Muhimman abubuwa 37 da suka faru a shekarun Najeriya 100

A kokarin da ake yi na gudanar da bikin cika shekara 100 da kafuwar Najeriya, Aminiya ta zakulo wadansu muhimman abubuwa da suka faru a cikin shekara 100 da samuwar Najeriya. Kamar haka: 1.    Hada yankuna biyuSa Frederick Lugard shi ne ya taso daga kasar Hong Kong  ya koma Legas domin aiwatar da tunanin ofishin […]

Muhimman abubuwa 37 da suka faru a shekarun Najeriya 100

A kokarin da ake yi na gudanar da bikin cika shekara 100 da kafuwar Najeriya, Aminiya ta zakulo wadansu muhimman abubuwa da suka faru a cikin shekara 100 da samuwar Najeriya. Kamar haka:

1.    Hada yankuna biyu
Sa Frederick Lugard shi ne ya taso daga kasar Hong Kong  ya koma Legas domin aiwatar da tunanin ofishin mulkin mallaka da ke Landan, inda ya yi amfanin da alkalaminsa ya hada yankunan arewaci da kudanci da kuma Legas suka zama kasa daya mai suna Najeriya a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1914.

2.Kudi da amfanin gona masu samar da kudi
Manoma a fadin Najeriya sun dade suna noma abincin da za su ci, amma da Turawan mulkin mallaka suka zo sai suka karfafa wa manoma gwiwar noma amfanin gona da za su rika samar da kudi domin fitar da shi zuwa masana’antun kasashen Turai. Gyada da koko da manja da taba da auduga sune suka fi daraja a lokacin. Turawan Ingila kuma sun fito da amfani da kudi domin jin dadin gudanar da harkar.

3.    Fari da yunwa
An yi fama da manyan bala’o’in yunwa a Najeriya lokacin mulkin mallaka, wadanda suka faru a shekarun 1914 da 1927 da 1942 da 1951. Hakan ya faru ne a sakamakon fari da aka yi da kuma watsi da noman abinci aka mayar da hankali wajen noma amfanin gona mai samar da kudi kawai. Mafi munin yunwar da aka yi ita ce ‘’Yunwar Muda’’ da ta mamaye yankin arewa a tsakanin shekarar 1913 zuwa 1915.

4.    Kafuwar majalisa a 1922
An kaddamar da majalisa ta farko a Najeriya a shekarar 1922 domin masu yunkurin kwato wa kasa ‘yanci su samu kafar isar da matsalolinsu ga shugabannin mulkin mallaka.

5.     Yakin duniya na biyu
Da farko ba mu san dalilin da ya sanya Turawa suke yakar junansu ba, sai a tsakanin shekarar 1940 zuwa 1945 lokacin da aka kwashi dubban matasan Najeriya da karfin tsiya aka sanya su a soja aka kwashe su a jirgin ruwa zuwa Bama domin su dakatar da kasar Japan daga shiga Indiya.

6.    Taron tsarin mulki a Landan
An gudanar da tarurruka a kan tsarin mulki har sau uku a Landan a shekarun 1954 da 1957 a shirye-shiryen da ake yi na samar wa Najerya ‘yancin kai. Sa Ahmadu Bello shi ne ya jagoranci wakilan yankin Arewa, DaktaNnamdi Azikiwe kuma ya jagoranci wakilan gabashi, shi kuma Cif Obafemi Awolawo ya jagoranci na yammacin kasar nan zuwa wurin taron.

7.    Gano mai
Bayan an dade ana neman mai tun  daga shekarar 1938, kamfanin Shell sai ya gano mai a yankin Neja delta, inda mai ya fara bubbugowa a rijiya ta farko a shekarar 1956 a Oloibiri da ke jihar Ribas a halin yanzu. Asusun kasar nan ya kasura tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu.

8.     Kwamitin Willink
Taron Landan na shekarar 1957 ya amince a kafa wani kwamiti a karkashin jagorancin tsohon shugaban jami’ar Cambridge Harry Willink domin ya yi nazarin tsoron da tsirarun kabilu suke yi a yayin da Najeriya ta kama hanyar samun ‘yancin kanta, inda ya gabatar da cikakken rahoton da ya tayar da kura a karo na farko.

9.Samun ‘yanci a shekarar 1960
Da tsakar dare ranar 1 ga watan Oktobar shekarar 1960 Gimbiya Aledanda tana ji, tana gani aka sauke tutar Ingila, wanda ke nuna cewa mulkin mallaka ya kawo karshe a Najeriya, inda shi kuma Firayiminista Sa Abubakar Tafawa balewa zura ya ido yana kallon yadda ake daga tutar Najeriya sama domin ta maye gurbin ta Ingila.

10.     Tsarin mulkin Jamhuriya
Shugabannin janhoriya a karo na farko sun amince a shekarar 1962  dan Najeriya ya maye gurbin Sarauniyar Ingila a matsayin shugaban Najeriya, inda shugaban jam’yyar NCNC Dokta Nnamdi Azikiwe da Sarauniya ta nada shi a matsayin Gwamna Janar a shekarar 1960,  ya zama shugaban kasa mara iko na farko a ranar 1 ga watan Oktobar 1963.

11.Hukuncin cin amanar kasa, 1962-1963
An kama shugaban jam’iyyar  Action Group kuma jagoran ‘yan adawa Cif Obafemi Awolawo tare da wadansu ‘ya’yan jam’iyyar guda 28 ana tuhumarsa da laifin yunkurin kifar da gwamnatin Tafawa balewa a shekarar 1963. Inda aka daure su, amma Gowon ya sake su a watan Agustan shekarar 1966.

12.     Dokar Ta-baci
Rikici ya barke a tsakanin bangarori biyu na jam’iyyar AG a majalisar yankin yammaci a watan Mayun shekarar 1962, inda magoya bayan Cif Obafemi Awolawo da Firimiya Cif Samuel Akintola suka yi ta kisan junansu. Hakan ya sanya gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-baci a yankin.

13. Juyin mulki na farko, Janairu 1966
Jamhuriya ta farko ta kawo karshe da karfin tsiya a shekarar 1966 lokacin da Manjo Chukwuma Nzeogwu ya jagoranci wadansu sojoji suka yi awon-gaba da Farayiminista Tafawa balewa da ministan kudi Festus Okotie-Eboh da Firimiya Ahmadu Bello da Ladoke Akintola da wadansu manyan hafsoshin soja irin su Birgediya Zakari Maimalari da Kanar Kur Muhammad da Kanar bictor Yakubu Pam da Laftanar Kanar Abogo Largema, suka kashe su.

14.Dokar mayar da Najeriya malukiya, May 1966
Manjo janar Johnson Thomas Umunnakwe Aguyi-Ironsi, wanda ya kwace iko daga hannun masu juyin mulki ya zama shugaban kasa kuma babban kwamandan rundunar sojojin kasar nan, ya fito da wata dokar soja a watan Mayun 1966 da ta rushe yankunan Najeriya ta mayar da Najeriya malukiya mai gwamnati a tsakiya.

15.     Rikicin  A raba, 1966-67
Dokar soja da ta rushe yankuna da Ironsi ya kafa ta haifar da rikicin kabilanci. Rikici ya fara barkewa ne a kasuwar Jos, nan da nan ya watsu a sauran yankunan Arewa, inda masu zanga-zanga ke kiran ‘’A raba’’ kasar kowa ya kama gabansa.

16.Juyin mulki na biyu, Yuli 1966
Al’’amarin sai ya koma cin tuwon kishiya ramuko. Domin a ranar 29 ga watan Yuli 1966  jami’an soja daga yankin Arewa suka kaddamar da wani juyin mulkin, inda suka kifar da gwamnatin Ironsi, suka kashe Janar Ironsi da Gwamnan mulkin soja na jihar yamma Kanar Adekunle Fajuyi da kuma wadansu hafsoshin soja da dama.

17.Taron Aburi, Janairun 1967
Gagarumin taron da aka gudanar a kan Najeriya an yi shi ne a wajen kasar,inda a farkon shekarar 1967 shugaban kasar Ghana ya karbi bakuncin majalisar koli ta mulkin soja da ta rabe biyu, aka gudanar da taro a Aburi ta kasar Ghana domin a magance matsalolin bangarorin biyu. Bayan sun dawo Najeriya kuma sai suka ci gaba da rikici dangane da shawarar da suka amince da ita a Aburi.

Cigaba a shafi na 5

Cigaba daga shafi na 4

18. kirkiro jihohi, watan Mayu 1967
Domin share wa kananan kabilu hawayensu, Janar Gowon sai ya raba yankunan Najeriya guda hudu zuwa jihohi 12 a ranar 27 ga watan Mayun 1967, wanda hakan ya taka wa gwamnan mulkin soja na yankin gabashi Kanar Ojukwu birki game da burinsa.

19.     ballewar Ynkin Biafara
A ranar 30 ga watan Mayun 1967 Ojukwu ya ayyana ballewar yankin gabashin kasar nan tare  da kafa kasar Biyafara mai hedkwata a Enugu. Tun da farko sai da taron dattawan yankin gabashin ya amince da yunkurin.

20.     Yakin basasa, 1967-1972
Saboda kafa kasar Biyafara da aka yi ya sanya Gowon ya  bayar da umarnin a nuna ba-sani, ba-sabo a yankin, wanda hakan ya haifar da yakin basasa da aka rasa miliyoyin rayukan jama’a. An kawo karshen yakin a shekarar 1970 lokacin da Ojukwu ya tsallake ya bar kasar. Sojojin Biyafara sun mika wuya, shi kuma Gowon ya ayyana cewa, babu wanda ya samu nasara kuma babu wanda aka ci galabansa.

21.Mayar da tuki hannun dama,Afirilu 1972
Ranar 2 ga Afirilu 1972 da karfe 6 na safe ne  ababen hawa a Najeriya suka bar tuki a bangaren  hagu suka koma amfani da bangaren dama, wanda ya sanya aka kwashe shekaru motoci masu sitiyari a dama suke dauke da alamar da ke nuna cewa sitiyarinsu a dama yake.

22.     Naira da Kobo, 1973
Tun zamanin mulkin mallaka muna amfani da kudin fam ne da sule da kwabo mai huji, amma a ranar 1 ga Janairu 1973 kwamishinan kudi na tarayya Alhaji Shehu Shagari da Gwamnan babban bankin Najeriya Dokta Clement Isong suka fito da sabon kudi Naira da kobo. Wanda sule yake da kobo goma maimakon tsohon sule mai kwabo 12.

23.     Garabasar Odoji, 1974
Wani kwamiti a karkashin jagorancin Cif Jerome Odoji ya zauna na tsawon shekara biyu ya bayar da shawarar a nininika wa ma’aikata albashinsu, saboda dimbin kudin da ake samu daga man fetur, Gowon ba amince da shawarar kawai ya yi ba, har ma cewa ya yi a biya ma’aikata kudin baya na shekara biyu. Hakan ya sanya farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabo a tarihin Najeriya.

24.     Kifar da gwamnatin Gowon, Yuli 1975
An kifar da gwamnatin Gowon a ranar 29 ga Yuli 1975 lokacin yana halartar taron kungiyar hada kan Afirka a Kampala kasar Uganda, bayan ya kwashe shekara 9 yana mulki.

25. Kashe Murtala Muhammad, Fabrairu 1976
A ranar 13 ga Fabrairun 1976 ne aka ji muryar  Darektan horar da sojoji motsa jiki Kanar Bukar Suka Dimka a rediyo yana sanar da canjin gwamnati, yunkurin juyin mulkin bai yi nasara ba, amma Dimka ya kashe shugaban kasa Janar Murtala Muhammad.  A sakamakon haka aka zartar da hukuncin kisa a kan jami’an soja 43 da farar hula guda daya saboda laifin yunkurin juyin mulki.

26.Sauyin kananan hukumomi, 1976
A hankali sarakunan gargajiya suna ta rasa ikon da suke da shi a tsarin gudanar da gwamnatin N.A da suka samu tun zamanin mulkin Turawa. An fara rage musu iko ne a shekarar 1960, lokacin da aka dauke kotuna da ‘yan sanda da kuma gidajen yari daga karkashinsu. A shekarar 1976 kuma aka kwace musu iko gaba daya, inda aka maye gurbin gwamnatin N.A da zababbun shugabannin kananan hukumomi.

27.    Komawa mulkin farar hula, 1979
Tun ranar da Yarima Aledanda ya tsaya yana kallo aka sauke tutar Ingila a watan Oktoba 1960, wani abu mai kama da wannan bai sake faruwa a Najeriya ba sai a ranar 1 ga Oktobar 1979 lokacin da babban mai shari’a na kasa Atanda Fatai Williams ya rantsar da Alhaji Shehu Shagari a matsayin shugaba mai cikakken iko na farko, inda shi kuma shugaban mulkin soja Janar Olusrgun Obasanjo ya ja da baya ya sara masa, wanda hakan ya nuna cewa mulki ya tashi daga hannun soja ya koma hannun farar hula.

28.     Rikicin Maitatsine, 1980
An kwashe makonni biyu ana ba-ta-kashi tsakanin ‘yan sandan kwantar da tarzoma da almajiran Muhammadu Marwa Maitatsine a unguwar ‘Yan awaki da ke cikin birnin Kano. Da al’amarin ya yi kamari sai aka tora sojoji wadanda suka ragargaza unguwar, suka kashe Maitatsine tare da fatattakar dubban almajiransa.

29.Faduwar Jamhuriya ta Biyu,1983
Kafin wannan lokacin Birgediya Sani Abacha ba fitacce ba ne, amma sanarwar da ya yi a rediyo na kifar da gwamnatin janhoriya ta biyu ta sanya ya yi fice. A lokacin an kama dubban ‘yan siyasa an tsare, tare da daure da dama daga cikinsu saboda da laifin rashawa, wadansu ma har daurin shekara 300 aka yanke musu.

30. Shirin tayar da komadar tattalin arziki (SAP), 1986
Wannan kusan za a iya cewa shi ne shirin gyarar tattalin arziki mafi bakin jini a tarihin kasar nan, domin shirin tsuke bakin aljihu da Shagari ya fito da shi a 1981 bai yi zafin wannan shirin da gwamnatin Babangida ta fito da shi a shekarar 1986 ba. Mutanen Najeriya da dama suna ganin an yi haka ne domin a biya wa Asusu lamuni na duniya (IMF) bukata.

30.     Kasuwar shunku, 1986
Kasuwar shunku tana daya daga cikin jigogin tsarin shirin tayar da komadar tattalin arziki na SAP, inda aka bar Naira ta samar wa kanta daraja, wanda ya sanya darajar Naira ta sulmuyo daga kobo 70 dala daya a shekarar 1986, zuwa  Naira 176 dala daya a halin yanzun.

31.    ballewa, 1990
A ranar 22 ga Afirilun 1990 Manjo Gideon Orkar ya fito da wani sabon shafi a tarihin Najeriya inda ya ware wadansu jihohi ya ce ya kore su daga Najeriya, a yayin wani yunkurin juyin mulki da ya yi.  A karshe dai an zartar masa da hukuncin kisa.

32.     Zaben 12 ga Yuni
An yi ta shakkun shirin mika mulki ga farar hula da Janar Babangida yake tsarawa saboda kwan-gaba, kwan-bayan da shirin ke cike da shi. Al’amarin ya kawo karshe a ranar 23 ga Yuni lokacin da gwamnati ta bayar da sanarwar soke zaben shugaban kasa da aka gudanar kwanaki 11 da suka gabata, wanda Cif Moshood Abiola da ya kama hanyar lashewa ya tayar da kayar baya tare da magoya bayansa. Hakan ya sanya ‘’ranar 12 ga Yuni’’ ta zama muhimmiya.

33. Rasuwar Abacha da Abiola, Yuni 1998
Masu lura da yadda al’amura ke gudana na ganin Allah ne Ya karbi addu’ar da al’ummar kasa suka yi domin ya samar musu da mafita, inda aka wayi gari shugaban kasa Janar Sani Abacha,wanda tsarin Tazarce ya bullo a zamaninsa, ya fadi ya mutu a ranar 8 ga Yunin 1998. Bayan wata guda kuma babban fursunan da ya daure Cif Abiola shi ma ya rasu, wanda ya sanya Janar Abdulsalami ya zama shugaban kasa kuma ya kafa kwamitin mika mulki ga farar hula.

34.Komawa mulkin farar hula, 1999
Hannun bayarwa, hannun karba. Lokacin da soja suka mika mulki a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1999, wanda ya mika a madadin soja shekara 30 da suka gabata ne, watau Janar (wanda yanzu ya zama) Cif Olusegun Obasanjo ya sake karba.

35.     Rasuwar ‘Yar’aduwa guda biyu
Fitattun ‘Yar’aduwa guda biyu sun rasa rayukansu shekaru 13 a tsakani. Janar Shehu Musa ‘Yar’aduwa shi ne jigo a siyasa lokacin da Abacha ya daure shi a gidan yari, inda ya rasu a watan Disambar 1997. Bayan shekara 10, kanensa Umaru Musa ‘Yar’aduwa ya kai ga zama   shugaban kasa, amma ciwo ya galabaita shi ya rasu a shekarar 2010.

36.      Boko Haram
Bayan yakin basasa ‘yan fashi da makami ne suka rika cin karensu babu babbaka, amma da ‘yan Boko Haram suka bayyana sai al’amarin ‘yan fashi ya zama wasan yara. Bayan an murkushe yunkurinsu a karo na farko a shekarar 2009, sai ‘yan Boko Haram suka sake fitowa da karfi suka girgiza Najeriya ta hanyar tayar da kayar bayan da ba a taba ganin irinsa ba. Dubban rayuka ne suka salwanta.