Mugunta fitsarin fako

Ra’ayin kamfanin jaridar barkwanci ta Hebdo a birnin Paris, da kuma harin da aka kai ma jami’an kamfanin a ‘yan kwanakin baya ya tayar da kura iri-iri daga wurare daban-daban, musamman ma daga masu kishin addinin Islama. Amma idan aka yi la’akari da kyau game da haka sai a fahimci irin kisisina da kutungwilar Yahudu […]

Mugunta fitsarin fako
Mugunta fitsarin fako

Ra’ayin kamfanin jaridar barkwanci ta Hebdo a birnin Paris, da kuma harin da aka kai ma jami’an kamfanin a ‘yan kwanakin baya ya tayar da kura iri-iri daga wurare daban-daban, musamman ma daga masu kishin addinin Islama. Amma idan aka yi la’akari da kyau game da haka sai a fahimci irin kisisina da kutungwilar Yahudu da nasara wajen yin batanci ga addinin Musulunci da kuma dimbin mabiyansa a fadin duniyar nan. kasar Faransa da kuma sauran kawayenta na nahiyar Turai sun ce abubuwan da jaridar Hebdo ke yi da gangar don shafa wa addinin Musulunci kashin kaji, wai ya dace da ‘yancin ra’ayin fadin albarkacin bakin ‘yan kasashensu. A cewarsu hakan ne ma sauran kasashen duniya da suka ci gaba suke ba talakawansu damar fayyace ra’ayinsu kan dukkan al’amura ba tare da wata tsangwama ba. Amma sai ga shi nan kuma a irin wadanan kasashen ana ba wasu damar kaje albarkacin bakinsu yadda suke so, wasu kuma ana muzguna masu don hana su furta kalamun kare mutuncinsu da kuma abin da suka yi imani da shi.

Jaridar Hebo dai ta bayar da dama ga masu ra’ayin kyamar addinin Musulunci su ci karensu ba babbaka, kamar yadda a ‘yan shekarun baya aka yi ta tsangwaman mutanen gabas ta tsakiya, musamman ma Yahudawa saboda kasancewarsu marasa bin addinin Almasihu. Dangane da haka ne wata kotu a kasar Faransa, a ‘yan kwanakin baya ta yanke hukuncin cewa wa zanen da wani fitaccen dan kasar Italiya da ya yi rayuwa fiye da shekaru 105, Lionel Da binci ya yi, wanda kuma aka siffanta shi da gyauton da Isa Almasihu ya yafa yayin cin abincinsa na karshe, aka yi talla da shi a kafafen yada labarai, cin mutunci ne na kin karawa ga abin da wasu mutane suka yi imani da shi.
Haka nan kuma a shekarar 2005 an yi wani zanen wata “LIMAMIYAR” ja-gabar addinin Kirista don bayyana wata manufa ta yaki da cutar kanjamau wanda ya nuna ta kai da kuma kafadun matar sanye da kallabin limamiyar coci hade da wasu kwaroron roba guda biyu da ake amfani da su yayin jima’i. Hakan ya tayar da gagarumin yamutsi, saboda an danganta wannan manufa da addinin Kirista, kuma ba tare da bata lokaci ba kotun kasar Faransa ta hukunta wanda ya yi wannan zanen.
To, amma ai idan ba a mance ba ita wannan jaridar, Hebdo ta taba hukunta wani ma’aikacinta, ta kuma nemi gafarar dan tsohon shugaban kasar Faransa, Nicholas Sarkozy da kuma uwargidansa, Jessica Sebaoun Darty saboda da cin mutuncin da aka yi musu a cikin jaridar, amma sai ga shi nan a yanzu jaridar ta dage kan cewa ita tana kare hakkinta ne na fadin albarkacin bakinta. Haka nan kuma a kotun kasar Faransa ta taba hukunta wani marubuci da ya yi batanci ga Yahudawa, musamman ma wadanda Adolf Hitler ya halaka sa’ilin yakin duniya na biyu, wadanda ya ce gara da aka yi musu haka domin kuwa dukkansu ‘yanwuta ne.
A kasar Faransa akwai dokar da aka kafa ta a shekarar 2003, wacce ta yi tanadin tarar Yuro 9,000, ga wanda duk ya muzanta tutar kasar, ko kuma ya ki rera taken kasar a wuraren da ake yin tarurruka, ko kuma ya tafi gidan maza, ya ci gabza na tsawon watanni shida. Baicin haka nan kuma akwai wata dokar da ta haramta cin mutuncin dukkan wani mahalukin da ya taba yi wa kasar Faransa hidimar da ta daukaka matsayinta. To, amma idan har kasar Faransa za ta hukunta wadanda duk suka wulakanta sunayen wasu fitattun ‘ya’yanta, watau Napoleon Bonaparte da kuma Charles De Gaulle, sai ga shi nan Faransa ba ta damu da yadda aka ci mutuncin Manzon Allah (SAW) ba, mutumin da ya kasance haske ga duniyar nan, kuma wanda ya idar da sakonni da hukunce-hukuncen Mahalicci, don jama’a su kasance bisa mikakkiyar turbar shiriya.
Musulmin duniya baki daya ba su goyon kisan kai muddin dai ba bisa tsarin shari’a ne ba, kuma Musulmi ba su goyon cin fuska ko cin mutuncin kowane mutum, Musulmi ko kuma mabiyin wani addini ne can daban. Ya kamata kasar Faransa ta fahimci cewa ba daidai ba ne ta kafa dokar da ba za ta yi aiki akan wsu ba, sai wadanda kawai ta kI jini ko take kyama. Idan da ita ma ana yi mata haka a kasashen Musulmin duniya, musamman ma wuraren da ta shimfida mulkin mallaka ai da ba haka ba. Faransa dai ta mulki kasashe sama da sittin a duniya, kuma ko da yake sun samu ‘yancin gudanar da harkokinsu, amma har yanzu ita ce ke karkata harkokin tattalin arzikinsu, ita ce kuma ke tastesu yadda ta ga dama, sa’annan kuma sai tafarkin siyasar da ta gwada musu za su bi. Idan har da wadancan kasshen da kum sauran da take cin moriyarsu za su juya mata baya, ai cikin dan kankanen lokaci za ta gamu da karayar arziki, mutuncinta kuma ya zube warwas.
Musulmin duniya dai masu hakuri da son zaman lafiya, kamar yadda addininsu ya koya masu, kuma wajibi ne sauran kasashen duniya su fahimci haka, su kuma gane cewa yanzu addinin Musulunci ke kara yaduwa yake yi a kasashensu kamar wutar daji a lokacin hunturu. Dalili kuwa, shi ne, jama’ar nahiyar Turai da Amurka sun fahimci cewa Musulunci shi ne addinin adalci da sanin ya kamata da kuma bin turbar gaskiya, kuma shi ne mafita daga matsalolin da kasashensu ke fama da su. Saboda haka nan idan har suka ce za su ci gaba da yakan Musulunci ko muzgunawa bayinsa, to da jama’ar kasarsu za su yi, domin cikin dan kankanen lokaci fiye da rabin jama’an kasashensu za su rungumi Musulunci, su kuma kyamaci wadancan dokokin da suka saba da’a da sanin ya kamata, wadanda tsire su da zimmar muzgunawa dan Adam, amma da sunan kare masa hakki.