Mu ’yan Darul Islam ne ba ’yan Boko Haram ba – Iyalan wadanda aka kama a Zariya
Bayan da ’yan sanda suka bayyana kama mutum 10 bisa zarginsu da kasancewa ’ya’yan kungiyar Boko Haram a kauyen Dogarawa da ke karamar Hukumar Sabon Garin Zariya a Jihar Kaduna, iyalan wadanda aka Kaman sun ce sub a ’yan Boko Haram ba ne, ’yan Darul Islam ne da aka wargaza a Jihar Neja. A farkon […]

Bayan da ’yan sanda suka bayyana kama mutum 10 bisa zarginsu da kasancewa ’ya’yan kungiyar Boko Haram a kauyen Dogarawa da ke karamar Hukumar Sabon Garin Zariya a Jihar Kaduna, iyalan wadanda aka Kaman sun ce sub a ’yan Boko Haram ba ne, ’yan Darul Islam ne da aka wargaza a Jihar Neja.
A farkon wannan mako ne Rundunar ’Yan sanda ta Shiyyar Zariya ta kama wadanda ake zargin inda ta ce sun yiwo gudun hijira ne daga dajin Sambisa dake Jihar Borno.
’Yan sandan sun ce kama mutanen ya biyo bayan bayanan sirri ne da suka samu kan yadda mutanen suke gudanar da harkokinsu tun lokacin da suka shigo unguwar, inda nan da nan sai aka hada ’yan sandan kwantar da tarzoma suka kama su.
Dukan mutanen goma da ake zargi suna hannun ’yan sanda na ci gaba da bincikensu kamar yadda Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda mai kula da Shiyya ta daya A.C Muhammad D. Shehu ya tabbatar wa Aminiya, inda ya ce binciken farko ya nuna wadanda ake zargi sun fara zama ne a Darul Islam a Jihar Neja daga nan suka koma dajin Sambisa da ke Jihar Borno domin haduwa da ’yan kungiyar Boko Haram, ya ce farmakin da mayakan Najeriya ke kaiwa a dajin Sambisa ba kakkautawa a kan ’yan Boko Haram da ya tilasta su tarwatsewa ya sa wadannsu suka nufo Zariya.
Sai dai da Aminiya ta ziyarci gidan da aka maka wadanda ake zargi a Unguwar Dogarawa, iyalansu sun musanta zargin na ’yan sanda. Wani matashi mai suna Malik bin Muhammad bin Adam mai kimanin shekara 22, ya bayyana wa Aminiya cewa: “A gaskiya mu ba ’yan Boko Haram ba ne mu ’yan Darul Islam ne, kuma a ranar Laraba 22 ga Yuni da misalin karfe 8:30 na dare mu idar da Sallar Isha’i muna tasbihi za mu fara Sallar Tarawihi sai jami’an tsaro suka zo suka zagaye gidan suka tattara iyayenmu da yayyena su takwas suka tafi da su hedikwatar ’yan sanda da ke Zariya. Da gari ya waye sai muka tura mutum biyu domin su je su ji dalilin kama danginmu da aka yi, su ma sai aka hada da su aka ce wai mu ’yan Boko Haram ne, a karshe an shaida mana cewa an wuce da su Kaduna,” inji matashin.
Ya kara da cewa, “A ranar Talata 28 ga Yuni, sai aka zo da biyu daga cikin mutanenmu domin bincike, to bayan sun kammala bincike sai aka koma da su Kaduna.
Malik Ibn Muhammad ya ce asali suna zaune ne a dajin Darul Islam da ke Jihar Neja inda suka kebe kawunansu suka yi wa garin suna Darul Islam. Amma shekara bakwai da suka wuce sai tsohon Shugaban kasa Umaru Musa da Gwamnan Jihar Neja suka rusa garin suka kwashe su kaf suka mai da su garuruwansu na asali. “Bayan mu kwashe tsawon akalla shekara 17 muna gudanar da rayuwarmu a daularmu muna yin sana’o’inmu tare da gudanar da duk al’amuranmu wadanda suka dace da shari’ar Musulunci bisa karantarwar Alkur’ani da Hadisan Manzon Allah kuma har karatun boko muna yi saboda mu mun yarda da ilimi kowane iri ne don haka ba ma kyamar karatun boko,” inji shi.
Malik ya kara da cewa bayan da aka mai da su garuruwansu na asali, to su mutanen Zariya ne don haka suka zabi zama a wannan unguwar kuma yau shekarunsu bakwai a unguwar suna gudanar da al’amuransu kamar yadda shari’a ta tanada, kuma ba su shiga huldar kowa. Ya ce “A nan inda ka same mu din nan a nan muke karatunmu kuma cikin karatunmu har da koyar da ilimin boko kuma ka ga litattafan boko a gabana, muna karatun Alkur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) da sauran littattafan Musulunci da suka dace da karantarwar Manzo. Mu dai ka gan mu nan abin da ya sa haka ya faru da mu ba ma shiga lamuran kowa, ba ma zuwa masallacin kowa kuma duk abin da ya faru da makwabta idan na farin ciki ne mukan ziyarce su mu taya su murna, idan kuma akasi ne misali kamar rasuwa to bama zuwa jana’izarsu, sai dai mu je mu yi musu ta’aziyya, haka mu ma a bangarenmu idan wani abu ya faru da mu ba ma gayyatar kowa mu muke abinmu da kanmu, sai dai inda suke rufe mutanensu idan an mutu mu ma can muke kai namu kuma haka azumin nan da aka fara mutanen gari sun riga mu da kwana daya domin mu sai mun ga wata da idanunmu, don haka idan mutum daya ya ga wata daga cikinmu, to, dukkanmu za mu yi azumi. To ganin irin wadannan abubuwa ne dalilin da wadansu makwabta suka yi ta kai rahoto a kanmu, kuma an sha turo jami’an tsaro na sirri suna zuwa suna ganin yadda muke gudanar da lamarin addininmu, wadansu daga cikinsu ma har Sallah muna yi tare da su. Don haka mu mun yarda da karatun boko.”
Wadansu daga cikin matan da aka kama mazansu Sadiya bintu Alhadar da Bara’atu bintu Yahaya da Maryam bin Yunus sun tabbatar da cewa su ba ’yan Boko Haram ba ne, domin suna karatun boko kuma suna zuwa asibitin gwamnati domin ko kwanan nan Sadiya ta kwanta a asibitin gwamnati to da ba mu yarda da boko ba ai da ba za mu je inda suke ba. Sun ce abin da ba su amince da shi ba irin wadannan darikokin da ake yin su wadanda suka saba wa karantarwar Manzon Allah (SAW) su ne suke inkari don haka suka ware kansu suke gudanar da addininsu yadda suka fahimta.
Sun ce ’ya’yansu suna karatun boko amma ba don su yi aikin gwamnati ba, sai domin su samu ilimi daidai da zamani don haka sun bukaci a sako musu mazansu.
Sun ce tun lokacin da aka raba su da matsugunninsu aka dawo da su garuruwansu na asali yau shekararsu bakwai ke nan a Zariya ba wai yakin da ake yi da Boko Haram ne ya sa suka dawo nan ba.