Muhimman abubuwa 6 da ke cikin hudubar Arafa ta bana 

Al’ummar Musulmi fiye da miliyan guda na gudanar da aikin hajji a kasa mai tsarki.

Muhimman abubuwa 6 da ke cikin hudubar Arafa ta bana 

Mahajjata a kan dutsen Arafah

Al’ummar Musulmi fiye da miliyan guda ne ke gudanar da aikin hajji a kasa mai tsarki, inda a Juma’ar nan su ka yi hawan Arafa wanda ke matsayin jigo a aikin hajji kuma wajibi ga dukkan musulmi.

Limamin da ya jagoranci sallah a filin Arafa na bana, Sheikh Dakta Muhammad Al-Iissah, ya yi tsokaci akan muhimman batutuwa da suka shafi rayuwar Musulmai a hudubar da ya gabatar.

Bayan yi wa Allah godiya da kirari da kuma jan hankali kan sanya tsoron Allah a dukkanin ibadun da bawa zai aikata ya kuma taba batutuwa kamar haka:

1. Jan hankali a kan ibadar Hajji da Umarah da irin ladan da ke ciki.

2. Tabbatar da zaman lafiya tsakanin musulmai da ma’abota wasu addinan da ba musulunci ba.

3. Hadin kan musulmai a duk inda suke ba tare da rarrabuwar kai ba.

4. Kyautatawa musulmai da ma wadanda ba musulmai ba.

5. Rige-rigen aikata ayyukan alkhairi a kodayaushe.

6. Kyawawan dabi’u da kyautata mu’amala a tsakanin juna a kodayaushe.