Muhammad Hosni Mubarak (1928 zuwa 2020)

Ranar Talata 25 ga watan Fabrairun bana, tsohon Shugaban Kasar Masar Muhammad Hosni El Sayed Mubarak ya rasu a wani asibitin sojoji da ke birnin Alkahira bayan fama da doguwar jinya, ya rasu yana da shekara 91.  Ya mulki Masar daga ranar 14 ga Oktoban 1981 zuwa 11 ga  Fabrairun 2011 wanda ya zama shi […]

Muhammad Hosni Mubarak (1928 zuwa 2020)
Muhammad Hosni Mubarak (1928 zuwa 2020)

Ranar Talata 25 ga watan Fabrairun bana, tsohon Shugaban Kasar Masar Muhammad Hosni El Sayed Mubarak ya rasu a wani asibitin sojoji da ke birnin Alkahira bayan fama da doguwar jinya, ya rasu yana da shekara 91. 

Ya mulki Masar daga ranar 14 ga Oktoban 1981 zuwa 11 ga  Fabrairun 2011 wanda ya zama shi ne Shugaban Masar na hudu, kuma Shugaba mafi dadewa a kan karar mulki tun bayan samun ’yancin kan kasar.

Ya kasance Mataimakin Shugaba ga Anwar Sadat, wanda sojoji suka harbe shi ranar 6 ga Oktoban 1981, lokacin yana duba faretin sojoji don tunawa da fafatawar da sojin Masar suka yi da kasar Isra’ila a 1973. 

Kafin ya shiga harkokin siyasa, Mubarak yana daya daga cikin zaratan sojin saman kasar inda daga baya ya zama kwamandan wannan runduna, ya kasance daya daga cikin sojojin saman da suka fafata da kasar Isra’ila a 1973, wanda wannan ya jawo masa shahara a fadin kasar. Har ta kai Shugaban wancan lokacin ya nada shi Mataimakin Shugaban Kasa.

Bajintar da Mubarak ya yi ta jawo masa daukaka a fadin Masar wanda Shugaba Anwar Sadat, ya nada shi Mataimakinsa a cikin watan Afrilun 1975. Tun daga wannan mukami ya zama ana damawa da shi a cikin harkokin kasar, inda ya jagoranci tattaunawar da aka yi a tsakanin kasar Masar da Isra’ila wanda kasar Amurka ta shiga tsakani tattaunawar da aka yi mata take da Yarjejeniyar Camp Dabid domin samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu a 1977.

Mubarak ya maye gurbin Anwar Sadat a matsayin Shugaban Kasar a cikin wani yanayi na rudani da kasar ta shiga. Wanda hakan ya jawo wadansu a kasar suke ganin yarjejeniyar da aka kulla da Isra’ila ta jawo faruwar wannan domin suna ganin a cikin sojoji akwai masu adawa da wannan yarjejeniya da aka kulla da Isra’ilar.

 Kisan gillar da sojoji suka yi wa Anwar Sadat da Laftana Islambouli ya jagoranta ta nuna cewa a cikin sojin akwai masu jin haushin wannan yarjejeniya da Masar ta yi da Isra’ila, wannan ya jawo kasashen Larabawa suka dakatar da kasar Masar daga cikin kungiyarsu ta Kasashen Laraba (Arab League).

Kasar Masar ta  amfana da mulkinsa, kasancewar Mubarak na daya daga cikin masu rajin kawo ci gaban zamani a kasar ba ya ga mawuyacin halin da Masar ta tsinci kanta a ciki. Mubarak ya amfanar da Masar domin ya kasance mutum mai saukin kai wanda ba ya son ayaniya. Ya yi kokarin sauka daga mukamin Shugaban Kasa saboda ya kawo daidaito, lura da yunkurinsa na kawo sauyi a bangaren siyasa da walwalar jama’ar Masar da kuma kokarin dinke barakar da ke tsakanin kasarsa da kasashen Larabawa domin a ci gaba da mu’amala da su. Wannan ya kawo karshen dakatarwar da kasashen Larabawa suka yi wa Masar a 1989.

A lokacin da Mubarak yake mulkin Masar ya kawo ci gaba mai yawa da suka hada da samar da masana’antu da gina hanyoyi da gidaje da sauransu da kuma kawo ci gaba ta bangaren bunkasa ilimi da harkokin lafiya. Wanda har sai da Masar ta zama daya daga cikin kasashe masu ci gaba a bangaren tattalin arziki a duniya.

Ya kuma taimaka wa kasar Masar ta zama daya daga cikin masu fada- a-ji a Gabas ta Tsakiya inda ta taka rawar gani a lokacin da Iraki ta mamaye Kuwait da Yakin Gulf sannan ta kasance mai sa-ido a kan abin da ke faruwa tsakanin Falasdinawa da Isra’ila.

Har ila yau, cikin ci gaban da ya kawo wa Masar ya cancanci yabo. Musamman yadda ya tunkari magance matsalar matasa, lura da yadda kasar take fama da karuwar yawan jama’a. Ya yi namijin kokari wajen bin doka domin tunkarar matsalar da kasar Masar take ciki  lura da yadda wasu suke korafin an bar su a baya a bangaren ci gaban tattalin arzikin kasar.

A lokacin da makwabciyar kasar wato Tunusiya ta shiga cikin matsin tattalin arziki wanda ya jawo mummunar zanga-zangar a kasar da ta fantsama cikin kasashen Larabwaa, ita ma Masar ta yi fama da wannan zanga-zangar da ta yi sanadiyar  kubucewar mulki daga hannun Mubarak a shekarar 2011.

Mu a nan Afirka, za a ci gaba da tunawa da Mubarak saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen taimaka wa Kungiyar Tarayyar Afirka  (AU). A lokacin yana mulki, Masar ta zama daya daga cikin kasashe masu fada-a-ji a Nahiyar Afirka. Sannan ya taimaka wajen kawo hadin kai ga kasashen Afirka. Haka zalika kasar Masar ta kulla dangantaka a lokacinsa ta kut-da-kut da Najeriya, an samu yawan masu kawo ziyara a tsakanin kasashen biyu da kuma kulla yarjeniyoyi masu yawa.

Lura da irin ayyukan alheri da ya yi a rayuwarsa, duk da kowane dan Adam ba a rasa shi da kura-kurai, muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya yafe masa kura-kuransa kuma Ya sa shi daga cikin ma’abuta Aljannar Firdausi, amin.

 

 

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos