Muhimman Darussa Daga Littafin Umar A Birnin kudus

Sunan Littafi: Umar A Birnin kudus.Sunan Marubuci: Najib Kelani (Fassarar Hamisu Gumel).Kamfanin Wallafa (dab’i): Dee-nee Multi Trade Co.Shekarar Wallafa: 2014.Yawan Shafi: Babi 24, Shafuka 378.Farashi: Ba a fada ba. A tarihin mulki a duniya, an san irin yadda Musulunci ya kafa mulkin adalci da gaskiya. Izzar Musulunci ta mamaye fadin duniya, yadda ta ci galaba […]

Muhimman Darussa Daga Littafin Umar A Birnin kudus
Muhimman Darussa Daga Littafin Umar A Birnin kudus

Sunan Littafi: Umar A Birnin kudus.
Sunan Marubuci: Najib Kelani (Fassarar Hamisu Gumel).
Kamfanin Wallafa (dab’i): Dee-nee Multi Trade Co.
Shekarar Wallafa: 2014.
Yawan Shafi: Babi 24, Shafuka 378.
Farashi: Ba a fada ba.

A tarihin mulki a duniya, an san irin yadda Musulunci ya kafa mulkin adalci da gaskiya. Izzar Musulunci ta mamaye fadin duniya, yadda ta ci galaba a manyan daulolin duniya, kamar Rum da Fasha da sauransu. Tarihi ya taskance mulkin adalci da ya gudana a zamanin mulkin Sahabin Annabi Muhammadu (SAW), Umar dan Khaddabi, kamar kuma yadda shi kansa ya zama wani babban jigo, jarumi, adali a tarihin Musulunci.
Wannan tarihi, shi ya darsu a zuciyar shahararren marubuci, dan kasar Masar, Najib Kelani, inda tunaninsa da fikirarsa suka fada kan rayuwar Umar dan Khaddab, ya dauki alkalami ya kirkira ingantaccen labari, yana hasashe da tunanin cewa Umar ya dawo duniya, ya sauka a Birnin kudus. Abubuwan da suka wakana a tunanin nasa, su ne suka kasance kunshiyar wannan littafi da muke nazari a yau.
Labarin, duk da cewa kirkirarre ne, amma yana dauke da labarin duniyar nan tamu a yanzu da abubuwan da ke faruwa a yau da kuma wasu da suka faru a jiya. Yana ba mu labarin Musulunci da yadda al’ummar Musulmi suke a jiya da yadda suke a yau da kuma yadda ya kamata su kasance a kowane zamani. Ya ba mu labarin yadda al’ummar Falasdinawa ke rayuwar kunci da ukuba, bisa mulkin zaluncin Yahudawa ’yan kaka-gida. Dawowar Umar a birnin kudus, ya haskaka mana hanya, na abubuwan da Musulmin zamanin yanzu ya kamata su yi domin su samu nasara kwatankwacin yadda Musulmin zamanin Umar (RA) suka samu.
Kamar yadda mafassarin littafin nan, Hamisu Gumel ya bayyana a shafi na 378, ya ce:
“Mai karatu, wannan littafi kirkirarren labari ne daga alkalamin kwararre kuma gogaggen marubucin nan dan kasar Masar, wato Najib Kelani. Kelani marubuci ne da ya shahara a fagen rubutn zube da sauran nau’ukan rubutun littafi, wanda kuma tasiri da nason kalmomin da alkalaminsa ya zana ya game duniya baki daya. Wannan littafi yana daya daga cikin fitattun littaffansa. Ya rubuta shi ne cikin harshen Larabci da sunan ‘Umar Yazharu Fi al-kuds’ wanda kuma aka fassara da Turanci a matsayin ‘Omar Appears in Jerusalen’ inda ni kuma na fassaro shi daga harshen Turancin zuwa Hausa da taken ‘Umar A Birnin kudus.’ Ina da yakinin cewa wannan littafi zai yi matukar kayatarwa ga duk wanda ya karanta shi tare da sanya tunani da kuma kyakkyawan fata a kan al’amarin kudus da yankin Falasdinu baki daya.”
Shi kuwa marubucin littafin, Najib Al-Kelani, ga abin da yake cewa game da aikin nasa, a shafi na 2:
“Mai karatu, na san watakila wannan littafi ya zama abin al’ajabi da rikitarwa ta fuskar adabi da ilimi da kuma akida saboda nau’in jigo da salon da aka rubuta shi. To, amma bakin hadarin da ya lullube sararin samaniyar wannan kasa da tsananin bala’i da wahala da suke yin barazana ga hadafi da makomarta da kuma irin rudanin da ya mamaye zukatan mutanenta; gaba daya wadannan su suka haddasa faruwar abubuwa daban-daban, wanda kuma hakan ya afkar da tunani da ra’ayoyi iri-iri, inda wasu ra’ayoyin na karya ne da rudanin batan basira, yayin da wasu kuma suke sahihai, ingantattu da ke kan turba. A cikin wannan yanayi, akwai al’amuran hankali da na son zuciya, sannan kuma akwai al’amura masu rikitarwa, wadanda ke yin dawurwura cikin kwakwalenmu, suke azabtar da zukatanmu dare da rana. Don haka ne ya zama ba makawa ga marubuta, ma’abota alkaluman ’yanci, wadanda rayuwarsu take tsundum cikin wannan lamari, su yunkura cikin shauki da jimami, su bayyana dukkan lamarin a sigar fasaha da manufa. Bugu da kari, wannan littafi yana da matukar tasiri saboda yanayin fasahar da ke cikinsa, sannan kuma littafin zai kasance shimfida ta sabon salon adabi.”
Hakika, wadannan bayanai na marubuci da kuma mai fassarar littafin nan sun tabbata gaskiya, domin kuwa bayan na kammala karanta littafin, na fahimta da fiye ma da abin da suka tsakura a nan. Dalili ke nan a yanzu zan tsakuro wasu daga cikin muhimman darussan da ke kimshe a littafin.
Darasi na farko da aka dabbaka a littafin shi ne, tabbatar da cewa lallai Allah (SWA) ne mahaliccin komai da kowa. Mu dubi abin da Umar ya fada a shafi na 17, da yake cewa: “Mutum yakan sarrafa karfe ne amma ba shi ne ke kirkirarsa ba. Akwai matukar bambanci tsakanin wanda ya kirkiro abu a lokacin da babu shi da kuma wanda cikin sauki ya sarrafa abin nan zuwa ga wata siga, ta yin amfani da hannu da kuma tunaninsa.”
Darasi na biyu, an yi amfani da ayoyin Alkur’ani da hadisan manzon Allah domin jan hankalin Musulmi, domin su gane irin gatan da Allah Ya yi musu. Idan suka bi Allah da gaskiya, za su yi galaba, su buwayi duniya. Dubu abin da Umar ya ce a shafi na 18: “Me zai sa ku ji tsoron wata kasa duk kuwa da irin girmanta? Mun bar ku lokacin duniya tana cike da gaskiya; lokacin da takubbanku suke murkushe karya da kafirci. Ku ne mafificiyar al’umma da aka fitar cikin mutane. Kun kasance madaukakiyar al’umma da aka aiko don ku shiryar da al’ummun duniya. Shin wai ba ku karanta kur’ani ne?”
Domin karfafa wannan darasi, dubi amsar da aka ba Umar, a dai shafi na 18: “Ai yanzu komai ya canja, halin mutane ya canja. Yanzu ba a maganar wata ka’ida ko gaskiya. Tuni mulkin duniya ya subuce daga hannunmu. Mun fada cikin kangin bauta da mamaya, ba abin da ya rage a gare mu ban da fata.”
Wannan ke nuna yadda al’ummar Musulmi suke a halin yanzu, saboda sun saki Alkur’ani da Sunna, dalili ke nan kafiran duniya suka danne su.
