Mu’amala Tsakanin Vangaren Zartarwa Da Majalisa: Qalubalen Dimokuraxiyya Da Ci Gaba A Jihar Katsina (3)

A ranar Alhamis 24 ga Agusta, 2017, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya gabatar da takarda mai take na sama, a Kwalejin Nazarin Al’amuran Tsaro da ke Bwari-Abuja. Saboda muhimman darussan da ke qunshe cikin takardar nan, shi ya sa Gizago ya kawo ta nan, domin a amfana kuma ga kashi na uku: […]

Mu’amala Tsakanin Vangaren Zartarwa Da Majalisa: Qalubalen Dimokuraxiyya Da Ci Gaba A Jihar Katsina (3)

A ranar Alhamis 24 ga Agusta, 2017, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya gabatar da takarda mai take na sama, a Kwalejin Nazarin Al’amuran Tsaro da ke Bwari-Abuja. Saboda muhimman darussan da ke qunshe cikin takardar nan, shi ya sa Gizago ya kawo ta nan, domin a amfana kuma ga kashi na uku:

Idan muka waiga baya daga watan Mayu na 1999, lokacin da dimokuraxiyya ta dawo Najeriya, sannan muka duba irin qalubalen da aka shiga, babu shakka za mu iya bugun gaba mu ce dimokuraxiyya ta samu gindin zama. Don haka an samu kawar da tsoron komawa mulkin kama-karya. Kodayake dimokuraxiyyarmu ba ta balaga, ta kafu irin ta Yammacin Turai ko Arewacin Amurka ko Latin Amurka ba. Muna da sauran jan aiki a gabanmu, musamman idan muka yi la’akari da dangantaka tsakanin Vangaren Zartarwa da na Majalisa, biyu daga cikin vangarorin gwamnati bisa tsarin dimokuraxiyyar Shugaban Qasa Mai Cikakken Iko.

Dangantaka Tsakanin Vangaren Zartarwa Da Majalisa A Tsarin Shugaba Mai Cikakken Iko A Dimokuraxiyyance:

Dangantaka tsakanin waxannan vangarori biyu, babban jigo ce a tsarin gudanuwar tsarin Shugaba Mai Cikakken Iko a dimokuraxiyyance. A wannan tsari, tafiyar da mulki abu ne mai sauqi, saurin gudanarwa, buxaxxe kuma wanda za a iya bin kadi, muddin dai sassan gwamnati uku na cin gashin kansu bisa doron tsarin mulki kuma suna aikinsu yadda ya dace. Waxannan ayyuka kuwa sun haxa da tsarawa da aiwatar da dokoki da kuma gudanarwa. Majalisa ke tsara dokoki domin kare qasa da bunqasa rayuwar al’umma, a yayin da Vangaren Zartarwa ke gudanar da waxannan dokoki da tabbatar da an bi su sau da qafa. Masana sun tafi cewa, dangantaka mai kyau tsakanin waxannan sassa biyu, su ke haifar da nasara a tafiyar mulki a dimokuraxiyyance. Kowane vangare dai yana da muhimmanci kuma yana da ayyukansa a tsare, don haka tuntuvar juna ba qarfa-qarfa ba, ita ce hanya mafi a’ala wajen samun nasara.

An samu bayanin cewa, dalilin da ya sanya aka amince da turaku uku ko vangarori uku a Kundin Tsarin Mulkin Amurka a Qarni Na 18, na tafiyar da tsari gwamnatin Shugaban Qasa Mai Cikakken Iko, shi ne domin a kare dimokuraxiyya daga faxawa komar mulkin gargajiyanci ko tsarin gurguzu da masu qarfa-qarfa. Mu duba yadda a lokacin nan Amurka ba ta daxe da fitowa daga yaqin qwatar kanta daga Daular Haxaxxiyar Turai ba. Dalilin da ya sanya Najeriya ta aro tsarin Shugaba Mai Cikakken Iko daga Amurka, saboda masana sun bayyana cewa tsarin yana ba shugaba qarfin ikon haxa kan al’ummu daban-daban da muke da su a qasa irin tamu, wanda haka zai kwantar da hankalin tsirarun qabilu, sannan ya xora wa shugaba haqqin tantancewa, yadda za a bi kadin yadda ya aiwatar da mulki dalla-dalla, idan ya kauce a dawo da shi hanya. Waxannan dalilai ne suka sanya masu tsara mulkin Najeriya suka zavi wannan tsari a 1979, maimakon salon mulkin Falamantare da aka yi amfani da shi a baya. Marigayi Janar Murtala Ramat, ya yi la’akari da cewa tsarin mulkin na Falamantare a Jamhuriyya ta Farko, shi ne ya ba da damar aka shiga yaqin basasa, inda aka rasa rayukan al’umma kusan miliyan biyu, don haka aka amince da wannan tsari na Shugaba Mai Cikakken Iko, inda masana 49 suka zauna, suka tattauna, sannan suka amince da wannan tsari.

