu a jere. Ina so mutane su fahimta ba wai wayo da dabarata ba ne suka ba ni wannan nasarar, nasara ce daga Ubangiji.” Inji shi.
Jarumin ya yi wa masoyansa addu’ar alheri, dalilin irin soyayyar da suke nuna masa, sannan ya kuma kira da masoyan nasa su ci gaba da yi masa fatan alheri hade da sanar da shi kura-kurensa don ya gyara.
Ya ce: “Allah Ya saka wa masoyana da alheri, domin ina ganin fa’idar addu’arsu gare ni. Ina fata za su ci gaba da yi mini addu’a, sannan su rika sanar da ni duk wani kuskure da suka ga na aikata don in gyara. Ina kuma godiya ga ’yan uwana ’yan fim bisa taimaka mini da suke yi wajen duk wani taimakonsu da na bukata. Kun taimaka mini har na kai matsayin da na kai.”
A karshe ya bukaci ’yan fim su hada kai don ganin masana’antar fina-finan Hausa ta kai tudun tsira.
“Ina kira ga ’yan uwana ’yan fim da mu hada kai, mu kuma jajirce don ganin mun kai masana’antar fina-finan Hausa tudun tsira. Mu sani wannan masana’anta tamu ce, ba mu da abin da ya fita, don haka ya zama dole mu tashi tsaye don ganin mun bi hanyoyin da za su kai ta tudun tsira.” Inji shi.
Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyana jarumin a matsayin mai hazaka da kuma  haba-haba da abokan sana’arsa.
Ta ce: “Kowa nasa ne, ba ya raina na kasa da shi, sannan yana girmama na sama da shi, ban taba jin wanda ya yi kuka da shi ba, shi ya sa ka ga daruruwan ’yan fim sun bar abin da suke yi suka halarci wannan bikin. Ka duba wannan mutanen da suka halarci filin wasa da kuma wannan dakin taron, ba sai an fada maka ba ka san na jama’a ne.”
Jaruma Jamila Nagudu ta bayyana jarumin a matsayin mutumin da baya nuna bambanci tsakanin ’yan fim.
“Ba ya nuna bambanci tsakanin ’yan fim, kowa nasa ne, yana da sakin fuska, yana da kyauta, yana kuma damuwa da damuwar duk wani na kusa da shi. Kowa ka tambaya zai ba ka kyakkyawar shaida a kansa. Don haka muka halarci wannan biki don nuna farin cikinmu.” Inji ta.
An fara taron da misalin karfe 8:00 na dare aka tashi 2:00 na dare.
’Yan fim din da suka halarci bikin sun hada da Darakta Ali Gumzak da Al’Amin Buhari da Nafisa Abdullahi da Isah Bado da Bello Muhammad Bello da sauransu.