Muhimman abubuwa kan Matatar Man Dangote
Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya gina matatar a kan kudi Dala biliyan 19 (Naira triliyan 8.7) cikin shekara
A shekarar 2017 aka fara aikin gina Matatar Man Dangote, wadda ita ce mafi girma a Nahiyar Afirka.
A ranar 22 ga Mayu 2023, mako guda kafin saukar Shugaba Muhammadu daga mulki, ya kaddamar da matatar, wadda babban attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya gina a kan kudi Dala biliyan 19 (Naira triliyan 8.7).
- Dokta Abdul-aziz Idris Dutsen Tanshi ya isa gida
- Barayi 2 da suka sace wayoyin hannu 48 sun shiga hannu a Katsina
Ga abubuwan 12 da ya kamata ku sani game da matatar a takaice:
- Tana da karfin samar da tataccen mai ganga 650,000 a kullum.
- Ita ce irinta (mai samar da ganga 650,000 a wuri guda) mafi girma a duniya.
- Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ke da kashi 20% na hannun jarin matatar.
- Tattaccen man da za ta samar zai iya biyan bukatar Najeriya gaba daya.
- Za ta rika fitar da tataccen mai zuwa kasashen Afirka 12.
- Za ta samar da kashi 36% na tataccen man da ake bukata a Afirka.
- An gina ta a yankin Ibeju-Lekki, kuma fadinta ya kai hekta 2,635.
- Ana hasashen za ta samar da Dala biliyan 21 — Naira tiriliyan 9.7 — a shekara
- Tana da tankuna guda 177, wadandan za su ci jimillar lita biliyan 4.742.
- An horas da injiniyoyi 900 a kasashen waje kan aikin matatar mai.
- Za ta iya danyen mai wasu kasashen Afirka da Gabas ta Tsakiya da Amurka.
- Ta cika ka’idojin Bankin Duniya da Tarayyar Turai da hukumar DPR na takaita fitar da gurbataciyar iska.