Mu’assasin Cibiyar NTI, Hafiz Wali ya rasu

Fitaccen masanin ilimin nan Dokta​ ​Hafiz Sulaiman Wali, wanda ya kafa Cibiyar Ilimi ta kasa (NTI) da ke Kaduna ya rasu. Dokta Hafiz Wali ya rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano yana da shekara 81 bayan ya yi fama da jinya. “Marigayi mahaifina […]

Mu’assasin Cibiyar NTI, Hafiz Wali ya rasu

Fitaccen masanin ilimin nan Dokta​ ​Hafiz Sulaiman Wali, wanda ya kafa Cibiyar Ilimi ta kasa (NTI) da ke Kaduna ya rasu.

Dokta Hafiz Wali ya rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano yana da shekara 81 bayan ya yi fama da jinya. “Marigayi mahaifina ya rasu ne sakamakon kamuwa da rashin lafiya a mako biyu da suka gabata, kuma an kwantar da shi a asibitin Malam Aminu Kano, inda ya rasu,” inji dansa ​Aminu Hafiz Wali. ​

Marigayin ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya hudu da jikoki da dama.

Marigayin yayan Farfesa Sadik Suleiman Wali ne, wani tsohon likitan shugabannin Najeriya hudu.

Ya fara aikin koyarwa a Sakandaren Yerwa da ke Maiduguri kafin an mayar da shi makarantar koyar da sana’o’i ta Idah da ke Jihar Kogi a yanzu, sannan ya koma makarantar koyar da sana’o’i ta Mashi da ke Jihar Katsina a yanzu. 

Marigayin ya koyar a Kwalejin kere-kere ta Wudil kuma daga baya ya zama Sufeton ilimi a Kaduna kafin ya yi ritaya.