Mu’azu Magaji: Yadda baki yake yanka wuya

Ya sha wallafa sakonni a shafinsa na Facebook inda yake cacakar gwamnatin Ganduje.

Mu’azu Magaji: Yadda baki yake yanka wuya

Injiniya Muazu Magaji

A jiya Litinin ce wata Kotun Majistare da ke zamanta a Nomansland a Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji wanda aka fi sani da Dan-Sarauniya gidan gyaran hali.

An dai gurfanar da tsohon Kwamishinan wanda ake yi wa lakabi da Dan Sarauniya a gaban kotun bisa zarginsa da cin zarafin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Bisa ga wannan tuhuma ce Alkalin kotun, Mai Shari’a Aminu Gabari ya bayar da umarnin tisa keyarsa zuwa gidan dan Dan Kande sannan kuma ya dage zaman kotun zuwa ranar 3 ga watan Fabrairun 2022.

A wannan karo, lauya mai gabartar da kara Barista Wada A. Wada, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya nnata sunan Gwamnan a shafinsa na Facebook, inda ya sa hotonsa tare da wata mata.

Hakan, a cewar lauyan na nuni da cewa Gwamnan yana neman mata a waje ke nan, wanda a cewarsa irin wannan laifukan suna cin karo da sashe na 392 da 399 da 114 na kundin laifuka na ACJL.

Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifukan da ake zarginsa da su na bata suna da tayar da hankalin Gwamna da kirkirar karya .

Lauyan wanda ake kara, Barista Garzali Ahmad ya nemi kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa sakamakon rashin lafiya da ke damunsa, wacce ya hadu da ita a daidai lokacin da ’yan sanda ke kokarin kama shi, dogaro da sassa na 168 da 172 da kuma 174.

Sai dai lauyan mai gabatar da kara ya soki batun belin inda ya ce lauyan wanda ake karar ya gaza gabatar da kwararran hujjoji a kan batun rashin lafiyar wanda yake karewa da ya ce yana fama da ciwon kunne, don haka ya nemi kotun da ta yi watsi da bukatar tasa.

Haka kuma ya bayyana cewa bayar da belin wanda ake kara zai zama wani abu da zai kara wa matasa kwarin gwiwar cin zarafin shugabanmi da kuma mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Sai dai Aminiya ta yi waiwaye kan irin tababar da tsohon Kwamishinan ya rika shiga a baya, wanda galibi lafuzan da yake furtawa suka rika zame masa alakakai.

Mu’azu Magaji ya sha wallafa sakonni a shafinsa na Facebook inda yake cacakar gwamnatin Ganduje, wadda ya bayyana a matsayin wacce ba ta da alkibla.

A baya dai, Gwamna Ganduje, ya dakatar da tsohon Kwamishinan daga aiki bayan ya wallafa wasu sakonni da ake gani na murna ne da mutuwar Malam Abba Kyari, tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Najeriya wanda cutar Coronavirus ta yi ajalinsa.

Ana iya tuna cewa, a watan Afrilun 2020 ne bayan gudanar da bincike da gwamnatin Kanon ta yi kan sakon da ya wallafa da aka rika kallonsa a matsayin murna ga mutuwar Abba Kyari, kai tsaye Ganduje ta bakin Kwamishinan Labarai, Muhammad Garba ya bayar da umarnin sallamarsa.

Daga bisani bayan ya nemi afuwa kuma ya yi karin haske kan hakikanin ma’anar sakonsa da ya wallafa, Gwamna Ganduje ya sake ba shi mukami a matsayin Shugaban Kwamitin da zai jagoranci ayyukan samar da Bututun Iskar Gas a Jihar Kano.

Mu’azu Magaji wanda ya sha cewa ba murna ya yi da mutuwar Malam Kyari ba, ya ce murna ce yake taya mamacin murna saboda ya yi shahada kasancewar ya mutu a lokacin annoba.

A kan haka ne a wata hira da ya yi da BBC, Dan Sarauniya ya yi fashin baki kan kalmar Win-Win da ya yi amfani da ita, yana mai cewa, Abba Kyari ya yi shahada, wanda wannan nasara ce, sannan kuma mutuwarsa za ta ba da kofa a maye gurbinsa da wanda zai gyara kurakuran da aka tafka a ofishinsa na Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Najeriya yayin da yake raye.

Jahilai ne ke juya al’amuran siyasa da gwamnati a Kano —Dan Sarauniya

Injiniya Mu’azu Magaji, ya ce masu fama da duhu na jahilci ne ke juya akalar al’amura na siyasa da jagorancin al’umma a Jihar Kano.

Dan Sarauniya ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa kan shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 12 ga watan Janairun 2021.

A sakon nasa, ya bayyana damuwa dangane da yadda wasu marasa ilimin addini da na zamani ke cin karensu babu babbaka wajen jagorantar al’amura na siyasa a Kano duk da cewa akwai tarin Malamai kuma shi kansa Gwamnan Jihar, Abdullahi Ganduje yana da shaidar karatu ta digirin digirgir wato PhD.

Ya wallafa cewa, “Jahilci ba ado bane, illa ne ga rayuwa, ci gaba da zaman lafiyar al’umma.”

“Jiha kamar Kano da take da Gwamna mai PhD, mai ilimi da Malaman addini, a ce wasu tantirai…ba Arabi ba Boko ne ke juya akalar lamuranmu a siyasa da rayuwa! Da sake!”