Muhimman abubuwa 13 a hukuncin Kotun Ƙoli kan ’yancin ƙananan hukumomi

Gwamnan jiha ba ya da ikon naɗa shugabannin riƙo a ƙananan hukumomi.

Muhimman abubuwa 13 a hukuncin Kotun Ƙoli kan ’yancin ƙananan hukumomi

Kotun Kolin Najeriya (Hoto: Onyekachukwi Obi)

A ranar 11 ga Yulin 2024 Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin hana ƙananan gwamnonin jihohi katsalandan ko danne kuɗaɗen ƙananan hukumomin ƙasar nan.

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da hukuncin ya ƙunsa.

Sashi na 116 na Tsarin Mulki ya ce kuɗaɗen ƙananan hukumomi a miƙa su ga fallen na uku na gwamnati, don haka bai bayar da kafar asusun haɗa-ka a tsakanin jihohi da ƙananan hukumomi ba.

Tsarin Mulki bai amince wa jihohi su karɓa kuma su raba kuɗi a madadin ƙananan hukumomin ba.

Kotun ta yanke hukuncin cewa Asusun Tarayya ya miƙa kason ƙananan hukumomi kai-tsaye gare su, tunda jihohin sun ci gaba da karɓa da yin amfani da kuɗaɗen.

Sashe na 162 (5) ya hana biyan kuɗin ƙananan hukumomin ta hannun jihohi, don haka daga ranar a riƙa tura wa ƙananan hukumomin kuɗinsu kai-tsaye.

Gwamnatoci a matakan ƙananan hukumomi: Sashe na 77 ya wajabta wa jihohi su tabbatar da samuwar ƙananan hukumomi.

Gwamnatin dimokuraɗiyya da aka zaɓa ba ta kasancewa shifcin gizo ko ’yar amshin shatan gwamnatin. Wajibi ne a tabbatar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin dimokuraɗiyya a matakinƙaramar hukuma.

Kada gwamnoni su riƙa rusa shugabannin ƙananan hukumomi da zaɓaɓɓun kansiloli.

Gwamnan jiha ba ya da ikon naɗa shugabannin riƙo a ƙananan hukumomi.

Gwamnoni da majalisun dokoki na jihohi ba su da ikon yin amfani da dokokin jihohi da majalisun dokokin jihohi suka kafa wajen rusa zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi su naɗa shugabannin riƙo.

Bayar da odar bin wannan hukunci nan take.

Duk wani aiki saɓanin abubuwan da aka ambata a sama haramtacce ne kuma ya saɓa wa Tsarin Mulkin Nijeriya.

Majalisun dokoki na jihohi ba su da ikon kafa kowace doka don rushe zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan.

Hukuncin Kotun Ƙolin wajibi ne dukkan hukumomin gwamnati da ke sassan ƙasar nan su tabbatar ana aiki da shi.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan