Mu yi taka-tsantsan kan salon da rikicin Fulani makiyaya da manoma ya dauka – Shagaya

Ana fama da matsalolin tsaro, musamman rikicin makiyaya da manoma. Wace shawara za ka ba gwamnati don magance matsalar? Wajibi ne mu fahimci salon wannan rikici da muke fuskanta saboda kai-kawon Fulani makiyaya ko kaurarsu, in za mu kira shi da haka. Saboda duk wanda ya kai shekaruna ya san a wannan bangare na Arewacin […]

Mu yi taka-tsantsan kan salon da rikicin Fulani makiyaya da manoma ya dauka – Shagaya

Ana fama da matsalolin tsaro, musamman rikicin makiyaya da manoma. Wace shawara za ka ba gwamnati don magance matsalar?

Wajibi ne mu fahimci salon wannan rikici da muke fuskanta saboda kai-kawon Fulani makiyaya ko kaurarsu, in za mu kira shi da haka. Saboda duk wanda ya kai shekaruna ya san a wannan bangare na Arewacin Najeriya inda muka fito, duk shekara ana samun kaurar Fulani da mutanen Ghana daga baya suka kira da ayarin Fulani masu kaura. Misali a Langtang, ka san labin da aka kebe don wannan kaura duk shekara daga Wase zuwa Garkawa zuwa Yelwa zuwa Shendam zuwa Kudu. Mun san lokacin da suke zuwa Kudu ko su dawo Arewa. Kuma Fulanin da suke wucew a kowane wuri da za su kai mako ko fiye sukan aiko da wakilansu, saboda suna da masu rauni a cikinsu ko matan da za su haihu. Kuma ba a samun takaddama. Don haka mun taso da wannan fahimta. A shekarun 1950, lokacin da muke makarantar firamare akwai wani babban rediyo da muke dauka idan iyayenmu sun fita. Sai mu je labin Fulanin mu zauna a gindin itatuwa, idan matan Fulanin suna wucewa da nono sai mu ce, ‘Kun ga wadannan mutane’ suna jin yunwa ko kishi, sai mu kashe rediyon mu ce mutanen da suke cikin rediyon suna jin yunwa ko kishi, sai matan Fulanin su yi murna su ba mu madara domin mutanen su ci gaba da magana. Wannan shi ne irin zaman lafiyar da muka sani muna yi, shi ya sa nake bayar da shawarar cewa tilas ne mu yi taka-tsantsan. 

A wannan yawon kiwo akwai abubuwa uku da suke faruwa. Na farko akwai kwararowar hamada. Wannan tare da kafewar Tafkin Chadi wanda ke daukar dimbin Fulani makiyaya, mahukuntan Kamaru sun datse ruwansa. Don haka ya zama wajibi da damansu su rika zarya a kokarinsu na neman abin da dabbobinsu za su ci su sha a yankin kogunan Benuwai da Kwara. Hakan na bukatar cikakken tsari. Kuma bisa lura da yadda al’amura suke canjawa ne Misis Mary Lar da Farfesa Jibril Aminu suka bullo da Shirin Ilimin ’Ya’yan Makiyaya, kuma Misis Mary ta yi digirinta na uku ne a kan haka. A cikin nazarin da ta yi, idan muka fahimce shi, za mu samar da wani yanayi na dakatar da Fulanin daga yawon kiwo ta bin labibbukansu. A yau abu ne mai dadi da wani ya kira shi da Gandun Kiwo. Dama akwai wuraren tsayuwarsu idan suna wucewa, amma ba a ba su babban suna da Ingilshi ba, amma yanzu kana samar da babban suna, kuma kana samar da babbara matsala.

