Muhimman darussa daga jawabin Malala

Abin kunya ne da takaici, yadda aka halaka dalibai 40 da malaman makaranta biyu a kauyen Mamudo na Jihar Yobe (kamar kuma yadda munanan aika-aikar da ke faruwa a sauran sassan duniya, yadda ake halaka malamai da yara da malaman asibiti). Haka kuma ga abin takaicin da muke zama muna kallo yana faruwa a kullum, […]

Muhimman darussa daga jawabin Malala
Muhimman darussa daga jawabin Malala

Abin kunya ne da takaici, yadda aka halaka dalibai 40 da malaman makaranta biyu a kauyen Mamudo na Jihar Yobe (kamar kuma yadda munanan aika-aikar da ke faruwa a sauran sassan duniya, yadda ake halaka malamai da yara da malaman asibiti). Haka kuma ga abin takaicin da muke zama muna kallo yana faruwa a kullum, na rahotannin bama-baman da ke tashi da harbe-harben da ake yi wa masallata a masallatai lokacin da suke ibada ko kuma a lokacin da suke buda-baki. Wannan abin takaici duk yana faruwa a sassa daban-daban na Gabas Ta Tsakiya, kuma har da aka fara azumin Ramadan, abin bai tsaya ba. Wadannan kashe-kashe da ta’annati, wadansu karkatattu ne ke aiwatar da su da sunan addini da sunan “aikin Allah” suke aiwatarwa. Na kuduri aniyar rubuta wani abu ne dangane da haka da zai karfafa mana zuciya, sai hankalina ya dauku ga wani jawabi da wata ’yar shekara 16 ta yi wa daukacin al’ummar duniya.
Wannan yarinya kuwa ita ce Malala Yousafzai, ’yar Pakistan, wacce wani dan Taliban ya harbe ta a ka, a lokacin da take kan hanyar tafiya makaranta. Duk da harbin nata, Allah Madaukakin Sarki Ya kadarta sai ta rayu kuma godiya ta tabbata ga Allah. A halin da ake ciki, yarinyar ta zama wata fitilar haskaka duniya, musamman ga mata da yara. Ta zama muryar kwato wa mata da yara ’yanci, cewa suna da hakkin a ilimantar da su. Ta gabatar da wannan jawabi ne a gaban Majalisar Matasan Duniya, a bikin zagayowar haihuwarta, inda ta cika shekara 16 a duniya. A tunanina, kawo muku kyakkyawan jawabin Malala a nan, babbar gudunmowa ce da zan ba ku, a matsayina na marubucin shafin nan. Yarinyar nan mai karsashi, tana gaya mana cewa, lokaci ya yi da za a daina maida hannun agogo baya, ta yadda ake son cusa mutane cikin duhun jahilliyar baya. Wannan misali nata, lallai abin koyi ne ga al’umma gaba daya. A yanzu ga jawabin nata, wanda ya jawo mata yabo da tafi daga wakilan da suka fito daga dukkan sassan duniya. (Ina taya ki murnar bikin cikarki shekara 16, Malala).
Jawabin Malala ga duniya:
Da sunan Allah, mai rahama, mai jinkai. Assalamu alaikum.
Ni ban ma san ta inda zan faro wannan jawabin nawa ba. Da farko, ina godiya ga Allah, wanda a wurinSa muke abu daya. Haka kuma ina godiya ga mutanen da suka yi ta taya ni addu’a domin ganin na warke cikin lokaci kuma na fara sabuwar rayuwa.
Na samu dubban katin karfafa gwiwa da taya alhini daga dukkan sassan duniya. Ina godiya gare ku duka. Ina godiya ga daukacin yaran duniya, wadanda kyawawan lafuzzansu suka karfafa mani gwiwa. Zan kuma so in mika godiya ga jami’an asibiti da likitoci da sauran ma’aikatan asibitin da suka kula da ni a Pakistan da Ingila da Hadaddar Daular Larabawa da gwamnatocinsu.
Ya ku ’yan uwana maza da mata, ina son ku tuna da wani abu daya: Ranar Malala, ba ranata ce ni kadai ba, rana ce ta kowace mace a duniya da kowace yarinya da kowane yaro, wadanda suka daga muryarsu, suna neman ’yancin kansu.
’Yan ta’adda sun karkashe dubban mutane, sun kassara miliyoyin mutane. Ina daya daga cikin irin wadannan mutane da aka raunata. A yau ga ni a tsaye, ga ni tsaye, ga ni ’yar yarinya daya tal a cikin dubbai. Ina magana ba don ni kadai ba, sai domin wadanda ba su da muryar magana su saurara. Ina magana ne domin nema wa al’umma damar su rayu cikin lumana, domin su samu damar zama cikin ’yanci da mutunci. Ina magana domin al’umma su kasance cikin damar rayuwa kamar kowa ba tare da bambanci ba, domin su samu damar samun ilimi.
Ya ku ’yan uwana ku sani, a ranar 9 ga Oktoba, 2012, wani sojan Taliban ya harbe ni a gefen hagu na goshina, sun harbi kawayena ma. Sun yi tsammanin za su rufe bakunanmu da karfin harsashi amma sun gaza. Bayan faruwar haka, sai ga muryoyi da dama sun bayyana. ’Yan ta’addar sun tsammaci za su iya kashe mani himma da kaimi, za su iya hana ni cin ma burina. Sai dai ba kamar yadda suka so ba, babu abin da ya canja daga rayuwata; illa kawai wasu sababbin al’amura da suka bijiro mani, da suka kara mani karsashi. Wadannan kuwa su ne cewa, na samu rashin tsoro, na samu himma da karfin zuciyar tunkarar al’amura.
Har yanzu dai ni ce Malala kuma burace-buracena suna nan ba su canza ba. Ya ku ’yan uwana maza da mata, ba na adawa da kowa kuma ba na zo nan don in yi magana kan sukar wani ko yin ramuwar gayya ga wani ko ’yan Taliban ko wasu kungiyoyin ta’adda ba. Na zo ne nan in yi magana da nufin nema wa yara ’yancin neman ilimi. Ina son in ga kowane yaro da yarinyar ’yan Taliban da sauran ’yan kungiyoyin ta’addanci sun samu damar neman ilimi. Hasali ma, ni ba na nuna kiyayya ga dan Taliban din nan da ya harbe ni. Koda a ce yanzu zai zo ya tsaya a gabana kuma a ce ina rike da bindiga, ba zan harbe shi ba. Wannan tausayi da jinkai da yafiya da ke zuciyata, na koye su ne daga Annabi Muhammadu (SAW), manzon rahama. Na gaji wannan halayya ce ta son kawo canji daga koyarwar da Martin Luther King ya bar mana. Kamar yadda Nelson Mandela da Muhammad Ali Jinnah suka koya mana.
Za mu kammala

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos