‘Mugun gudu da abubuwan hawa ke kawo hadari a kasar nan’

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurruka ta kasa (FRSC) na shiyyar Saminaka a Jihar Kaduna, ACC Moses Audu ya ce mugun gudu da masu abubuwan hawa suke yi a kan hanyoyin kasar ne nan yake kawo hadarurrukan da suke faruwa. Kwamandan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron tunawa da ranar kungiyar […]

‘Mugun gudu da abubuwan hawa ke kawo hadari a kasar nan’
‘Mugun gudu da abubuwan hawa ke kawo hadari a kasar nan’

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurruka ta kasa (FRSC) na shiyyar Saminaka a Jihar Kaduna, ACC Moses Audu ya ce mugun gudu da masu abubuwan hawa suke yi a kan hanyoyin kasar ne nan yake kawo hadarurrukan da suke faruwa.
Kwamandan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron tunawa da ranar kungiyar Kiyaye Hadarurruka ta kasashen Afirka ta Yamma (WARSO) da hukumar ta shirya a garin Saminaka.
Ya ce mugun gudu ne yake kawo fashewar tayoyin abubuwan hawa wanda hakan yake jawo yawan hadarurruka. Ya ce hadarurrukan suna karya tattalin arziki domin ta hanyar hadari za a iya rasa ran mai mota da motar baki daya, ko kuma a kashe kudi mai yawa wajen yi wa wadanda suka ji rauni  jinya a asibiti.
Ya ce an gano kashi 80 zuwa 90 na hadarurrukan da suke faruwa a kan hanyoyin kasar nan suna faruwa ne kan irin halayenmu na mugun gudu. “Mugun gudu ne babban abin da yake kawo mana hadarurruka a kan hanyoyin kasar nan. Domin a lokacin da direba yake mugun gudu, taya tana iya fashewa, wanda hakan zai iya kawo hadari, irin abubuwan da suke faruwa ke nan a kan hanyoyin kasar nan. Don haka muke amfani da wannan rana wajen wayar da kan jama’a kan illolin mugun gudu ga direbobin. Muna kira ga masu abubuwan hawa su guji mugun gudu kuma su guji amfani da tsofaffin tayoyi, idan muka yi haka za mu samu saukin hadarurrukan da suke faruwa a kasar nan,” inji shi.
A jawabin Shugaban Riko na karamar Hukumar Lere, Alhaji Sani Tanimu ya mika godiyar karamar hukumar ce kan kakarin da jami’an hukumar kiyaye hadarurrukan suke yi wajen kare rayuka da dukiyar jama’a a yankin.
Shugaban wanda Kansilan Ayyuka na karamar Hukumar, Ibrahim danjuma ya wakilta ya ce suna ganin irin gudunmawar da jami’an hukumar suke bayarwa wajen ceto rayukan jama’a da zarar hadari ya faru a yankin. Kuma suna ganin irin yadda jami’an hukumar suke wayar da kan direbobi don kiyaye aukuwar hadari a yankin. Ya ba da tabbacin cewa karamar hukumar za ta taimaka wa hukumar a kan ayyukan da take gudanarwa a yankin.
Taro fadakarwar ya samu halartar wakilan kungiyoyindirebobin motoci na NURTW da RETAIN da sauran masu ruwa-da-tsaki a harkokin sufuri a yankin.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe