Manyan abubuwa 5 kan sabon tsarin NYSC

Sabon tsarin NYSC ya soke yin faretin karshe, ya canja tufafin masu yi wa kasa hidima, tare karbe shugabanci daga sojoji zuwa hannun farar hula

Manyan abubuwa 5 kan sabon tsarin NYSC

A ranar Litinin Gwamnatin Tarayya ta sanar da sabbin sauye-sauye a Shirin yi wa Kasa Hidima (NYSC).

Ministan Ci-gaban Matasa, Ayodele Olawande, ya bayyana matakin a matsayin garambawul na gaba ɗaya da NYSC ya samu tun bayan kafa shirin shekara 53 da suka gabata.

Bayan kammala taron Majalisar Zartarsa ta Kasa (FEC), ne ministan tare daHadimar Shugban Kasa kan Tsare-tsare, Hadiza Bala Usman suka bayyana sauye-sauye.

Ga muhimman sauye-sauyen da ya kamata ku sani kan sabon tsarin NYSC, wanda aka assasa shi a zaman mulkin soja na Janar Yakubu Gowon shekaru 53 da suka wuce:

 

Sabon yanayin tufafi

Sabon tsarin na NYSC ya bullo da sabon tsarin  tufafin masu yi wa kasa hidimia maimakon na yanzu da ake amfani da shi tun shekara 1973 da aka kafa shirin.

 

Soke faretin POP

Haka kuma, an soke bikin faretin yaye matasa masu yin NYSC, inda aka maye gurbinsa da wani sabon biki. Haka kuma za a inganta yanayin cibiyoyin horon matasan da wani sabon tsari da ya tanadi tantancewa ta tabbatar da ingancinsu a fadin Najeriya.

 

Karbe shugabanci daga hannun sojoji

A karkashin sabon tsarin, shugabancin hukumar NYSC zai tashi daga hannun sojoji ya koma hannun fararen hula. Amma sojoji za su ci gaba da bayar da horo ga matasan NYSC da ke rukunin rundunar aikin tsaro.

 

Nazarin wurin da za a tura matasan

Sauye-sauyen sun hada da sabunta tsarin matasan zuwa inda za su yi aki, la’akari sosai da matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan.

 

Tsawaita zama a sansanin NYSC

Za a tsawaita lokacin zaman da matasan a sansanin samun horo zuwa makonni shida, maimakon mako uku da ake yi a halin yanzu.

An raba makonni shidan zuwa gida uku, inda a makonni biyu na farko za a koya musu dabarun jagoranci, sanin ya kamata da kuma kisan kasa da kishin kas

Makonni biyu na tsakiya kuma an ware su domin koyon sana’a, dabarun tsarin kasuwanci da samun jari da kuma ajiyar kudi. “An ware rana ta mumman domin masu yin NYSC su tattauna da al’umma kan sana’o’i.

Ragowar makonni biyun kuma za a yi amfani da su wurin bayar da horo na musamma da ya kebanci rukunin aikin da suka zaba wa kansu da kuma abin da suka karanta a makaranta, da kuma sana’o’i.

Rukunin sana’o’i 11

Sabon tsarin ya samar da fannonin (rundunonin) sana’o’i 11 da kowane matashi zai zabi daya daga ciki domin samun kwarewa a kansa kamar haka:

  1. Kula da lafiya
  2. Ilimi
  3. Kimiyya da fasahar zamani
  4. Noma da kiwo
  5. Shari’a
  6. Aikin Al’umma
  7. Ababen more rayuwa
  8. Muhalli
  9. Sana’o’i
  10. Nishadi
  11. Tsaro

Dun rukunin da mai yin NYSC ya zaba, za a ayyana shi a matsayin dan rundunar — kamar rundunar likitanci — kuma zai samu horo na musamman a bangaren, a cikin makonni biyu na karshe zamansa a sansanin NYSC.