Salo na biyu, shi ne wanda ya faru a 1984 bayan an kori ’yan Ghana daga Najeriya. Daga 1984/1985, abin da muke gani a yau ya faru a Saliyo da Ghana da Jamhuriyyar Benin da kuma Togo. Sun ce duk Fulanin da suka yi kaura can su bar musu kasa, daga nan ne aka samo sunan da na ambata a baya. Sun bayar da umarni ga dukan Fulani su bar kasashensu tare da shanunsu, suna cewa Fulanin Najeriya ne. Sai ya zamo yau a Ghana sai dai ka ga gonar kiwo kawai babu Fulani maso yawo da shanu. Sun dawo Najeriya lokacin na bar ofishin Sakataren Soji na karbi shugabancin Birged ta 9. An tura ni in kakkafa tanti-tanti in karbe su, na tattara sunayensu da bayanansu na san inda za su je, ko da gaske za su zauna a Najeriya ko za su tafi Mali ko duk inda suka fito. Gwamnatin wancan lokaci ta kula da su cikin karramawa. To akwai wani daji da ya hada Najeriya da Togo da Jamhuriyyar Benin a kusa da Kamba. Wannan daji na Kamba ya gangara har zuwa Kainji zuwa Babana zuwa Kayama, dajin Digidiru mai kyau cike yake da dausayi da kyau a gefen Kogin Kwara. Sai muka karbe su suka warwatsu suka zauna na watanni. Kuma a lokacin da gwamnati take tunanin abin yi, sai suka bar daji kungiya-kungiya. Wadansu suka koma hanyarsu da suka saba ta yawo da dabbobinsu. Abu na gaba da gwamnati ta ce, shi ne ya kamata a samu shugabancin a tsakanin Fulani, wannan ne ya karfafa yi wa kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyeeti Allah (MACBAN) rajista. Ni na sanya hannu a satifiket din rajistarta.

Niyyar gwamnati a lokacin ita ce; idan muka fuskanci wata karamar matsala, akwai shugabannin da gwamnati za ta dora wa laifi. To amma a yau su kansu makiyayan sun rarrabu zuwa kungiyoyi, kuma Fulani masu yawon kiwo sun ki yin komai da Fulani mazauna, wannan wani bangare na matsalar.

 Akwai bukatar mu nazarci wadannan abubuwa sosai kafin mu fara zargin junanmu, suna bukatar a ba su tabbaci a lokacin tattaunawa, kuma wannan ne maganar da na fada wa Gwamnan Jihar Benuwai cewa wajibi ne a tsoma dukan masu ruwa-da-tsaki a yayin tattaunawar, kowa ya ga dalilin haka. 

Na uku, masu dauke da makamai da ’yan fashi da abin da kuke da shi. Faduwar Mu’ammar Gaddafi a Libya, akwai bukatar mu tuna akwai sojojin sa-kai da dama da suka fito daga Chad da Nijar da Najeriya wadanda suka samu kansu suna samun kudi mai yawa a Libya. Wadansu daga cikinsu har yanzu ana koro su. Wadansu sun je ne a matsayin sojojin sa-kai da za su yi aiki su kare Libya, lokacin da aka rusa gwamnatin, wasu miyagun makamai sun fada hannun wadansu da suka gudo Nijar da Chadi suka hade da ’yan ta’adda. Za ka iske akwai wadanda suka riga suka samu horon soja, suna da wadannan makamai, ina da tabbacin wannan yana daga cikin bangaren abin da ya haifar da matsalar da muke fuskanta a Arewa maso Gabas. Za ka ga a cikin ’yan watanni kadan na wannan gwamnati, Shugaban kasa ya kai ziyarce-ziyarcen karfafa abota ga kasashen makwabta domin ya san inda matsalar take fitowa da kuma kawar da dabi’ar nan ta nuna cewa a Najeriya kawai matsalar take. Wannan ne ya taimaka mana amma mutane da dama ba su fahimci haka ba .

Wata matsalar kuma tana iya kasancewa an sanya siyasa a cikin lamarin a tsakanin dukan kabilun, kuma ina jin akwai bukatar gwamnati ta tashi haikan wajen fadakar da jama’a. Akwai bukatar ’yan Najeriya su rika kallon wasu matsaloli a matsayin na kasa ba na wani addini ko kabila ko a’a wata matsala ta Buhari ba, saboda shi Bafulatani ne idan wani Bafulatani ya shiga wata gona.

Wajibi ne mu watsi da wannan, kuma mu duba a can Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu inda sata da garkuwa da mutane suka zama sana’a, me ya sa ba a jingina su da addini, kuma suna da gwamnoni a can wadanda suka fito daga wadancan kabilu. Me ya sa ba mu zuwa can muna cewa wannan kabila ce  take aikata wannan saboda sun fito daga wancan gwamna ko gwamnan yankin ne yake ba su kariya. Ba matsala ba ce, amma in haka ya faru a Arewa sai a ce batun ne na Bahaushe Musulmi ko Kirista. Ina ganin wadannan abubuwa ne da suka wajaba mu kawar da su.