Mu’amala Tsakanin bangaren Zartarwa Da Majalisa: kalubalen Dimokuradiyya Da Ci Gaba A Jihar Katsina (1)
A ranar Alhamis 24 ga Agusta, 2017, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya gabatar da takarda mai take na sama, a Kwalejin Nazarin Al’amuran Tsaro da ke Bwari-Abuja. Saboda muhimman darussan da ke kunshe cikin takardar nan, shi ya san Gizago ya kawo ta nan, domin a amfana: Gabatarwa: Dimokuradiyya da samun […]
A ranar Alhamis 24 ga Agusta, 2017, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya gabatar da takarda mai take na sama, a Kwalejin Nazarin Al’amuran Tsaro da ke Bwari-Abuja. Saboda muhimman darussan da ke kunshe cikin takardar nan, shi ya san Gizago ya kawo ta nan, domin a amfana:
Gabatarwa:
Dimokuradiyya da samun nasarar dabbaka ta a kasashen Afrika ya dogara ne ga wasu ginshikai da dama. daya daga cikin wadannan ginshikan shi ne yanayi da turakun siyasa da ke akwai a kasa. Haka kuma ya dogara da ayyuka da karfin wadannan turaku da kuma dangantakar gudanarwa da ke tsakaninsu. Biyu daga cikin wadannan turaku mafiya muhimmanci, wadanda ayyukansu da musharakarsu ke shafar nasara ko akasinta ga dimokuradiyya su ne bangaren Zartarwa da kuma bangaren Majalisa. Masana harkar dimokuradiyya sun tafi da cewa irin mu’amalar da aka samu tsakanin wadannan muhimman turakun dimokuradiyya biyu, ita ke bayyana salon gwamnati da ci gaban da ake samu a karkashin mulkin dimokuradiyya. Shi ne kuma ke haifar da dorewar salon mulkin dimokuradiyya a matsayinsa na tsarin siyasa. Idan muka yi la’akari da wannan bayani a matsayin jigon wannan takarda, haka kuma za mu kara da cewa, gamsuwa da biyan bukatar da mafi yawan al’umma za su samu daga gwamnatin dimokuradiyya, sun dogara ne kacokan ga sakamakon wannan mu’amala tsakanin wadannan turaku guda biyu. Wato idan mu’amalar ta kasance bisa hadin kai da lumana tsakanin bangarorin biyu. A yayin da wannan mu’amala ta kasance cikin rashin fahimta da zargi da rashin mutunta juna da rashin hadin kai da kuma rikici tsakaninsu, gwamnati za ta zama sukurkuce yadda ba za ta amfanar da komai ga al’umma ba, na ribar dimokuradiyya. Dalilan da za su haifar da haka ga su nan karara, domin kuwa idan aka samu irin wannan yanayi, yana da wahala a samu jituwa tsakanin wadannan turaku biyu.
Al’amari bai zo da mamaki ba, yadda tun 1999, lokacin da dimokuradiyya ta dawo Najeriya, dangantaka tsakanin bangaren Zartarwa da bangaren Majalisa ta ci gaba da zama al’amari mafi muhimmanci da ake tattaunawa a kansa. Wannan abin dubawa ne mai matukar muhimmanci, musamman idan muka yi la’akari da muhimman abubuwa biyu da suka biyo bayan dawowar mulkin dimokutradiyya a 1999. Na farko dai, Najeriya ba ta dade da samun kanta daga takurar mulkin soja ba – mulkin da ke kassara sassan gwamnati ya raunana su. A nan, idan muka lura, an dunkule bangaren zartarwa da bangaren majalisa wuri guda, domin kuwa a karkashin mulkin soja, wadannan turaku biyu ana hade su ne zuwa gida guda, inda ake samun Shugaban kasa na soja a matsayin babban mai kafawa da kuma zartar da doka. A mafi yawan lokaci, shi kadai ke zama wuka da nama ko kuma ya tare da abokan aikinsa da suka kafa mulkin tare. A irin wannan tsari na mulkin soja, hukumomi da ma’aikatun gudanar da gwamnati ba su da wani ’yanci.
Na biyu, Najeriya ta zabi ta gudanar da Tsarin Shugaban kasa Mai Cikakken Iko, wanda ya kunshi rarraba iko da tafiyar da shi ga Turakun Gwamnati uku. Hanyar da wadannan turaku uku za su bi su samar da ’yanci da dogaro a tsakaninsu, al’amari ne babba da ke jan ra’ayin masana da ’yan siyasa da makamantansu. Wannan wani abin dubawa ne da zai iya kawo tasgaro ko ma ya ruguza dimokuradiyyarmu gaba daya, tun ma kafin ta girma.
Yanzu dai an kusa share shekara 20 ke nan da dawowar mulkin dimokuradiyya a Najeriya, inda aka sha gudanar da zabubbuka daban-daban a matakin jihohi da kasa baki daya. Abin da ya kamata mu tambaya shi ne, shin an samu abin da ake bukata daga dimokuradiyya ko kuwa an samu akasi a wannan Jamhuriya Ta Hudu? A kan wannan ne za mu tattauna irin dangantakar da ke wakana tsakanin bangaren Zartarwa da bangaren Majalisa a matakin jihohi a Najeriya, ta hanyar daukar misali da Jihar Katsina.
Na zabi in doka misali da Katsina ne a wannan takarda saboda dalilai na musamman. Jihar Katsina ta dade da kasancewa jiha mai mutunci, wacce ta sama wa kanta suna a matsayin wuri mai karimci da zaman lafiya. Mu’amala da dangantaka tsakanin bangaren Zartarwa da bangaren Majalisa tun daga 1999, dangantaka ce mai tsafta, ta lumana da hadin kai tsakanin juna. Haka kuma, sama da shekara biyu ke nan da jam’iyyarmu ta APC da mulkinta, a karkashin shirinta na Dawo Da Martabar Katsina ta samu nasarar daidaita mu’amala, ta hanyar rarraba hakki da ’yancin gudanarwa tsakanin wadannan muhimman turaku na dimokuradiyya biyu.
Domin a samu saukin fahimtar wannan takarda, mun rarraba ta zuwa sashi-sashi. Sashi na daya kamar yadda za mu gani, ya yi kokarin bijiro da muhimmancin wannan takarda. Sashi na biyu ya yi bayani ne tare da tantance muradun dimokuradiyya da suka shafi dangantaka tsakanin bangaren Zartarwa da na Majalisa. Wannan tsarin shi ne mafi dacewa, domin zai ba mu damar baje komai a faifai domin tankadewa da fitar da tsaba. Sashi na uku ya mayar da hankali ne wajen bin kadin tarihin dangantaka tsakanin bangarorin biyu a siyasance a Najeriya. A sashi na hudu, takardar ta tsunduma ne wajen bijiro da darussan da za a iya samu dangane da dangataka tsakanin bangaren zartarwa da majalisa a Jihar Katsina, domin bayyana muhimmancin aikin tare, hadin kai, zaman lumana tsakanin sassan biyu masu muhimmanci ta bangaren gudanar da mulki a Jamhuriya Ta Hudu a Najeriya. Sashi na biyar na takardar nan ya karkare ne da duba wasu muhimman al’amura tare da bayar da shawarwari, yadda za a kara karfafa mu’amala tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa, domin a samu wanzar da romon dimokuradiyya cikin nasara tare da tabbatar da dorewar tsarin dimokuradiyyarmu.
Dangantaka Tsakanin bangaren Zartarwa Da Na Majalisa: Tsokaci Da Zubi Da Tsari:
Littattafai daban-daban da suka yi bayani game da tsarin dimokuradiyya suna da yawa, duk da cewa sun bayar da mabambantan bayanai dangane da zubi da tsarin gudanuwarta. Masana sun yi rubuce-rubuce dangane da yadda dimokuradiyya ke gudana, musamman ma a kasashe masu tasowa na Afirka da Latin Amurka. Akwai dalilai da dama da suka sanya masana da masu bincike suka sanya ido wajen binciken al’amuran dimokuradiyya a wadannan al’ummomi. daya daga cikin wadannan bayanai sun danganci siyasa, tarihi, al’ada da ma yankin mafi yawan wadannan kasashe, shekara sama da arba’in da ta gabata. Kusan dukkan kasashen Afrika da Latin Amurka sun dandana matsalolin siyasa daban-daban, wadanda ko dai suka raunana mulkin dimokuradiya ko kuma suka kashe shi gaba daya. A Afrika kadai, idan ka debe tsirarun kasashen da ba su kai dozin daya ba, kusan dukkan sauran sun taba dandana mulkin soja a wasu mabambantan lokuta tun daga lokacin da suka samu mulkin kai. Sun gamu da juyin mulki daban-daban gami da wasu matsalolin siyasa da suka yi wa dimokuradiyya karan tsaye.
Za mu ci gaba