Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

Babu wani abu mafi tasiri wajen bayar da dama mai zurfi da kuma haɗari ga tattalin arzikinmu da tsaronmu, al’ummarmu ga ɗan Adam kamar ƙirƙirarriyar fasaha.

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

Shugaban Amurka mai barin gado, Joe Biden ya yi wa al’ummar ƙasar jawabinsa na bankwana bayan shafe shekaru huɗu na tsawon wa’adi ɗaya a karagar mulki.

Yayin da ya rage ‘yan kwanaki ya bar fadar White House, Biden a jawabinsa na ban kwana na yammacin jiya Laraba ya fitar da wani gargaɗi game da abin da ke tafe a nan gaba sannan ya buƙaci a gudanar da muhimman sauye-sauye a kundin da aka assasa ƙasar a kai.

Sai dai sabanin jawabansa na baya, Biden bai mayar da hankali wajen lissafo jerin abubuwan da ya yi ba a kujerar mulki.

A cikin jawabin na tsawon mintuna 19, Biden ya bayyana fargaba dangane da tsarin siyasa da aka san ƙasar a kai da ke neman gushewa.

Shugaban ya yi amfani da damar wajen yin gargaɗi ga al’ummar kasar, kamar yadda Dwight Eisenhower ya yi a 1961 sa’ilin da ya bayyana damuwa game da “kamfanonin ƙera makamai” a jawabinsa na ban kwana.

Biden ya bayyana cewa “salon mulkin ‘yan tsiraru na ƙara kankama a Amurka” kasancewar an tattara iko da kuɗaɗe a hannun wasu mutane kalilan.

Ya kuma caccaki “kamfanonin fasaha” da dandalin sada zumunta, inda ya ce ana cakuɗa gaskiya da ƙarya domin samun mulki da riba.”

Ya buƙaci ƙasar ta ci gaba da yaƙar matsalar sauyin yanayi, yana cewa, “kada mu bari a yi mana barazana mu sadaukar da makomarmu.”

Biden ya yi amfani da jawabin wajen sanar da shawarar da yake da matuƙar buri a kai.

Ya buƙaci a yi wa kundin tsarin mulkin Amurka kwaskwarima “domin fayyace cewa babu wani shugaban kasa da ke da kariya daga laifuffukan da ya aikata yayin da ya ke kan karagar mulki.”

Biden ya yi matuƙar alfahari da jerin nasarorin da ya samu, sai dai ya ce har yanzu bai samu isasshen yabo a kan hakan ba.

“Za a ɗauki lokaci kafin ganin cikakken tasirin abin da muka yi tare. Amma duk kyawawan ababen da muka shuka za su yi tsiro da fure nan da shekaru da dama masu zuwa.”

Biden ya yi gargadi game da “muhimmanci da hatsarin da ke tattare da ƙirƙirarriyar fasaha wato AI (Artificial Intelligence).

“Kirkirarriyar Fasaha ita ce mafi tasirin fasaha a wannan zamani da duk wasu zamunna da suka gabata.

“Babu wani abu mafi tasiri wajen bayar da dama mai zurfi da kuma haɗari ga tattalin arzikinmu da tsaronmu, al’ummarmu ga ɗan Adam kamar ƙirƙirarriyar fasaha.

“Ƙirƙirarriyar fasaha za ta taimaka mana matuƙa amma ya wajaba mu mayar da hankali kan tasirinta domin tana barazana ga kowanne fanni na rayuwarmu,” in ji Biden.

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi