Muhimman abubuwa daga mukabalar Abduljabbar da Malaman Kano
Malaman dai sun bukaci Malam Abduljabbar ya tuba.
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
Karshen tika-tika tik, inji Hausawa. A karshe dai an yi mukabala tsakanin Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara da Malaman Kano.
An shafe kimanin sa’o’i biyar ana tattaunawa kan maganganun da ake zargin malamin da yi, wadanda masu korafi suka yi zargin cin zarafi ne ga Sahabban Annabi (S.A.W).
- Mukabala: Yau za a yi ta ta kare tsakanin Sheik Abduljabbar da malaman Kano
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 40 a kauyukan Zamfara
Zaman dai ya gudana ne a karkashin jagorancin Alkalin Mukabala, Shugaban jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila, Farfesa Salisu Shehu a Hukumar Zakka ta Jihar Kano ranar Asabar.

‘Abduljabbar ya gaza’
Bayan kammala mukabalar dai, alkalinta, Farfesa Salisu Shehu ya ce Malam AbdulJabbar yayi gaza amsa dukkan tambayoyin da tuhumce-tuhumcen da ake yi masa.
A maimakon haka ya zargi malamin da bigewa wajen sauya akalarsu ba tare da ya amsa ainihin abubuwan da ake magana a kai ba.
‘Da na sani ban zo da litattafai 500 ba’
Sai dai Malam AbdulJabbar ya yi korafin cewa minti 10 da aka bashi domin ya kare kansa ya yi kadan saboda yawan litattafan da ya zo da su kimanin 500.
“Da na sani ba zan zo da littattafai har 500 ba,” inji shi.
‘A shirya sabuwar mukabala’
Malam Abduljabbar ya bukaci gwamnatin Jihar da ta sake samar da wani lokaci daban domin sake wata mukabalar.
Hakan, a cewarsa shine zai bashi isasshen lokacin da zai fito da matsalar yadda take.
Daga nan kuma ya roki idan za a sake yi a nuna mukabalar kai tsaye duniya na gani.
‘Abduljabbar, ka tuba’
Malaman da suka halarci mukabalar dai sun bukaci Malam AbdulJabar ya tuba ya nemi gafara, amma ya ce sam ba zai yi ba.
Daya daga cikinsu, Malam Abubakar Madatai ya yi kira ga Malam Abduljabbar ya tuba kuma ya nemi gafarar al’ummar Musulmi su yafe masa bisa taba mutuncin Annabi (S.A.W) da yayi.
Sai dai a martaninsa, Malam Abduljabbar ya ce ba zai tuba a wajen wannan mukabala ba saboda ba a bi hanyar da zai tuba ba.
Ya ce tilas sai an kawo masa hujjojin da suka fi nasa kafin ya amince cewa a kan kuskure ya ke.