Mu yi watsi da son rai don hadin kan Musulmi – Assheikh Labbo
Assheik Murtala Labbo Gusau Shugaban kungiyar matasan kungiyar Izalatul Bidi,a wa Ikamatus Sunnah da ke kalaba jihar kuros riba, ya bayyana cewa sai fa Musulmin kasar nan sun watsar da son zuciya da ra’ayi akan abin da duk ya saba wa shari’a, an hada kai a kan gaskiya da rikon amana ce mafita,musamman halin da […]
Assheik Murtala Labbo Gusau Shugaban kungiyar matasan kungiyar Izalatul Bidi,a wa Ikamatus Sunnah da ke kalaba jihar kuros riba, ya bayyana cewa sai fa Musulmin kasar nan sun watsar da son zuciya da ra’ayi akan abin da duk ya saba wa shari’a, an hada kai a kan gaskiya da rikon amana ce mafita,musamman halin da Musulmi suka tsinci kan su a sassa daban-daban na duniya, idan aka lura da irin yadda aka sanyawa musulmi ido a Najeriya.
Malamin ya bayyana wa Aminiya, haka a Kalaba jim kadan da kammala wata lacca mai take ‘Gaskiy da rikon amana ita ke tabbatar da jagoranci ga al’umma tagari’ da kungiyarsa ta shirya a Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba, inda ya ce “wajibi ne ga kowane musulmi a kasar nan ya ajiye duk wani ra’ayinsa da son zuciya ya zo a hada kai a watsar da duk abinda ya sadawa sharia a hadu a kan gaskiya da rukon amana lura da yadda karancin hakan ya haifarwa kasar nan tabarbarewar shugabanci da kuma wadanda ake shugabanta .
Wata matasala da shugaban kungiyar ya ce ya gano ita ce “yau idan da akwai gaskiya da rikon amana tsakanin mu duk matsalolin nan da muke fuskanta ba za su faru ba, lura da yadda Allah ya ba mu shugabanni da ba su da amana haka muma mabiyan wasu ba su da gaskiya, da amana .”inji shi
“Matukar kowa na da wani ra’ayi na kashin kansa, to da wuya hadin kai ya iya yiwuwa har ma a hadu a taimaka wa addini” a cewarsa, inda ya ce, matukar aka samu rabuwar kai hakan babu abin da zai haifar face da mara Ido.
Haka nan kuma shugaban kungiyar matasan Izala kalaba, ya kara da cewa kungiyar su tana tallafa wa wasu bayin Allah,‘yan asalin Kuros Riba da suka musulunta, iyayen su da dangin su suka kisu “har ma mun jawo su a jiki mun dauki malamai da suke karantar da su ilmin addinin Musulunci da na zamani a wata makaranta da ke Nasarawa, muna biyan su albashi, don burin mu nan gaba mu ga mun tura su Arewa su samu ilmi mai zurfi na larabci da addini”.
Da ya juya kan daukacin Musulmin duniya da na Najeriya, Assheik Murtala Gusau ya yi hannunka mai sanda ga Musulmin kasar nan da su mike tsaye wajen hada kan su, tunda babu wani wanda ake kyara ko aka sanya wa Ido ko nema da fitina kamar musulmi.