Darasi na uku a littafin nan ya bayyana dalla-dalla bambance-bambancen da ke akwai tsakain Musulunci da Kafirci da sakamakon mabiyinsu. An bayyana bambance-bambancen da ke tsakanin zamanin Annabi Muhammadu (SAW) da na Sahabbansa da kuma zamanin karshen duniya. Darussan haka sun fito karara a shafi na 43 zuwa na 44.
Darasi na hudu, shi ne yadda aka fayyace wane ne Musulmi ko Mumini na kwarai, a shafi na 26. Darasi na biyar, an bayyana illar da tsoro ke haifarwa ga mutum shi kansa da kuma daukacin al’umma, a shafi na 30.
Darasi na shida, ya bayyana ne a shafi na 44, inda karara ake nuna yanayin al’umma cewa abu biyu ne ke haduwa su saita halayyar al’umma – wa’azi da kuma hukunci. Wato aikin malamai ne su fadakar, kuma aikin hukuma ne ta ladabtar. Dubi abin da Umar ya ce: “dana, akwai mutanen da suke wa’azi kadai ya ishe su, sannan kuma akwai wadanda ba sa gyaruwa da wa’azi sai an buge su. Ga ku Musulmi amma kuna halayyar Yahudawa.”
Shugabanci babban al’amari ne mai nauyin gaske, don haka darasin da littafin nan ke nunawa a shafi na 69 ya ta’allaka ne da nauye-nauyen da mai mulki ke dauke da su. Don haka wannan shi ne darasi na bakwai a littafin.
Darasi na takwas ya bayyana ne a shafi na 70, inda Umar ya nuna yadda ake cin abinci a musulunce da kuma ma lokacin da ake cin abincin. Hakan ke nuna cewa Musulunci cikakken addini ne mai tarbiyya ga dukkan rayuwa da dukkan abin da ake gudanarwa a cikinta.
Darasi na tara ya bayyana ne a shafi na 107, inda littafin nan ya bayyana mana yadda tsiraici da fasadi a duniya suka samo asali da kuma wadanda suka assasa shi, da kuma dalilansu na yin haka.
Darasi na goma ya bayyana a shafi na 148, inda Umar ke bayyana abin da ake so ga Mumini, yana cewa: “Ku kunna fitilar alheri da man ilimi. Ku lallausa zukatanku da yakinin imani, ku bice wutar kafirci da bata ta yin nadama da tuba; ku canja rayuwarku ku komo kamar ranar da iyayenku suka haife ku, masu tsarki, marasa zunubi. Sannan ku furta kuma ku rera madaukakin lafazi, wato ‘Babu abin bauta sai Shi kuma Muhammadu (SAW) manzonSa ne.”
A wannan zamani da muke ciki, Musulmi na cikin jarabawa mai girma, don haka littafin nan, a shafi na 168 yana bayyana mana abin da ya kamata mu yi domin tsira. Wannan ne kuma darasi na goma sha daya da hankalin mai sharhin ya kai kansa a wannan littafi.
Wadannan darussa goma sha daya, kadan ke nan daga cikin dimbin darussan da ke cunkushe a cikin wannan ingantaccen littafi, wanda ya dace da ingantattar fassara. An inganta littafin da bango mai kyau, mai santsi, mai daukar hankali. Sai dai duk da cewa an yi matukar kokari wajen amfani da ingantatta kuma daidaitattar Hausa, amma an samu zamiya da kura-kuran dab’i ko tuntuben alkalami a wurare da dama. Misali, wasu wuraren ba a yi amfani da haruffan Hausa ba masu lankwasa, a yayin da wasu wuraren kuma aka sanya su. Haka kuma littafin ba ya da lambar mallaka, wanda haka ke nuna cewa an yi wallafar-kashin-kai ne.
Ina shawartar al’umma da hukumomin ilimi da su mallaki littafin nan, musamman saboda dacewarsa wajen gina tarbiyya da sassaita tunanin al’ummar Musulmi. Haka kuma, ina ba mawallafansa shawarar da a nan gaba, idan an tashi sake buga shi, a aiwatar da gyare-gyare da kwaskwarima, domin a samar da ingantaccen bugu da ya dace da tsarin wallafa na duniya.