Muhimman abubuwa 10 da Gwamnan Kano ya aiwatar a kwana 10 na mulkinsa

Wadanne abubuwa Abba ya aiwatar a kwana 10 a Kano

Muhimman abubuwa 10 da Gwamnan Kano ya aiwatar a kwana 10 na mulkinsa

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023, Abba Kabir Yusuf ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon Gwamnan Jihar Kano.

Abba, na jam’iyyar NNPP, ya karbi mulkin ne daga tsohon Gwamna, Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC.

Jim kadan bayan rantsar da shi, sabon Gwamnan ya yi dogon jawabi kan muhimman ayyuka da kudurorin da gwamnatinsa za ta sa gaba, a cikin shekaru hudu masu zuwa, inda a nan take ya fara aiwatar da wasu.

Aminiya ta yi nazari tare da zakulo muku muhimman abubuwa guda 10 da Gwamnan ya sami aiwatarwa a daidai lokacin da yake cika kwana 10 a kan kujerar mulki.

Nada manyan mukarraban gwamnati

A ranar da aka rantsar da Abba ya sanar da nada wasu mukamai da suka hada da Sakataren Gwamnati, Sakataren Yada Labaran Gwamna, Mai Kula Baki da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati.

Kai ziyara wasu muhimman wurare

Ko kafin ya shiga gidan gwamnati bayan kammala rantsar da shi, sai da Gwamnan ya wuce makarantar kula da gyaran hali da ke garin Kiru. Daga bisani kuma ya ziyarci asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da madatsar ruwa ta Challawa da sauransu.

Ayyana dokar ta-baci a kan samar da ruwan sha

A makon da aka rantsar da shi, sabon Gwamnan ya kai ziyarar gani da ido madatsar ruwa ta Challawa, inda a can ya sanar da ayyana dokar ta-baci a bangaren samar da ruwan sha a Jihar.

Rushe gine-ginen da aka yi ‘ba bisa ka’ida ba

Daga tsakain daren ranar Juma’a zuwa na Lahadi, Gwamna Abba ya jagoranci rushe gine-ginen da ya ce an yi su ba bisa ka’ida ba a Filin Sukuwa da Sansanin Alhazai na Kano da Otal din Daula da kuma Babban Filin Idi na Kano.

Soke sayar da asibitin Asiya Bayero

Gwamnan ya kuma ce ya soke zargin sayar da Asibitin Yara na Asiya Bayero da ke Kano ga wani dan siyasa, kodayake daga bisani gwamnatin da ta gabata ta musanta sayar da wajen ga wani.

Sauke dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar

Abba ya kuma sanar da sauke dukkan masu rike da mukaman siyasa da ke jihar, tare da umartarsu da su mika ragamar gudanarwarsu ga Manyan Sakatarorinsu nan take.

Rushe shugabancin Hukumar Alhazai tare da nada sabo

Har ila yau, Gwamnan ya rushe shugabancin Hukumar Jindadin Alhazai ta Jihar, tare da nada sabo, wanda kuma aka mika wa ragama nan take, domin su ci gaba da shirye-shiryen Aikin Hajjin Bana.

Kafa kwamitin yaki da kwacen waya

Gwamnan ya kuma sanar da kafa wani kwamitin kar-ta-kwana da zai yi yaki da matsalar kwacen waya, wanda ya kunshi jami’an tsaro da kotuna taf-da-gidanka.

Sauke Jami’an Alhazai na Kananan Hukumomi 44

Ba wai iya shugabancin Hukumar Alhazai ta Kano kawai Abba ya rushe ba, hatta Jami’an Alhazai na Kananan Hukumomi 44 da ke Jihar sai da Abba ya sallame su daga bakin aiki.

Ba da umarnin kama masu ‘dibar ganima’

Abba ya kuma ba Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano umarnin kama duk wanda aka samu da laifin dibar kayayyaki a wuraren da aka yi rusau da sunan ganima.

2025: ’Yan Najeriya suke bibiyar abin da shugabanni ke yi – Atiku

Abba ya sanya hannu kan kasafin kuɗin N719bn na 2025

Mutum 5 da aka fi ambato a 2024 a Afirka

Gwamnatin Borno ta horar da mata 162 sana’o’in dogaro da kai

Tags