Muhammad Auwal Ijakoro ne sabon Sarkin Bwari

Ministan Abuja malam Muhammad Musa Bello, ya tabbatar da nada Alhaji Muhammad Auwal Ijakoro a matsayin sabon sarkin Bwari. Sabon sarkin wanda shi ne babban da ga tsohon sarki, marigayi Alhaji Musa Muhammad Ijakoro, shi ne dama ’yan majalisar zaban sarki su ka mika sunansa ga minisatan kwanaki kalilan bayan rasuwar mahaifinsa a ranar 29 […]

Muhammad Auwal Ijakoro ne sabon Sarkin Bwari

Ministan Abuja malam Muhammad Musa Bello, ya tabbatar da nada Alhaji Muhammad Auwal Ijakoro a matsayin sabon sarkin Bwari. Sabon sarkin wanda shi ne babban da ga tsohon sarki, marigayi Alhaji Musa Muhammad Ijakoro, shi ne dama ’yan majalisar zaban sarki su ka mika sunansa ga minisatan kwanaki kalilan bayan rasuwar mahaifinsa a ranar 29 ga watan Agusta ta wannan shekara, kuma ya riki mukamin ciroman Bwari gabanin nadin, wanda a ka tabbatar a ranar Talata da ta gabata.

An haifi sarkin ne a ranar 9 ga watan Yuni ta 1977, ya kuma halarci makarantar Firamare ta Anguwar Gayan da ke garin Suleja a tsakanin shekarar 1984-1989, sannan ya kammala makaraantar Sakandaren Gwamnati (GSS) ta Kwali Abuja, a 1997. Ya kuma yi Difloma a sha’anin gudanar da mulki a jami’ar Abuja a 2003, sannan ya yi digiri a bangaren a jami’ar Jihar Nassarawa da ke Keffi. Sarki Muhammad Auwal Ijakoro na da mata biyu da ’ya’ya 5.

Bayanai sun ce alamun za a nada sarki sun fara bayyana ne tun a ranar Litinin a lokacin da labarin hakan ya fara zuwa fadar, sannan aka wayi gari da tarin jami’an tsaro na soja da kuma farin kaya a ranar Talata wadanda su ka rika sintiri a garin, kafin tawagar minista ta shigo fadar da misalin karfe 2 na ranar inda ta nemi ganinsa sannan aka mika masa takardan tabbacin nadin. Babu dai labarin wani bore a garin har zuwa lokacin hada wannan labarin a ranar Laraba, sai dai shagulgulan da a ka ci gaba da yi a fadar, da kuma karban gaisuwa daga manyan mutane da ke ta shigowa.

Garin Bwari wanda ke da masarauta biyu wato masarautar sarki wanda kabilar Koro ce ke mulkanta da ta fara sarauta tun a shekara ta 1902, da kuma ta Esu Bwari da kabilar Gbagyi ke mulka, ta samu kanta a halin takaddamar sarauta a tsakanin masarautun biyu tun a shekara ta 1997 a lokacin da minstan Abuja na lokacin Jeremiah Useni ya bai wa Sarki Ijakoro sandar girma mai daraja ta biyu, kafin daga bisani aka daga sarautar bangaren Esu daga matakin dagaci zuwa hakimci a matsayin don kwantar da hankali. 

Sai dai bayan rasuwar sarki Ijakoro bangaren Esun ya nemi da a kawo karshen masarautar Sarki kan ikirarin cewa su baki ne sannan Gbagyi ce ta kafa garin. Aminiya ta gana da Esu Bwari J.P Ibrahm Yaro bayan tabbatar da nadin inda ya bayyana al’amarin a matsayin danniya ga al’ummarsa. Esu ya ce ba daidai bane gari daya ya ci gaba da kasancewa da masarautu biyu. “Bayan rasuwar sarki mun yi rubuce-rubuce a kan hakan tare da mika bayanin mu ga hukuma. 

“Irin haka ya faru a Kwali sannan kwamitin da ministan Abuja na lokacin ya kafa ya bada shawaran da a kawo karshen masarautar kuma a ka yi amfani da shawaran. Mun dauka irin wancan adalcin za a yi mana a nan. “Ba wani mataki da za mu dauka, mun bar komi ga Allah kuma tini na nemi al’ummata da su yi hakuri su bar wa Allah komi, inji Esu Bwari.