Muhimman ayyukan ci gaba da gwamnatina ta yi a watanni 14 — Tinubu

Na shirya fuskantar kowane irin ƙalubale muddin zai samar da kyakkyawar makoma.

Muhimman ayyukan ci gaba da gwamnatina ta yi a watanni 14 — Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa akwai matakan da ya ɗauka domin ci gaban ƙasar duk da sanin cewa zai fuskanci ƙalubale.

A jawabin da ya yi wa ’yan kasa kai tsaye a safiyar wannan Lahadin, Tinubu ya ce “ina mai tabbatar muku cewa na shirya fuskantar kowane irin ƙalubale muddin zai samar da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar Nijeriya.

“A cikin watanni 14 da suka gabata, gwamnatinmu ta samu gagarumin ci gaba wajen sake gina ginshikin tattalin arzikinmu domin ciyar da mu gaba cikin wadata mai ɗorewa.

“Sai dai na tsinci kaina a yanayin da ba ni da zaɓin da ya wuce na ya ɗauki matakin da ya dace duk da raɗaɗinsa, don haka na cire tallafin man fetur da kuma kawar da tsarin musayar kuɗaɗen waje da yawa waɗanda suka haifar da tsaiko da cikas ga tsarin tattalin arzikin ƙasarmu da ci gabanta da namu.

“Haka kuma matakan sun toshe tallafin da muka bai wa ƙasashen da ke maƙwabtaka da mu na a-sai-da-rai-a-nemo-suna, da tuni kafin mu farga sun mayar da tattalin arzikinmu kashin-baya.

“Mun fitar da sama da Naira biliyan 570 ga jihohi 36 domin faɗaɗa shirye-shiryensu na tallafa wa rayuwar al’ummomin jihohinsu, yayin da ƙananan ‘yan kasuwa 600,000 suka ci gajiyar tallafinmu, ana sa ran ƙarin ƙananan ‘yan kasuwa 400,000 su ma za su amfana.

“Gwamnatinmu ta bai wa matasa kulawa ta hanyar kafa tsarin rance ga ɗalibai mai suna NELFUND.

“Yanzu haka an fitar da kuɗi da ya kai Naira biliyan 45.6 ga ɗalibai da cibiyoyinsu daban-daban, kuma ina kira tare da ƙarfafa gwiwa ga ƙwararrun matasanmu da su yi amfani da damarsu wajen cin gajiyar shirin.

“A bangaren ƙididdigar kasafin kuɗi, jimillar kuɗaɗen shiga na gwamnati ya ruɓanya fiye da ninki biyu, inda ya kai sama da Naira tiriliyan 9.1 a rubu’in farkon shekarar 2024 idan aka kwatanta da rubu’in farko na shekarar 2023, sakamakon ƙoƙarin da muke yi na daƙile duk wasu hanyoyi da kuɗaɗe ke zirarewa ta barauniyar hanya.

“Waɗannan matakai da na ɗauka sun toshe duk wata ribar da ’yan fasa-ƙwauri da masu yi wa ƙasarmu zagon-ƙasa suke samu.

“A baya kasarmu tana kashe kashi 97% na duk kuɗaɗen shigar da muke samu wajen biyan bashi; a yanzu mun sami damar rage hakan zuwa kashi 68% a cikin watanni 13 da suka gabata.

“Wannan ya ba mu damar samun ƙarin kuɗin da muke kashe wa ƙasar da ’yan ƙasarmu, don samar da muhimman ababen zamantakewa kamar ilimi da kiwon lafiya. Haka kuma ya sa jihohinmu da ƙananan hukumomin ƙasarmu suka samu kaso mafi tsoka da ba a taba samu ba a tarihi daga Asusun Gwamnatin Tarayya.

“Mun kuma dirfafi ƙaddamar da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa a faɗin ƙasar nan.

“Muna ci gaba da aiki tuƙuru domin ƙarasa ayyukan da muka gada na tsohuwar gwamnati waɗanda suna da muhimmancin gaske ga ci gaban tattalin arzikinmu, da suka haɗa da hanyoyi, gadoji, layin dogo, wutar lantarki, da haɓakar mai da iskar gas.

“Musamman ayyukan babbar hanyar Legas zuwa Calabar da babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry wadda za ta haɗa jihohi 16 da samar da dubban ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki ta hanyar kasuwanci, yawon bude ido da al’adu.

“Nan ba a jima a makon da ya gabata na sanya hannu kan dokar albashi mafi ƙaranci, inda abin da ma’aikaci zai samu duk wata ba zai gaza Naira dubu 70 ba.

“Muna ci gaba da bai wa manoma tallafi domin bunƙasa samuwar abinci a farashi mai sauƙi.

“Na kuma ba da umarnin cire harajin shigo da wasu kayayyakin abinci kamar shinkafa, masara, alkama, dawa da kuma magunguna har nan da tsawon watanni shida masu zuwa domin ganin farashin waɗannan kayyaki ya sauko.

“Har yanzu ina ci gaba da tattaunawa da gwamnoni da wasu ministoci domin bunƙasa hanyoyin samar da abinci a ƙasar.

“Mun raba takin zamani wanda manufarmu ita ce mu noma fiye da kadada miliyan 10 domin samar da abincin da za mu ci.

“A ’yan watanni kaɗan da suka gabata mun ba da umarnin sayo kayayyakin noman zamani na biliyoyin naira daga ƙasashen Amurka da Belarus da Brazil, kuma ina mai tabbatar muku cewa waɗannan kayayyakin sun nan tafe a kan hanya.”