Muhimman abubuwan da suka faru a manyan gasannin Turai
Wasan Manchester United da Liverpool na Yammacin Litinin din nan shi ne zai fi daukar hankali.
Kamar dai yadda wasannin mako na farko da na biyu suka kayatar, haka su ma wasannin mako na uku na manyan gasannin Turai ba a barsu a baya ba.
Wasan da zai fi daukar hankali shi ne wanda za a kece raini tsakanin Manchester United da Liverpool a Yammacin Litinin din nan.
- Gwamnatin Borno za ta fara gine-gine a tsohon sansanin Boko Haram
- Kotu ta daure Faston da ya yi wa mata 3 ’yan gida daya fyade
Firimiyar Ingila
Tuni dai Firimiyar Ingila ta soma daukar zafi, inda duk manyan kungiyoyi a gasar sun zubar da maki in banda Arsenal wacca ta hada maki 9 cikin wasanninta uku.
Arsenal dai ta yi zaman dirshan a saman teburin Firimiyar Ingila bayan ta kai ziyara filin wasa na Vitality a ranar Asabar kuma ta zuba wa Bournemoouth kwallaye uku da nema.
Ita kuwa Manchester City da ke biye mata a matsayi na biyu, da kyar ta samu maki daya bayan ta tashi wasa canjaras uku da uku da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United a ranar Lahadi.
Crystal Palace ta samu nasara a kan Aston Villa da ci uku da daya, yayin da Chelsea ta kwashi kashinta a hannu bayan ta je bakunta filin wasa na Allan Road kuma Leeds United ta zuba mata kwallaye uku da nema.
Da kyar Tottenham Hotspur ta hada maki uku yayin da ta karbi bakuncin Wolverhampton a wasan da aka tashi da ci daya mai ban haushi.
Bundesliga
A gasar Bundesliga ta Jamus kuwa, wasan da aka fi ruwan kwallaye a karshen mako na ukun shi ne, wasa tsakanin Bayern Munich da Bochum.
Bayern Munich wadda ta je bakunta Vonovia Ruhrstadion, babu sani babu sabo ta yi wa Bochum da kwallaye 7 da nema.
Sabon dan wasan Bayern din kuma tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Sadio Mane na daga cikin wadanda suka zura kwallaye a ragar Bochum, inda dan kasar Senegal din ya zura wa masu masaukinsu kwallaye biyu cikin bakwai din da suka zura a raga.
Tun da fari dai a wasan da aka fafata a ranar Juma’ar da ta gabata, Borusssia Mönchengladbach ta samu nasara a kan Herthe Berlin da ci daya mai ban haushi kana Mainz ma ta bi Augsburg har gida a ranar Asabar tare da lallasa ta da ci biyu da daya.
Freiburg ma har gida ta bi Stuttgart ta kuma ba ta kashi da ci daya mai ban haushi.
Haka abin ya ke a wasa tsakanin Hoffenheim da ta bi Levekusen har gida ta kuma lallasa ta da ci uku da nema.
An tashi wasa canjaras tsakanin Wolfsburg da Shalke, yayin da aka tashi kunne doki daya da daya tsakanin Eintracht Frankfurt da Cologne.
Sai wasan da aka yi baya ba zani a ranar Asabar din karshen mako tsakanin Borussia Dortmund da Werder Bremen, inda Bremen din ta bi Dortmund har filin Signal Iduna Park ta kuma lallasa ta da ci uku da biyu.
Tun da fari dai Dortmund din ce ta fara zira kwallaye biyu a ragar Bremen, kafin ana daf da tashi wato mintoci 89 da fara taka leda, Bremen din ta yi wa Dortmund baya ba zani inda ta zira kwallaye uku cikin mintuna biyar kacal.
La Liga
Kwallaye biyu sabon dan wasan Barcelona, Robert Lewandowski ya jefa a wasan mako na biyu na La Ligar bana da suka je bakunta gidan Real Sociedad, inda kungiyar ta Cataloniya ta zuba kwallaye hudu da daya a Reale Arena.
Ita kuwa Villarreal casa Atletico Madrid ta yi da ci 2-0 a wasan da ta je bakunta, inda Yeremi Pino da Gerard Moreno suka samu sa’ar mai masaukinsu a minti na 73 da kuma mintin karshe na wasan.
Ita ma Real Madrid casa Celta Vigo ta yi a wasan mako na biyu na La Ligar da suka fafata ranar Asabar a filin wasa na Abanca-Balaidos.
Ruwan kwallaye biyar aka yi a wasan da Jesus Gil ya yi alkalancinsa wanda aka tashi 4-1 a gaban ’yan kallo 15,681.
Serie A
A ranar Asabar, uku babu ko daya Inter Milan ta ci Spezia a wasan mako na biyu na gasar Serie A ta Italiya wadda a yanzu ta hada maki shida.
Napoli wadda ke zaman ta daya a gasar da maki shida ita ma, kwallaye hudu ta zuba a ragar Monza wadda ta je mata bakunta filin wasa na Diego Armando Maradona.
Canjaras na 1-1 aka tashi tsakanin AC Milan da Atalanta ranar Lahadi a filin wasa na Gewiss wanda ’yan kallo suka halarta.