Muhammadu Kazallah: Jarumin da Sarki Dikko ya aro daga Kano

Lokacin da Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya zama Sarkin Katsina mutane da dama ba su sonsa, har ma ana sanya hula a gaban goshi ana yi mata kirari da ‘’sarautar Dikko ba ta zauna ba.’’ Amma Sarki Dikko ya bi da mutanen Katsina ta hanyar amfani da tsabar hikima, wadansu da karfin iko,wadansu kuma da […]

Muhammadu Kazallah: Jarumin da Sarki Dikko ya aro daga Kano
Muhammadu Kazallah: Jarumin da Sarki Dikko ya aro daga Kano

Lokacin da Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya zama Sarkin Katsina mutane da dama ba su sonsa, har ma ana sanya hula a gaban goshi ana yi mata kirari da ‘’sarautar Dikko ba ta zauna ba.’’ Amma Sarki Dikko ya bi da mutanen Katsina ta hanyar amfani da tsabar hikima, wadansu da karfin iko,wadansu kuma da lalama.
A lokacin kasar Katsina cike take da hatsabibai, sai sarki ya isa zai iya tafiyar da mutanenta, domin tun a wancan lokacin sun san suna da‘yanci, sannan ga shiri, kowane irin abu kake ji da shi sai ka iske shi a Katsina, har kirare ake wa garin ana cewa, Katsina garin shedanu, garin waliyai.
Dikko jarumi ne da ya rika gayyato jarumai daga wadansu masarautu domin su zo su zamar masa ’Yan Fada. Ya yi auratayya,a cikin matansa har da kanwar Sarki Kano Abdullahi Bayero.
Daga cikin jaruman da ya gayyato suka zauna tare da shi akwai Muhammadu Kazallah wanda da Sarki Dikko ya nemi Sarkin Kano- Abdullahi Bayero ya ba shi wani hatsabibi a cikin masarautarsa wanda zai zaunar da shi dindindin a fadarsa, sai Sarkin Kano ya ba shi Muhammadu Kazallah wanda mutumin kasar Tofa ne,a gundumar Kadandani. Yana daya daga cikin wadanda ake ji da su a fadar Sarkin Kano a lokacin. Asalinsa zuriyar shahararren matafiyin nan ne, kuma marubuci mai suna Ibn Batuta.
Muhammadu Kazallah ya yi farin cikin tura shi Katsina, don dama yana son garin, saboda akwai ‘yan uwansa da yawan suna karatun addinin Musulunci a Katsinan. Zuwansa kuma, ya sa wadansu danginsa suka taso daga kauyuka suka koma cikin birnin Katsina da zama.
Muhammadu Kazallah mutum ne karkarfa,jarumi kuma hatsabibi, masanin sihiri da asirai, babu wani makami da ke ratsa jikinsa, yana iya sarrafa barawo ko mai laifi, idan ya ce ‘’zauna nan’’, sai ya zauna, ‘’mu tafi’’ sai ya tafi.
Sarkin Katsina Muhammadu Dikko yana ji da shi, kuma yana takama da shi, asali ma idan ya fito sai ya tabbatar yana nan.
Idan Kazallah yana son ya sanyaya zuciyar Sarki a Fada, sai ya tashi tsaye ya yi masa kirari, a cikin kirarin ya kan fada masa cewa, “Me zai iya daga maka hankali bayan ga mu a gabanka?”
A lokacinsa ya hana barayi sakat a Katsina saboda idan Kazallah ya je wajen da aka yi sata ya ga sawun barawon sai ya gano shi, sai kuma ya kamo shi. Akwai lokacin da ya taba fadowa daga saman gidansa wajen gyaran damina, aka zo za a tafi da shi don a gyara shi, sai matarsa ta ce, a aje mata abinta a daki, daga wannan lokacin aka san tana dori, kuma wani abin al’ajabi, ta dora shi ta yadda ya fito da karfinsa kamar ba shi ne wanda ya fado daga sama ba.
Kamar yadda Sarkin Zagin,Sarkin Katsina Alhaji Mamman Na Kaduna mai shekaru 83 ya fada, ya ce, a lokacin da suke da kuruciya kowa so yake ya samu daukaka kamar Kazallah, da ka ji sunansa sai ka ji yana burge ka, idan ka ganshi ka ga iko. A wancan zamanin kowane dogari yana da doki, kamar yadda a yau ya kamata kowane dogari ya zama mai mota. Sannan akwai lokacin da aka sauya wa dogarai kaya, kayan nan ja da kore, sai aka ki sawa, ganin haka sai wata safiya Sarki Dikko ya sa kayan dogarai, ganin haka duk dogarin da ya ganshi da kayan sai ya koma ya sa nasa, a haka kayan suka karbu har suka zama kayan dogaran Katsina. Kuma daga nan kowane gari a kasar Hausa suka bi tsarin.
Kazallah malami ne, wanda ya karantu sosai, yana jin Larabci, kusan yana yawan sa baki a tattaunawar matsalar Musulunci a fadar sarki. Sunansa ya bace a tarihi, don bai taba haihuwa ba,tun zamanin Sarki Dikko yake fadar Katsina, ya rasu a lokacin Sarkin Katsina Usman Nagogo, ya rasu yana da shekaru 75 a duniya,bayan ya kwashe shekara biyar yana jinya, iyalensa sun ce a kullun yana cikin salati da Istingifari a tsawon wannan shekarun.
kanwar matarsa wadda har yau tana raye ta fada cewa ya rika addu’ar cewa, “Allah ba ka ba ni zuri’ar da za su rika tunani ba, Allah kar ka shafe sunana a  manta da ni, Allah ka sanya a tuna da ni a wata rana da ayyukan da na yi wa Katsina da Katsinawa.”
Wani shahararren mawakin a wancan zamanin, mai suna dan-Mani a shekarar 1952 ya yi wata shahararriyar waka da aka sanya mata Bakandamiya a lokacin, inda yake wa wani Alkali zambo lokacin da yake neman raba masa aure har aka je gaban Sarki, a cikin wakar yana cewa, ‘’Dubi Kazallah ya manta mu! Yana magana baki na kumfa!! Dakare a gaban-sarki bai tsoron kowa!!!’’ wannan waka ta kara fito da sunan Kazallah a kasar Katsina.
Wamban Katsina, Alhaji Abba Kalli, daya daga cikin wadanda suka yi zamani da Kazallah ya tabbatar da cewa Kazallah, “Jarumi ne na gaban Sarki, a lokacin babu kamarsa a cikin Dogarai. Ba ya rabuwa da takobinsa sai idan zai kwanta barci, kuma a kullun a shirye yake, idan za a kama kangararre shi ake turawa, sannan shi yake tsare masu aiki a gonar sarki, kuma ko ‘yan uwansa dogarai na shayinsa!, yayin da suke yi masa kirari su ce, “Ina maza suke” sai ya amsa “Ga mu nan”.
Sunansa ya fito a cikin rubuce-rubucen Turawan Mulkin Mallaka a kan Katsina, hotonsa da aka yi amfani da shi a cikin rahoton wani Bature ne ya dauke shi a shekarar 1960, kuma aka buga shi a jaridun Ingila da taken “Siffar masu ba saraki kariya a kasar Hausa”.
Ya kamata marubutan tarihin Katsina su binciko irin wadannan gwaraza don saninsu kamaryadda aka rubuta littafin Kano mai suna “Bayi a Gidan Dabo,” wanda Nasiru Wada ya wallafa a shekarar 2012.