Muhimman abubuwa a fagen kwallon kafa a 2022
Abubuwa da dama da suka shafi kwallon kafa sun wakana a 2022.
Duba da cewa wannan shekara muna yin bankwana da ita, Aminiya ta yi waiwaye don kawo wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a harkar kwallon kafa a duniya.
A karon farko a 2022 aka buga Gasar Cin Kofin Duniya a yankin Larabawa, wanda kasar Qatar ta karbi bakunci; an fara a ranar 20 ga watan Nuwamba, aka kammala ranar 20 ga Disamba.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kan Ranar Kyauta A Addinin Kirista
- Pele da iyalansa sun yi bikin kirismeti a asibitin da ya ke jinya
Kasar Ajantina ce ta lashe gasar, wanda shi ne karon farko da babban dan wasanta, Lionel Messi ya lashe Kofin Duniya.
Qatar ta kashe wa gasar kudade mafiya yawa a tarihi, inda ta kashe sama da Dala biliyan 220, ninki 16 na abin da aka kashe wa wanda aka yi kafin shi a Rasha, kuma ninki biyar na abin da aka kashe wa gasannin da aka yi shekara 30 da suka gabata.
Kasar ta kayata dagasar, inda ta gayyaci taurarin mawaka da jaruman fina-finai da sauran fitattun mutane daga sassan duniya don kara wa gasar armashi.
Qatar, ta yi amfani da zayyanar ayoyin Alkur’ani mai girma da Hadisan Manzon Allah (SAW) a kan manyan alluna, filayen wasanni, otel-otel da sauran wuraren da mutane za su ziyarta don yi musu karin haske kan abubuwan da suka shafi addinin Musulunci da rayuwar Musulmi.
Sai dai Qatar ta kafa mummunan tarihi a gasar, inda ta zama kasa ta farko da ta taba rashin nasara a wasan farko a hannu Ecuador da ci biyu da babu a matsayin mai masaukin baki, tun bayan fara gasar shekara 92 da suka gabata.
Gasar Kofin Duniya da aka kammala a Qatar shi ne wanda aka fi zura kwallaye a raga a tarihin gasar da kwallo 172 daga wasa 64 da aka buga.
Abubuwan Da Qatar Ta Amfana Da Su
Akalla mutum sama da miliyan daya ne suka ziyarci Qatar don kallon gasar da kuma yin yawon bude ido.
Hakan ya ta damar samun kudin shiga da bunkasa tattalin arzikinta.
Qatar ta karbi Dala biliyan 17 daga Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, a matsayin wani tagomashi na karbar bakuncin gasar da aka kammala.
An yi kiyasin kudaden da Qatar ta samu daga otal-otal, filayen wasanni, gidajen mai, manyan kantunan zamani da sauran wuraren yawon bude ido sun haura Dala biliyan 300.
Daga cikin alfanun da kasar ta samu shi ne, a sanadin gasar an gina sabbin tituna, filayen wasanni, otal-otal da kuma kara kawata kasar.
Har wa yau an gano sabbin abubuwan more rayuwa da kasar ta samar a dalilin gasar za a jima ana cin gajiyarsu ta hanyar bunkasa tattalin arzikinta.
Gasar Zakarun Turai
Idan muka yi waiwaye a Gasar Zakarun Turai da aka kammala a wannan shekara, ita ma za a ce ta zo da wani sabon ta’ajibi.
Real Madrid ce ta lashe gasar, inda ta kafa tarihin lashe gasar karo na 14.
Real Madrid ta doke Liverpool da ci daya mai ban haushi, ta hannun dan wasanta Vinicius wanda ya sake kai su ga sarautar Zakarun Turai.
Sai dai kafin samun wannan nasara, Real Madrid ta sha gumurzu, inda ta doke zaratan kungiyoyi irin su PSG daga Faransa, Chelsea daga Ingila, Manchester City daga Ingila sannan ta doke Liverpool a wasan karshe.
Gwarzon Ballon D’Or
A wannan shekara ne dai dan wasan Faransa da Real Madrid, Karim Benzema ya lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Duniya, wato Ballon D’Or, inda ya doke abokan hamayyarsa irin su Mane da Lewandowski wanda suka zo a matsayin na biyu da na uku.
Kofin Nahiyar Afirka
A wannan shekara da muke bankwana da ita ne aka yi Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka, wadda kasar Kamaru ta karbi bakunci.
Senegal dai ce ta lashe gasar inda ta doke Masar a bugun fanareti a wasan karshe.
Vincent Aboubakar na Kamaru ne dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a raga da kwallo takwas a gasar, yayin da Mohamed Salah ya zamo dan wasan da ya fi kowa daraja a gasar.
Gwarzon Dan Kwallon Afrika
A wannan shekara ne dai dan wasan gaban Senegal da Bayern Munich, Sadio Mane ya lashe kambun Gwarzon Dan Kwallon Kafar Afirka, inda ya doke Edouard Mendy na Kamaru da Chelsea da kuma Mohamed Salah na Masar da Liverpool.
Kasashen Da Suka Samu Gurbin Zuwa Gasar Kofin Duniya A Qatar
Kasashen Afrika biyar suka samu gurbin zuwa Gasar Kofin Duniya da aka kammala a Qatar.
Kasashen su ne Kamaru, Tunisiya, Maroko, Senegal da kuma Ghana.
Sai dai manyan kasashen Afrika da suka yi fice a harkar kwallon kafa kamar Najeriya, Aljeriya, Kwaddibuwa da sauransu sun rasa gurbin zuwa gasar bayan gaza hada makin da ake bukata.
Sai dai a gasar kasar Maroko ta daga darajar Afirka, inda ta je matakin kusa da na karshe a gasar, wanda babu wata kasa a Afrika da ta taba zuwa wannan mataki a tarihin gasar.
Maroko dai ta yi bajintar doke kasashe irin su Belgium, Croatia Sifaniya da kuma Portugal a gasar.
Maroko ta karkare gasar a mataki na hudu.
Gasar Firimiyar Najeriya
A wannan shekara da muke bankwana da ita ne, kungiyar kwallon kafa ta Ribas United a ranar 25 ga watan Yuni, ta kafa tarihin lashe Gasar Firimiyar Najeriya a karon farko.
Sai dai kuma jiga-jigan kungiyoyi irin su Katsina United, Heartland FC, Kano Pillars da kuma kungiyar MFM FC dukkaninsu suka fada ajin gajiyayyu.
Cinikayyar ’Yan Wasa A Nahiyar Turai
Idan kuwa muka yi waiwaye kan cinikayyar ’yan wasan kwallo kafa da aka fi kashe, Aminiya ta tabo biyar daga cikin wasu manyan ‘yan wasa da aka yi baje kolinsu a 2022.
Manchester United ta dauki Anthony daga Ajax a kan £82m; Chelsea ta dauki Wesley Fofana daga Leicester City kan £70m; Ita kuwa Real Madrid ta dauki Aurelien Tchouameni kan £68.3m daga Monaco.
Liverpool ta dauki Darwin Nunez kan £64m daga Benfica; Manchester United ta sake daukar Casemiro daga Real Madrid kan £60m.
Wannan shi ne kadan daga cikin waiwaye da Aminiya ta yi kan wasu muhimman abubuwa da suka faru a harkar kwallon kafar duniya a 2022.
Rasuwar Pele
Sarkin Kwallon kafa na duniya, Pele ya kwanta dama bayan shekara 82 a duniya a ranar Alhamis, 29 ga watan Disamban 2022 sakamakon jinya.
Rasuwar Pele ta girgiza duniyar kwallon kafa, ganin cewa shi ne dan wasa tilo da ya lashe Kofin Duniya sau uku, a tare da kasarsa, Brazil.
Ronaldo ya koma Al Nassr
Babban dan wasan kasar Portugal, Christiano ya koma kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr da ke birnin Riyadh na kasar Saudiyya bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara bakwai.
A ranar Juma’ar karshen 2022, dan wasan ya sanya hannu a yarjejeniyar buka wasa na shekara biyu da rabi sannan ya zama jakadan kwallon kafa a kungiyar Al Nassr.
Ronaldo ya koma Al-Nassr ne bayan a watan Nuwamba ya raba gari da kungiyarsa ta Manchester United da ke kasar Birtaniyya.