Muhammadu Issoufu Ne Ya Kitsa Juyin Mulkin Babana —’Yar Bazoum
’Yar hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, ta zargi wanda mahaifinta ya gada, Muhammadu Issoufou da kitsa juyin mulkin da sojoji suka yi wa mahaifinta watanni tara da suka wuce. An tsare Bazoum da matarsa a fadar shugaban kasa da ke Yamai tun bayan da sojoji suka kwace mulki a ranar 26 ga watan Yuli, […]
’Yar hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, ta zargi wanda mahaifinta ya gada, Muhammadu Issoufou da kitsa juyin mulkin da sojoji suka yi wa mahaifinta watanni tara da suka wuce.
An tsare Bazoum da matarsa a fadar shugaban kasa da ke Yamai tun bayan da sojoji suka kwace mulki a ranar 26 ga watan Yuli, 2024.
A wata hira da Hinder Bazoum ta yi da BBC, ta zargi Muhammadu Issoufou, tana mai cewa yanzu watanni shida ke nan rabon da su samu labarin iyayensu ko halin da suke ciki.
“Akwai abin mamaki ƙwarai da gaske a ce Mahamadou Issoufou ne wanda ya kitsa kifar da mulkin babana saboda son zuciya da kuma kare muradunsa na kashin kai.
“Akwai bacin rai ka gano cewa wanda ya cutar da kai wani ne da ka san shi ya sanka kuke mu’amalar arziki da shi.
“Abin ba daɗi a ce wanda ya rayu da mahaifunmu sama da shekaru 33, ya san haihuwarmu, ya san tashinmu, yau shi ne ya cutar da mu.
“Shi ne ya yi wa mahaifinmu juyin mulki, shi ne ya ci amanarsa; kuma muna da shaidar cewa Mohammadou Issoufou ne ya hana gwamnatin mulkin soja sakin mahaifinmu.
“An mayar da mu marayu, kuma ba wanda muke zargi sai tsohon abokin mahaifinmu, tsohon shugaban Nijar, Mohamadou Issoufou”.
Abdulmumini Gusmani, daya daga cikin na hannun daman tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa watanni tara tun da sojoji suka yi wannan juyin mulkin sun kasa gabatar da gamsassun hujjoji da ke tabbatar da ikirarin nasu.
Shugaban sojin Janar Abdourahamane Tchiani babban amini ne kuma sanannen aminin Muhammad Issoufou ne.
Hamɓararren shugaban ƙasar Nijar ɗin Muhammad Bazoum ya taba riƙe ministan cikin gida kuma na hannun daman Issoufou, wanda ya sauka bisa radin kansa bayan wa’adi biyu.