Muhimman Sigogin Dangantaka Tsakanin Vangaren Zartarwa Da Majalisa A Najeriya (1999-2017):

Idan muka lura da musharaqar da ke tsakanin Vangaren Zartarwa da Majalisa a matakin Tarayya da Jihohi, akwai yiwuwar mu gano wasu abubuwa masu muhimmanci da ke tattare da wannan tsari a dimokuraxiyyance.

’Yanci, Haxin Kai, Dogaro Da Juna: Waxansu muhimman al’amura da za a iya tsinkaya a wannan tsari su ne, kowane vangare tsakanin Majalisa da Zartarwa yana da ’yancin cin gashin kansa, sannan akwai musharaqar tuntuvar juna, akwai haxin kai da mutunta juna. Jihohi daban-daban sun samu irin wannan fahimtar a tsakani, musamman ma har da Jihar Katsina. Tsarin ya haifar da fahimtar cewa gwamnati dai rayayyen tsari ne mai gudana yau da kullum, domin haka yana buqatar tuntuva, tattaunawa da baiwa kowa haqqinsa domin a samu biyan buqatar juna, don haka aka samu irin wannan zaman lafiya da fahimta a Majalisar Wakilai ta Tarayya a shekarun 2003 da 2007 tsakanin vangarorin Majalisa da na Zartarwa. Kowane vangare ya riqe ’yancinsa, an yi haxin kai da mutunta juna wajen tafiyar da aikin da ya wajaba kan kowane vangare. Wannan ya haifar da zaman lafiya da bunqasa qasa da qarfafa tafiyar tsarin dimokuraxiyya.

Dacewa, Saryarwa da Tabbatarwa: A wannan tsari, ana samun aiwatar da al’amuran mulki yadda suka dace da abin da ake buqata, ana samun wasu lokuta da dole sai wani vangare ya saryar da wani haqqi ko wani abu domin ya samu wani abin na daban, wanda zai haifar da maslaha a tsakani. Haka kuma akan samu ikon tabbatar da al’amari da tsayawa kai da fata sai an aiwatar da wani abu, domin fa’idarsa ga al’umma. An samu wannan a Jamhuriya Ta Huxu. A Tarayya da wasu Jihohi masu dama, an samu qarancin rikici da qarancin hairani tsakanin vangarorin biyu na Majalisa da Zartarwa. Domin fahimtar wannan, mutum ya duba yadda wasu gwamnoni a qarqashin PDP suka tafiyar da mulkinsu, inda za ka ga an mayar da Majalisar Dokoki ’yar amshin Shata. Jihohi da yawa sun faxa cikin irin wannan yanayi, inda ba a martaba tsarin mulki, babu bin tsarin doka da shari’a, musamman a gwamnatocin da suka gabata.

Rashin Jituwa Da Fito-Na-Fito: Wannan ma wata siga ce na yadda dangantaka ke kasancewa tsakanin vangaren Zartarwa da Majalisa. Wannan ya sha faruwa a Jamhuriya Ta Huxu, da musamman Jamhuriya Ta Biyu, inda a Jihar Kaduna dangantaka ta yi tsami tsakanin ’Yan Majalisar NPN da suka fi yawa har suka tsige Gwamna Abdulqadir Balarabe Musa na PRP. Haka ma a wannan Jamhuriyya da muke ciki, an samu barazanar tsige-tsige da rikice-rikice tsakanin vangarorin Majalisa da na Zartarwa har ma a matakin Gwamnatin Tarayya. Za mu iya tuna tata-vurzar da aka yi a lokacin Obasanjo da Majalisar Wakilai tsakanin 1999 zuwa 2003, inda har aka yi masa barazanar tsigewa. 

Za mu kammala makon gobe