Mu zabi gwamnoninmu
Don Allah edita a bani dama in ja hankalin jama’ar jamiyyar adawa ta APC.ni mutumin Kwankwasiyya ne, amma tun da na ji cewa mai girma tsohon shugaban kasa, wato general Janar Muhammadu Buhari ya lashe zaben fitar da gwani na jamiyyar AP,C sai na ji a raina shi ne mafi alkhairi. Saboda a kodayaushe wannan […]
Don Allah edita a bani dama in ja hankalin jama’ar jamiyyar adawa ta APC.ni mutumin Kwankwasiyya ne, amma tun da na ji cewa mai girma tsohon shugaban kasa, wato general Janar Muhammadu Buhari ya lashe zaben fitar da gwani na jamiyyar AP,C sai na ji a raina shi ne mafi alkhairi. Saboda a kodayaushe wannan ita ce addu’armu Allah ya zaba mana mafi alkhairi. Ka da saboda kai kana son a tsayar da Atiku ko Kwankwaso ka ce tun da ba naka aka tsayar ba, shi ke nan ka fasa yin zabe; ko kuma wasu maganganu makamantan haka. Mu dage mu zabi gwaninmu a zaben 2015. Wassalam. Daga Isma’il Lawal Gambo 08032619334
Ga ’yan Najeriya
Gaisuwa da fatan alheri ga Mai Girma Janar Muhammadu Buhari : Fata nagari Lamiri ina ‘jan hankalin al’ummar Najeriya fadin cewa Janar in ya tsaya takara ba zai ci ba zabe ba. Idan ba ku manta ba, Alhassan Watara shugaban kasar Cote’Dboire na yanzu shekara nawa ya yi yana gwaggwarmayar Siyasa ? Har ka ji wadansu na’ cewa Janar Muhammadu Buhari wai Yayi tsufa ‘Yan iya magan nacewa abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai hango shi ba. Ya kamata mu rika yi wa kawunanmu adalci, Mulki na Allah , Shi ke bayar da shi ga wanda ya so, fadi alkhairi ko ka yi shiru. Daga Alhaji Umar Foreber, Gashua 08108003333.
Ga Gwamna Kwankwaso
Salam Editan Aminiya, Allah ya kara muku basira. Ina kira ga kwamnan kano ya jira lokacinsa yana nan tafe ya maida komai yana da lokaci; ya ware kamar yadda Atiku Turakin Adamawa ya nuna wa Baba uban Najeriya, cikin yardar Allah kaunata musamman. Daga lnusa Suya Spot, Ketu a Jihar Legas.
kuri’ar mu ‘yancin mu
To ‘yan Najeriya an ce”duk girman gona tana da kunyar karshe” Allah ya kawo karshen mulkin wannan gwamnati ta PDP, sai mu jajirce a zabe mai zuwa, mu dage mu canza gwamnati, don samun kwanciyar hankali da kykkyawan tsaro, kawo karshen cin hanci da rashawa, almundahana da sama da fadi. “kuri’ar mu ‘yancin mu.”
Daga Ibrahim AB. Balarabe, Birnin Zaria, 08023442901.
Ga ’yan kasa
Salam. Don Aminiya ku isar min da sako na ‘yan kasa, da mu tashi tsaye mu mara wa dan uwammu mai kishin Niajeriya gaba daya, Janar Muhammadu Buhari baya, a zabe mai zuwa, 2015 idan Allah ya kai mu. Allah ba mu lafiya da tsawon rai. Amin. Daga Ahiijo Tiddo, Gombe.
Ga Gwamnan Jigawa
Salam Edita Kabani Dama In Sanar Da Sako Zuwa ga Gwamnarn Jihar Jigawa, Sule Lamido Dan Allah ya taimaka ya bai wa wadanda suka gama r Koyon Sana’a kayan aiki. Sun hada kusan makonni shidda Daga Dan Birniwa .
Ga Gwmanan Barno
Editan Aminiya ka sanar da Gwamna Kashim Shettima na Jihar Barno, mu mabiyan Injiniya Ibrahim Ali a tsohuwar tafiyar ACN, ba mu ji dadin gamayyar jam’iyyu a Yobe ba, domin ba mu samu komai a jerin kwamishinoni ba. Gwamna ya saba wa yarjejeniyar hadewar mu, wadda ya daukar mana alkawari a shekarar 2011. ’yan CPC an ba su uku, mu kuwa ‘mun ta shi a tutar babu. Allah Ya sa gwamnan mu ya gyara kurensa. Idan kuwa bai yi ba, duk matakin da muka ga ya dace za mu dauka. Daga Tahir Mohammed, tsohon sakataren ACN.
Addu’a ga Najeriya
Slm Babban Edita da fatan kana lafiya, amin. Ina son ka ba ni dama in mika sakon gaisuwa ga daukacin ma’aikatan wannan jarida mai farin jini, watau Aminiya. Kuma don Allah ‘yan uwana ‘yan Najeriya, musanman ‘yan Arewa mu dage da rokon Allah da ya yi mana zabi mafi alheri a kan gwamnatin PDP. Amin. Daga Mannir M Yabo sokoto. 08034457387.
Martani ga Dokta Agabi
Mummunan neman shugabanci. Na karanta hira da aka yi da Dokta Yusuf Agabi, dan takarar neman kujerar gwamnan Jihar Nasarawa, a karkashin jam’iyar PDP. A gaskiyar kishiyar maganar sa ce ke haifar da rikici a jihar ta Nasarawa, domin kuwa gwamna mai ci yanzu mutum ne mai kokarin kawo ci gaba da kuma walwala ga jama’a, ga shi don mazaunin Mararaba tsawon lokacin mulkin PDP nake Mararaba, ba mu da wuta sai da Almakura ya hau mulki muke samun wutar lantarki. Don haka maganar Dokta Yusuf Agabi ba gaskya ba ce. Daga Garba Ya’u Majiya, 08067742692.
Haba Shugaba Jonathan
Edita bai kamata a ce a matsayin shugaban kasa yana yawo yana bude filayen jirgin sama a jihohin Jigawa da Kebbi, amma ga shi an salwanta da rayukan bayin Allah a jihar Borno da Kano da Yobe, da Adamawa ka kasa kai ta’aziya Allah ka yi mana canji a 2015. Daga Abdullahi Babangida Yar Akwa Kano.
Ga sarakunan Arewa
Kira ga sarakunan Arewa, kamar yadda mai girma sSarkin Kano Sunusi ya yi kira ga mutane, mu tashi mu kare kanmu. Ya kamata sauran sarakunan ma su bi sahunsa matukar ba ’yan amshin Jonathan ba ne, don abubuwan da ake yi a Arewa abin ya yi yawa, Mu tashi mu kare kanmu, kuma mu ci gaba da addu’a. Daga Aliyu Ibrahim Babanyara Shagamu. 07068867232.
Ga’yan jam’iyyar APC
Ina mika sakon godiya ga ban-gajiya ga dukkan wakilan zaben cikin gida (delegates) na jamiyyar APC wadanda suka zabo mana Baba Buhari, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben shekarar 2015. Da fatan Allah ya nuna mana ranar zabe, a lokacin da mu al’ummar Najeriya za mu fito mu kori mulkin kama-karya na jamiyyar PDP, tun daga
matakin karamar hukuma, har zuwa kasa. Ya Allah muna rokonKa, ka tabbatar mana da Baba Buhari, a matsayin sabon shugaban Najeriya. Daga Isah Ramin Hudu, Hadejia. 08060353382
Aminiya sau 2 a mako
Jaridar Aminiya zakarar gwajin dafi a cikin Jaridu. Edita don Allah ka ba ni dama in yi tsokaci, tare da yaba wa irin namijin kokarin da Jaridar Aminiya ke yi, musamman wajen kawo mana labarai masu inganci, Hakika ina alfahari da wannan jaridar ta zama aminiyata a duk lokacin da nike cikin nishaddi, tabbas tana gamsar da ni da labarai masu muhimmanci. Muna fata za ta koma fitowa sau biyu a sati Allah ya daukaka Ku Daga Aisha Kyauta Kano 07055903345
Guguwar zabe na kadawa
Salam don Allah Edita ka ba ni dama in yi tsokaci dangane da yadda zabe ke kara kusantowa, Hakika masu iya magana na cewa idan aski yazo gaban goshi ya fi zafi, ganin yadda kowace jam’iyya ke kara fito da wadanda za su rike mata tuta. To , amma wani abin takaici shi ne yadda aka dinga gudanar da zaben ya nuna a bayyane an yi amfani da kudi wajen sayan wakilan zabe, su kuma da dama sunyi amfani da hakan wajen zabar wadanda ba su cancanta ba; kuma hakan ba zai haifar wa tsarin dimokuradiyya da mai ido ba. Ya kamata dai a dinga sara ana duban bakin gatari. Daga Aminu Abdu Baka noma Sani mainagge Kano 08099479880.
Godiya ga Gwmana Lamido
Assalamu alaikum, Aminiya jarida mai farin jini, abar alfaharin mu. Don Allah ki mika min sakon godiya ga Gwmana Lamido saboda gudunmuwa da ya bai wa kurame, don yin taron wa’azi da za a yi nan da mako guda. A garin Hadeja. Nagode. Daga Mujahid Adam Hadeja. 081055