Mu yi hakuri da juna

Ko shakka babu, zaman yau da gobe sai Allah, ‘zo mu zauna, zo mu saba.’ Wata rana sai labari. Har kullum yana da kyau mu zama masu yawan hakuri da juna gun zamantakewar mu ta yau da kullum, duk yadda ka kai da hakuri, da zaman lafiya da abokan zaman ka, wata rana sai an […]

Mu yi hakuri da juna
Mu yi hakuri da juna

Ko shakka babu, zaman yau da gobe sai Allah, ‘zo mu zauna, zo mu saba.’ Wata rana sai labari. Har kullum yana da kyau mu zama masu yawan hakuri da juna gun zamantakewar mu ta yau da kullum, duk yadda ka kai da hakuri, da zaman lafiya da abokan zaman ka, wata rana sai an ji tsakanin ku (Sai kun bata da juna). Saboda wannan ita ce cikkkiyar dabi’a ta rayuwar kowane dan Adam.
Babban abin da zai kawo mana mafita, shi ne, kowa ya kudurce a zuciyar sa, kan cewa idan wani ya faranta maka, to  lallai dole wani sai ya bakanta maka. Saboda haka, abin da ya fi dacewa ga kowannen mu shi ne, mu yi kokari mu sanya hakuri cikin zukatan mu, mu zama masu yafiya da rangwame, tare  da yi wa juna uzuri. Shi mutum tara yake bai cika goma ba.
Da yardar Allah komai zai wuce, kuma da sannu za mu ci ribar rayuwar mu da kuma zamantakewar mu. Komai yana da iyaka, idan wata rana kaine, to, lallai wata rana ba kai ba ne. Duniyar nawa take? Komai ya yi zafi maganin sa Allah.
Wata rana da ni, da kai, da su, dukkan mu za mu gushe, mu koma zuwa ga Allah Mahaliccin kowa da komai (Allah). Babu abin da zai tseratar da mu sai kyawawan ayyukan mu da muka aikata. Saboda haka, mu yi kokari mu cire hassada da kyashi da kiyayya daga zukanta mu. Sannan mu yi kokari mu sanya soyayyar juna cikin zukatan mu, da kokarin kyautata zato ga ’yan uwan mu. Idan har mun yi haka, da sannu za mu samu cin nasara mai girma a duniya da lahira.
Allah ka kara mana son juna da kuma kaunar juna.

Muhammad Kabir Salisu ya rubutpo makalarsa daga  Gazarawa Communication Center Katsina 08034200141.