Muhawarar da ake shirya wa ’yan takarar shugabancin kasa tana da amfani kuwa?

A yayin da zabe ke karatowa, kowace jam’iyya na bayyana manufofinta ga al’ummar kasa. A lokacin ne kuma wasu kafafen watsa labarai ke shirya muhawara ga ’yan takarar shugabancin kasa da mataimakansu na jam’iyyu daban-daban. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko irin wannan muhawara tana da amfani kuwa? Ga abin da mutane ke […]

Muhawarar da ake shirya wa ’yan takarar shugabancin kasa tana da amfani kuwa?
Muhawarar da ake shirya wa ’yan takarar shugabancin kasa tana da amfani kuwa?

A yayin da zabe ke karatowa, kowace jam’iyya na bayyana manufofinta ga al’ummar kasa. A lokacin ne kuma wasu kafafen watsa labarai ke shirya muhawara ga ’yan takarar shugabancin kasa da mataimakansu na jam’iyyu daban-daban. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko irin wannan muhawara tana da amfani kuwa? Ga abin da mutane ke cewa:

Muhawarar na da amfani
– Badamasi Saleh

A. A. Masagala, a Benin

Alhaji Badamasi Saleh: “Ni a ganina, muhawara tsakanin ’yan takarar shugabancin kasa za ta amfani al’ummar kasa, idan suka tsaya a kan gaskiya ga alkawuran da za su daukar wa jama’arsu. Don haka ni abin da na fahimta shi ne, duk wani bayani da suka kudurta yana nan, tamkar alkawari ne tsakaninsu da al’ummarsu kuma shaida ce ga magoya bayansu da sauran al’ummar kasa baki daya. Don haka shirin yana amfani muddin shugabannin suka bi shirin cikin tsoron Allah, suka cika alkawura to lallai kome zai tafi daidai kuma zai amfani jama’ar kasa.”

Muhawarar ba ta da amfani – Lawan Muhammad

A. A. Masagala, a Benin

Lawan Muhammad Inuwa: “Abin da na gani game da wannan muhawara, manyan kasashe da suka ci gaba sun dade da wannan shirin, inda ’yan takara na kowace jam’iyya zai fito ya bayyana wa magoya bayansa irin aikin ci gaba da zai yi wa kasarsa. Saboda haka ina ganin a kasashe wadanda suka ci gaba, yana da amfani kwarai da gaske; domin yana bai wa al’umma damar fahimtar irin shugabancin da za a yi musu da kuma irin shugabannin da za su jagorance su. Amma fa a nan Najeriya, sun kirkiro shi ne kurum domin wasu daga ciki su kare muradunsu da cin ma bukatun da ke gabansu da kuma samun damar karya lagwan abokan takara daga jam’iyyun hamayya. Don haka a takaice zan iya cewa shirin ba yi da amfani ga jam’ar kasa har sai an tsaya an maida hankali a kan abin da zai kawo ci gaban kasa ta hanyar gaskiya da adalci.”

Muhawarar na da fa’ida – Salisu Umar

Muhammad Yaba, a Kaduna

Salisu Umar: “Akwai fa’ida a muhawarar, domin yana da kyau a ce jama’a sun san ’yan takararsu da kuma shiri ko manufofinsu idan an zabe su. Shi ya sa nake ganin dole ne jama’a su fahinci abin da dan takarar kowace kujera zai yi masu idan an zabe shi, tun kafin a zabe shi. Rashin yin hakan ne ke sanyawa ake zaben tumun dare. Saboda haka a ra’ayina, akwai fa’ida sosai ga ’yan takara su tattauna a tsakaninsu, domin fada wa jama’a manufofinsu.”

Akwai amfani ga muhawarar
– Aliyu Sulaiman

Muhammad Yaba, a Kaduna

Malam Aliyu Sulaiman: “Lallai akwai amfani ga muhawarar, domin tana bai wa jama’a damar sanin dan takarar da za su zaba domin ya shugabance su. Tana bai wa ’yan takara damar sanar wa da jama’a kudurorinsu kuma hakan na taimaka wa jama’a damar sanin shugabanni masu adalci saboda haka tana da amfani.”

Muhawarar na da muhimmanci – Liman Zanuwa

John Wada, a Lafiya

Barista Liman Zanuwa: “Ni dai a ganina, wannan mahawara tsakanin ’yan takarar shugabancin kasa da mataimakansu tana da mahimmanci sosai. Domin wata dama ce da suke yin amfani da ita wajen idar ko kuma sanar da al’ummar kasar nan manufofi da ayyukan da za su yi musu idan suka samu nasara. Ka ga haka ma zai taimaka wa talaka don ta haka ne zai iya tantance tsakanin wadannan shirye-shiryen shugabannin don ya zabi wadanda za su inganta rayuwarsa gobe. Saboda haka ni dai a guna hakan yana da mahimmanci sosai.”

Muhawarar ba ta da wani amfani – Hannatu Agyas

John Wada, a Lafiya

Misis Hannatu Agyas: “A nawa ra’ayin dai, wannan mahawara da ake shirya wa ’yan takarar kujerun siyasa wato Shugabannin kasa da mataimakansu ba ta da wani mahimmanci. Don ai hukumar zabe ta ba su damar gudanar da kanfen inda suke bayyana wa al’umma manufofi da shirye-shiryensu idan aka zabe su. Kuma ba cacar baki ne al’ummar kasar nan ke bukata a yanzu ba. Shugaba ya zo ya gudanar da ayyukan ci gaba ga al’ummar kasan nan a fili shi ne ake so. Saboda haka a takaice dai a ganina ba ta dace ba, don ba ta da muhimmanci ko kadan.”