Muhimman abubuwan da suka faru a Kannywood a 2014

Shekarar 2014 shekara ce da muhimman abubuwa suka faru a masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood. Abubuwan da suka faru sun hada na farin ciki da bakin ciki. Mutuwa ta ziyarci masana’antar, ’yan fim sun yi aure, wadansu sun hayayyafa, an kuma gudanar da bukukuwa daban. Aminiya za ta yi muku tariyar muhimman abubuwan […]

Muhimman abubuwan da suka faru a Kannywood a 2014
Muhimman abubuwan da suka faru a Kannywood a 2014

Shekarar 2014 shekara ce da muhimman abubuwa suka faru a masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood. Abubuwan da suka faru sun hada na farin ciki da bakin ciki. Mutuwa ta ziyarci masana’antar, ’yan fim sun yi aure, wadansu sun hayayyafa, an kuma gudanar da bukukuwa daban. Aminiya za ta yi muku tariyar muhimman abubuwan da suka faru a Kannywood a shekarar 2014

Rasuwar ’yan wasa
A lokacin da mutuwa ta ziyarci Kannywood ta da daukar fitaccen jarumin fina-finan barkwanci Shehu Golobo ne, inda ya rasu a ranar Alhamis 30 ga Janairu, 2014 a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato. Daga nan mutuwar ta dauke Musa Jalingo a ranar Alhamis 15 ga Mayu, 2014 a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Faruk Nagudu mai kamfani Nagudu Inbestment ya mutu a ranar Asabar 14 ga Yuni, 2014 shi ma a Asibitin Malam Aminu Kano bayan ya yi fama da rashin lafiya. Mahaifin Aminu Hudu Almah ya rasu a ranar Laraba 27 ga Agusta a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, Jihar Filato. A watan Nuwamba ne Abubakar Buwa wanda ake yi wa lakabin Darakta, wanda ke harkokin wasan kwaikwayo a Jabi daki-Biyu da ke Abuja ya rasu a Kano bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya. A ranar Laraba 10 ga Disamba, 2014 ne Allah Ya yi wa fitaccen jarumin barkwancin nan Rabilu Musa wanda aka fi sani da Ibro rasuwa. Marigayi ya rasu ne a Asibitin Annur da ke Gyadi-Gyadi cikin Jihar Kano bayan fama da jinya. Mahaifin Samira Saje ya rasu a ranar Lahadi 12 ga Oktoba, 2014 a gidansa da ke Unguwar Place Way da ke karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba.
Bikin ranar Haihuwa
Fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa ya shirya bikin zagayowar ranar haihuwarsa a ranar Talata 25 ga Maris, 2014, inda aka gudanar da bikin a gidansa da ke unguwar Badawa a cikin Kano. Mawaki Sa’eed Naguda ya yi bikin cika shekara 30 a ranar Laraba 16 ga Afrilu, 2014 a gidan kanen mahaifinsa da ke Lamba 18-19 a Titin Fanshekara a Kano. Sani Danja ya yi bikin cikarsa shekara 40 a ranar Lahadi 20 ga Afrilu, 2014 a wurin cin abinci mai suna Albasha Restaurant da ke Maitama a Abuja. Fati Muhammad ta yi bikin cika shekara 28 a ranar 21 ga Yuni, 2014. Samira Saje ta yi bikin cika shekara 20 a ranar 9 ga Agusta, 2014 a otal din Al-Ahad da ke Yakubu Abenue daura da Titin Alkali a Kaduna.
Haihuwa
A ranar Laraba 11 ga Yuni, 2014 Sadik Sani Sadik ya samu magaji, inda aka rada wa jaririn suna Shehu a wani masallaci da ke Jos. A ranar Alhamis 12 ga Yuni, 2014 matar mawaki Adamu Hassan Nagudu ta haifi santalelen jariri, inda aka rada masa suna Ahmad.  A ranar 25 ga Mayu jaruma Yahanazu Sani ta samu jika, inda ’yarta Hindatu ta haifi jariri, aka sa masa suna Muhammad. A ranar Talata 17 ga Yuni, 2014 Hamisu Lamido Iyantama ya samu jiki, inda ’yarsa mai suna Hadiza ta haifi jariri aka sa masa suna Mahmud. A ranar 18 ga Oktoba fitaccen Jarumi Zaharaddeen Sani ya samu karuwar sambaleliyar jaririya, inda aka haife ta a asibitin Garkuwa da ke Kaduna, a rana ta bakwai aka rada mata suna Muneera.
Aure
A ranar Asabar 23 ga Oktoba, 2014 furodusa Umar Aliyu Maijalingo ya auri Bara’atu a gidan iyayenta da ke Lamba 7 unguwar S/Maiduna a Kaduna a kan sadaki Naira dubu 100. A ranar Asabar 9 ga Agusta aka daura auren darakta Rabi’u Ibrahim (HRB) da amaryarsa Amina a Kontogora, Jihar Neja a kan sadaki Naira dubu 40.  A ranar 16 ga Agusta marubuci Yakubu M. Kumo ya kara mata ta biyu. An daura auren marubucin ne da Nana Khadija a Tudun Wada bayan Gidan Yari a Gombe a kan sadaki dubu 30.
Neman Ilimi
A ranar 27 ga Agusta, 2014 ’yan fim 19 suka tafi Indiya kwas a kan dabarun shirya fim. Daga cikin ’yan fim din akwai Ali Nuhu da Hamisu Iyantama da Ishak Sidi Ishak da Falalu dorayi da Mustapha Musty da Hauwa Maina da sauransu. Sun yi kwas din ne a wata makaranta mai suna Asian School of Media Suites Studies da ke New Delhi.
Mutuwar Aure
A watan Okotoba, 2014 ne auren tsohuwar shahararriyar jarumar fina-finan Hausa Rukayya Umar Santa wadda aka fi sani da ‘Rukayya Dawayya’ ya mutu. Idan ba a manta ba a ranar 6 ga watan Yuli, 2012 aka daura aurenta da dan kasuwa mazaunin Abuja mai suna Alhaji Muhammad Teku.
daukaka
A watan Afrilu, 2014 ne fitaccen jarumin fina-finan Hausa Adam A. Zango ya zama jakadan Kamfanin sadarwa na MTN na tsawon shekara daya. Abin da jarumin zai rika yi sun hada da  halartar galar kamfanin (show), wanda za a yi sau 10 a shekara; zai rika yi masa tallace-tallace, sannan idan ana gudanar da wata gasa kamar kwallon kafa ko Polo za a gayyaci jakadun MTN su rika tallata masa hajarsa.
 Jaje
A ranar Juma’a 21 ga watan Nuwamba masu ruwa da tsaki a masana’antar fina-finan Hausa da suka hada da jarumai da ’yan kasuwa da daraktoci da furodusoshi suka ziyarci sansanin ’yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, wadanda aka tsugunnar a ofishin Hisba na Kano, inda suka tallafa musu da kayayyakin jinkai. Alhaji Isma’il NaAbba Afakallah ne ya jagoranci ’yan fim din don kai gudunmuwarsu ga wadanda rikicin Boko Haram din ya shafa.
Jita-jita
A ranar Juma’a 14 ga watan Maris, 2014 aka baza jita-jitar cewa fitaccen jarumin fina-finan Hausa Ali Nuhu ya mutu, bayan wadansu ’yan bindiga sun harbe shi. Jarumin ya karyata jita-jitar, inda ya ce yana nan da ransa cikin koshin lafiya. A lokacin da ake yada jita-jitar yana Gwarinpa da ke Abuja lokacin daukar fim din Kamfanin Saira Mobies mai suna ‘Ya Daga Allah’.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa