Muhammad Elsayed Ali Muhammad: Bamisiren da ke nazartar jaridun Hausa

A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa, bai taba zuwa Nijeriya ba, yanzu kuma yana da shekara 36.

Muhammad Elsayed Ali Muhammad: Bamisiren da ke nazartar jaridun Hausa

An yi jarrabawar kare kundin digiri na biyu mai taken: ‘Jarida ta siyasa: Nazari a kan Harshe’, wanda mai bincike Muhammad Elsayed Ali Muhammad malami mai koyar da harshen Hausa a Sashen Harsunan Afirka a Babbar Kwalejin Nazarin Harkokin Afirka a Jami’ar Alƙahira da ke kasar Masar ya yi.

Ya yi jarrabawa a kan kundin ne a ranar Lahadi 10 ga Maris, 2024, bayan gama zaman tattaunawa game da bincike a farfajiyar tsangayar, mai binciken ya samu shaidar karatun digiri na biyu mai daraja ta farko (Excellent).

Kwamitin zaman tattaunawar ya ƙunshi malamai kamar haka: Mai duba binciken, Farfesa Sabry Salama, farfesa a Harshen Hausa da Adabinsa a Tsangayar Nazarin Harkokin Afirka mai zurfi – Jami’ar Alƙahira da Farfesa Khaled Fahmy Ibrahim, Farfesa a fannin Kimiyyar Harsuna, Tsangayar Adabi – Jami’ar Menoufiya.

Haka kuma, kwamitin ya haɗa da Farfesa Samir Ezzat Ibrahim, Farfesa a fannin Nazarin Harsuna da Harshen Hausa a Tsangayar Nazarin Harkokin Afirka mai zurfi – Jami’ar Alƙahira da kuma Farfesa Adel Othman Imam, Farfesa a sashen Harsunan Afirka, a Tsangayar Harsuna da Fassara, Jami’ar Al-Azhar.

Bangaren da ya yi binciken

Binciken ya yi nazari ne tare da yin tsokaci kan manyan abubuwa da dama kamar:

Na farko: Tantance tsarin jimlar taken jarida ta siyasa a Harshen Hausa, wadda ta ƙunshi jimla marar aikatau da mai aikatau da nazartar tsarin ginin jimlar taken jarida ta siyasa, ta hanyar nazarin Bishiyar Li’irabi, don yin ƙarin haske a kan ƙa’idojin harshe game da taken jarida.

Na biyu: Bayyana hanyoyin gamsarwa ta hanyar amfani da kalmomi da kuma ginin jimla da irin tasirinsu ga mai karatu da kuma yadda mai aikin rahoto wato dan jarida yake zaɓar mafi kyawun kalmomi don gamsar da mai karatu, tare da sanya su cikin mafi kyawun ginin jimla bisa tsarin Nahawu don fitar da mafi kyawun saƙo da zai gamsar a taken jarida.

Na uku: Hanyoyin gamsar da mai karatu da mai aiko da rahoto dan jarida ke bi da kuma yadda ɗan jarida ke iya ɓoye manufarsa ko bayyana ta a taken jarida cikin basira da ƙwarewa, gwargwadon yadda ake buƙata a taken.

Haka kuma binciken ya dubi hanyoyin da ake bi wajen gamsar da mai karatu ta hanyar amfani da alamar rubutu da kuma rawar da take takawa wajen gamsar da mai karatu.

Alamar kuma za ta iya kasancewa a nau’in harufan da aka yi amfani da su wajen rubuta taken da launukan rubutun da hoton bangon jaridar da sauransu.

Amfani da Aminiya a matsayin madogara

Abin da ya kamata a sani shi ne, mai binciken ya yi amfani ne a cikin binciken nasa da mafi yawancin taken jarida na siyasa a Jaridar Aminiya ko dai ta shafinta na Intanet ko kuma kwafin jaridar da ake fitarwa a mako-mako.

Haka kuma mai binciken ya amfana da ita sosai domin kasancewar tana da manyan ’yan jaridar Hausa da suka yi fice da ƙwarewa a fannin ilimin harshe wajen rubuta kanun labaran siyasa a harshen Hausa.

Tarihin mai bincike

An haife shi ne a 1988 a birnin Almansoura da ke ƙasar Masar.

A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa, bai taba zuwa Nijeriya ba, yanzu kuma yana da shekara 36.

Amma, “Ina da burin ziyartar Nijeriya nan da wani lokaci nan kusa. Ina so in zo in kewaya jami’o’in da ke kasar, sannan kuma in samu ƙwarewa a kan Harshen Hausa kamar yadda Hausawan asali suke magana da kuma gudanar da rayuwa.

“Abin da ya ja hankalinsa zuwa Hausa Game da abin da ya ja hankalinsa, cewa ya yi, “Hausa yare ne da ya watsu a wurare da yawa, kuma ake karanta shi a jami’o’i daban-daban na duniya, sannan adadin masu magana da shi na da yawa sosai.

“Wannan ne ya ja hankalina zuwa wannan harshe na Hausa,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Hakan ya sa na yanke shawarar karantar harshen, domin samun kwarewa a kansa, har na samu aiki a tsangayar da ake karantar da ita a Jami’ar Alkahira da ke Masar.”

Za a iya samun Muhammad Elsayed Ali ta imel: [email protected]