Mu’assasatul Tarbiyyatil Islamiyya ta yaye dalibai

Makarantar Mu’assasatut Tarbiyyatil Islamiyya da ke Madinatu Irshad a Unguwar Zumrah, Suleja a Jihar Neja ta yi bikin yaye dalibanta karo na uku inda dalibai 22 suka yi saukar hadda yayin da 58 suka saukar karatun Alkur’ani Mai girma. A jawabin Shugaban taron kuma tsohon Ministan Shari’a Alhaji Abdullahi Ibrahim (SAN) ya yaba wa hukumar […]

Mu’assasatul Tarbiyyatil Islamiyya ta yaye dalibai
Mu’assasatul Tarbiyyatil Islamiyya ta yaye dalibai

Makarantar Mu’assasatut Tarbiyyatil Islamiyya da ke Madinatu Irshad a Unguwar Zumrah, Suleja a Jihar Neja ta yi bikin yaye dalibanta karo na uku inda dalibai 22 suka yi saukar hadda yayin da 58 suka saukar karatun Alkur’ani Mai girma.

A jawabin Shugaban taron kuma tsohon Ministan Shari’a Alhaji Abdullahi Ibrahim (SAN) ya yaba wa hukumar makarantar ne kan yadda take bayar da ingantaccen ilimi, inda ya yi alkawarin bayar da gudunmawar Naira miliyan daya, yayin da matansa biyu da ’ya’yansa za su bayar da Naira miliyan daya.
Babban Bakon Malami mai jawabi Sheikh Umar Al-Haidariy At-Tijaniy daga kasar Aljeriya wanda ya zo tare da dansa Sheikh Shareef Ahmad kuma Sheikh Sanusi Arze Kano ya yi wa tafinta ya yaba wa shugaban makarantar ne Sheikh Raji kan yadda yake hidima wa ilimi a tsawon rayuwarsa inda kananan yara suke karatu da haddace Littafin Allah a hannunsa.
Sheikh Alhaidariy ya ce wadannan samari sun rike tutar ilimi da Musulunci domin su ne manyan gobe, sai dai ya ce ba kowadanne samari ne za su zama manyan gobe ba, sai samarin da suka zamo masu neman ilimi da biyayya ga Sunnar Manzon Allah (SAW) kuma suka tsaya wajen yin aikin kwarai.
Tun farko a jawabin maraba, Shugaban Makarantar Sheikh Usman Raji ya gode wa wadanda suka halarci bikin ne kan amsa kiran shugaban tafiyar kuma mai hidima wa ilimi da malamai Sheikh Yusuf Abdullahi Lokoja.
Sheikh Raji ya ce gudanar da irin wannan taro jihadi ne kamar yadda Allah Madaukaki ya yi ishara a cikin fadinSa: “Lallai wadanda suka yi kokarin don neman shiriyarMu, Za mu shiryar da su hanyarMu, kuma lallai ne Allah Yana tare da masu kyautatawa.”
Sheikh Raji ya yi addu’ar Allah Ya saka da alheri marar yankewa ga dukkan wadanda suka halarci walimar tare da fatar Allah Ya ba Najeriya zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Tunda farko Sakataren Makarantar Malam Suleiman Lawal wanda Malam Muhammad Kaduna ya wakilta ya ce an kafa makarantar ce da izinin Sheikh Yusuf Abdullahi At-Tijjani Lokoja a 1987 a Unguwar Nufawa da ke garin Kaduna, kafin a dauke ta zuwa muhallinta na Unguwar Zumra (Ludurious Park) a Suleja bisa umarnin Sheikh Yusuf Lokoja a shekarar 2003.
Ya ce an gina makarantar ce don koya wa yara: Son Manzon Allah da son iyalan gidansa da kuma karatun Alkur’ani.
Ya ce makarantar wadda ta kwana ce kafin a kaddamar da sashin je-ka-ka-dawo a bara, tana da sassan da suka hada da iftida’iyya da mutawassida, inda yara ke fara haddar Alkur’ani, sai babban sashi da ake koyar da addini da boko har zuwa babbar sakandaren Musulunci.
Malam Suleiman ya ce suna da sashin koyar da sana’o’in da suka hada da ilimin kwamfuta da kafinta da walda da gyaran wutar lantarki da kanikanci da riwaya da gyaran janareta da dinki da kiwon kifi ko kaji.
Ya ce daliban makarantar da suka fito daga sassan kasar nan, a yanzu haka akwai da dama da suke karatu a jami’o’i da kwalejojin ilimi da kasashen waje.