“Muhammad” ya zama sunan da aka fi sanya wa jarirai a Wales da Ingila a 2025

Wannan shi ne karo na uku a jere da sunan ‘Muhammad’ ke yin shura a Wales da Ingila.

“Muhammad” ya zama sunan da aka fi sanya wa jarirai a Wales da Ingila a 2025

Muhammad ya sake zama sunan da aka fi raɗa wa jarirai maza a Ingila da Wales a shekarar 2025.

Hukumar ƙididdiga ta Birtaniya (ONS) ce, ta bayyana hakan cikin rahoton da ta fitar kan sunayen da aka fi sanya wa yara a shekarar da ta gabata.

Wannan shi ne karo na uku a jere da sunan Muhammad ke zama sunan da aka fi sanya wa jarirai maza a Ingila da Wales.

Sunan ya kasance na farko a shekarun 2023, 2024 da kuma 2025.

Rahoton ya nuna cewa an sanya wa jarirai maza 5,957 suna Muhammad a shekarar 2025.

Haka kuma wasu hanyoyin rubuta sunan kamar Mohammed da Mohammad su ma sun shiga cikin jerin sunayen da aka fi amfani da su.

Sunan Mohammed ya zo na 20, inda aka sanya wa yara 1,712 wannan suna, yayin da Mohammad ya zo na 55, bayan an raɗa wa yara 895 sunan.

Masana sun ce ba abin mamaki ba ne ganin sunan Muhammad ya ci gaba da kasancewa a matsayi na farko, saboda sunayen da suka shahara kan ci gaba da zama sanannu na tsawon lokaci.

Clare Green, wata masaniyar sunayen jarirai, ta ce idan wani suna ya samu karɓuwa a tsakanin mutane, hakan kan sa iyaye su riƙa zaɓar shi saboda suna yawan jin sa.

Ta bayyana cewa yawan amfani da wani suna na iya sa ya ƙara yaɗuwa, domin iyaye sun fi son sunayen da suka saba ji ko suka ga wasu suna amfani da su.

Sauran sunayen da suka yi fice

Bayan Muhammad, sunayen jarirai maza da suka fi shahara a Ingila da Wales sun haɗa da:

  • Noah
  • Leo
  • Luca
  • Arthur
  • Oliver
  • George
  • Oscar
  • Theodore
  • Freddie

A ɓangaren jarirai mata kuwa, sunan Olivia ne ya ci gaba da zama na farko, inda ya shafe shekaru 10 a kan gaba.

A shekarar 2025, an sanya wa jarirai mata kusan 5,000 wannan suna.

Sauran sunayen mata da suka yi fice sun haɗa da Lily, Amelia, Isla, Florence, Freya, Poppy, Elsie, Ivy da Isabella.