Mu’amala Tsakanin bangaren Zartarwa Da Majalisa: kalubalen Dimokuradiyya Da Ci Gaba A Jihar Katsina (2)
A ranar Alhamis 24 ga Agusta, 2017, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya gabatar da takarda mai take na sama, a Kwalejin Nazarin Al’amuran Tsaro da ke Bwari-Abuja. Saboda muhimman darussan da ke kunshe cikin takardar nan, shi ya sa Gizago ya kawo ta nan, domin a amfana kuma ga kashi na biyu: […]
A ranar Alhamis 24 ga Agusta, 2017, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya gabatar da takarda mai take na sama, a Kwalejin Nazarin Al’amuran Tsaro da ke Bwari-Abuja. Saboda muhimman darussan da ke kunshe cikin takardar nan, shi ya sa Gizago ya kawo ta nan, domin a amfana kuma ga kashi na biyu:
Al’amarin bai zo da mamaki ba, kasancewar mafi yawan littattafan da ake nazarta dangane da yadda ake tafiyar da dimokuradiyya a Afirka da sauran kasashe masu tasowa an tsara su ne bisa la’akari da yanayin bangarorin tafiyar da gwamnati a siyasance da aka tanadar da nufin tallafar dimokuradiyya. Haka ma, an samar da bayanai game da irin karfinsu da kuma yanayin yadda suka yi tarayya da juna. Wannan tsari ne da ya shafi dimokuradiyya da mulki kuma shi ne ginshiki abin dubawa da tattaunawa dangane da dangantaka tsakanin bangaren Zartarwa da Majalisa a kasashe masu tasowa. Wannan ke nuna mana dalilin da ya sa dangantaka tsakanin bangarorin nan biyu ta kasance wata babbar jigo ga manazarta al’amuran dimokuradiyya. Tarihi a manya da kananan kasashe ya nuna yadda rashin jituwa tsakanin bangaren Zartarwa da na Majalisa ke haifar da babbar baraka da tashin-tashina a siyasa da mulki. Hairani kan haddasu a siyasance, inda wasu lokutan ma yake kassara gwamnati gaba daya, wasu lokutan kuma a yi ta tsige-tsigen shugabanni ko kuma a kassara doka da oda, kamar kuma yadda ake wancakalar da tsarin mulkin dimokuradiyya. Misali, mu tuna abin da ya biyo bayan mulkin ’yan Nazi kafin bayyanar Yakin Duniya Na Biyu a Jamus, a karkashin ikon Adolf Hitler. A kasashen da ginshikan mulki ba su gama kafuwa ba kuma tsarin dimokuradiyya bai kai ga amsuwa ya zama gama-gari ba a matsayin “tsarin tafiayr da mulki tilo da aka amince da shi,” kamar yadda masani Guillermo O’Donnell ya bayyana, akan samu rashin jituwa da rashin mutunta juna a bangarorin nan biyu na gwamnati kuma hakan kan haifar da barazana ta kai tsaye ga kafuwa da dorewar dimokuradiyya da wanzuwar tafiyar da mulki.
Don haka, abu ne mai muhimmanci mu fahimci wadannan abubuwa da suka shafi dimokuradiyya, sannan mu fahimci ma’anar ita kanta dimokuradiyyar, wanda hakan zai ba mu damar fahimtar wannan nazari namu dangane da dangantaka tsakanin bangaren Zartarwa da babgaren Majalisa a Najeriya. Mu sani, wannan ce shawarar da masanin harkokin siyasa da mulki dan kasar Girka, Socrates ya bayyana. Ya ce: “Matakin farko a nazari, shi ne bayyana ma’anar al’amarin da za a tattauna a kansa.”
Ma’anar Kafuwar Dimokuradiyya A Zahiri Da Badini:
Kafuwar Dimokuradiyya, wata kinaya ce da masana kimiyyar siyasa ke auna yanayin dimokuradiyya a siyasar kasa. Tana la’akari da yanayi da amsuwa da dorewar dimokuradiyya ko akasin haka a tsarin siyasa. Tana kuma duba zurfin yadda tsarin ya kafu da hasashen yadda zai kasance a nan gaba. Haka kuma, akan lura da yanayin gudanarwarta, shin tana fuskantar barazana ko akasin haka? Idan dimokuradiyya ta bunkasa, ba ta fuskantar wata barazana, irin wannan tsarin ne ake kira da Dimokuradiyya Mai ’Yanci, shigen irin ta Yammacin Duniya.
daya daga cikin fitattun masana nazarin dimokuradiyya, Philippe Schmitter ya ce ma’anar Kafuwar Dimokuradiyya shi ne kaiwa makura mai zurfi na wanzuwar tsarin dimokuradiyya a kasa ayyananniya. Abin la’akari da irin wannan kasa ga fahimtar Schmitter, ita ce inda aka samu tabbatuwar kafuwar ginshikan bangarorin mulki ko turakun mulki a dimokuradiyyance, amma ba lallai sai ta tsarin siyasa ba. Za mu ga haka baro-baro a nan gaba, kamar yadda wani masani, O’Donnell ya bayyana. O’Donnell ya ce za a iya cewa dimokuradiyya ta kafu ne kawai idan ta zama ’yar gida kuma ta amsu ga masu ilimi a matsayin hanya daya kacal wajen ginawa da bunkasa gudanuwar mulki a kasa.
Kodayake kamar yadda na fada a baya, wannan ma’anar ta yi mana jagora ne kadan, domin kuwa ba ta bayyana mana karara yadda za mu auna mu gane cewa masu ilimi sun amshi dimokuradiyya ita kadai a matsayin tsarin gudanar da mulki ba, musamman ma a irin kasa irin tamu mai yawan al’umma mabambanta. Irin wannan bayani, kamata ya yi ya zama ya kawo ma’ana ta karara. Rashin samun haka ne ya sanya wasu masanan suka turza wajen sake fadada ma’anar Kafuwar Dimokuradiyya. Larry Diamond, wani fitaccen masani, wanda ya dade yana nazari da bincike a Najeriya, ya bijirar da hanyoyi daban-daban na fahimtar wannan al’amari.
Domin fahimtar batun Kafuwar Dimokuradiyya a kasa, a fahimtar Diamond, sai an yi la’akari da tsarin rayuwar al’umma da al’adunsu da kuma siyasarsu. A bangaren tsarin rayuwa da al’adun mutane, mutum zai yi la’akari ne da abin da yawan al’ummar kasar suka rike, suka yarda da shi. A kasar da siyasar dimokuradiyya take kafuwa, kula da halayya da al’amuran mutane, ba na shugabanni kadai ne ba, bangarorin gwamnati, kamar Majalisa ko bangaren Zartarwa, bangarori ne da za su kasance wajen hada kai ne, tuntubar al’umma don shawara da kuma tattaunawa kan al’amura domin zartarwa. Ba ma sai an kai ruwa rana ba, wadannan al’amura, su ne kashin bayan dimokuradiyya. A siyasance, masana da dama sun bayyana cewa bangarorin nan su ne ke rike da mabudan samuwar hadin kai da kafuwar dimokuradiyya da gudanuwarta da kuma dorewarta. An samu tabbacin cewa, bangarori masu karfi, su ne ruhin dorewar dimokuradiyya a ko’ina ne kuwa a fadin duniya.
Shin me ya sanya masana suka dauki bangarorin tafiyar da gwamnati a matsayin gishin tafiyar da dimokuradiyya? Na yi amanna da cewa amsar a bayyane take karara, kowa zai iya tsinkayar ma’anarta. bangarorin mulki su ne ke daidaita gudanuwar mulki da kafawa, saitawa da aiwatar da dokoki. Suna taimaka wa shugabanni domin su bi tsari, su kauce wa daukar matakai kara-zube, sannan kuma suna taimakawa wajen samar da kididdiga da bin kadin yadda aka tafiyar da al’amuran mulkin. Haka kuma, bangarorin gwamnati suna samar da yanayin yi wa al’umma aiki da samar da daidaito da adalci tsakanin al’umma, domin gaskiya ta tabbata, musamman wajen samar da karsashin tafiyar da harkokin gwamnati bisa doka da oda a kowane lokaci.
Wannan ke nuna cewa tsarin dimokuradiyya kambamau ne da ke kunshe da siyasa, al’umma da al’adu wajen gudanarwa. Ke nan, dimokuradiyya tsari ne da ke tafiya ta la’akari da dabi’u, halaye da al’adun al’umma, musamman wajen musharaka tsakanin masu ilimi da sauran mayawaitan al’umma. Idan aka samu kafuwar dimokuradiyya irin wannan, an kawar da batun tsoron juyin mulkin soja, wanda ke kassara tafiyar da gwamnatin farar hula.
Ba zan kammala wannan bayani na ma’anar Kafuwar Dimokuradiyya ba, sai na aro karin haske daga masani Samuel Huntington. Wannan masani ya ce babu wani abu da ke tabbatar da dorewa da kafuwar dimokuradiyya kamar a ce ana samun hawa da saukar mulki daga wannan gwamnati zuwa wata a matakin kasa baki daya, cikin kwanciyar hankali da lumana. Ya yi wa wannan tsari lakani da Nasara-Rubi-Biyu. Kamar yadda ya ce: “Za a iya cewa dimokuradiyya ta kafu idan aka samu jam’iyya ko kungiyar da take kan mulki, aka gudanar da zabe ta fadi, amma ta mika mulkin ga wata jam’iyyar ta daban da ta samu nasara. Haka kuma idan aka samu ita ma wannan jam’iyya ta mika wa wata jam’iyya ta bayanta da ta samu nasara a mulki, bayan zabe.”
Za mu ci gaba