Muhimman gadoji uku a hanyar Wukari zuwa Jalingo na daf da karyewa

Manyan gadoji uku da ke kan hanyar Wukari zuwa Jalingo da ke Jihar Taraba na gaf da karyewa. Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa ruwan sama mai yawa da aka samu a jihar a bana ne ya haifar da ambaliya a manyan kogunan jihar, wanda ya sa sassan gadojin suka fada. Gadojin da […]

Muhimman gadoji uku a hanyar Wukari zuwa Jalingo na daf da karyewa
Muhimman gadoji uku a hanyar Wukari zuwa Jalingo na daf da karyewa

Manyan gadoji uku da ke kan hanyar Wukari zuwa Jalingo da ke Jihar Taraba na gaf da karyewa.

Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa ruwan sama mai yawa da aka samu a jihar a bana ne ya haifar da ambaliya a manyan kogunan jihar, wanda ya sa sassan gadojin suka fada.

Gadojin da suka lalace sun hada da wadda ke garin Namnai da ta garin Bambell a karamar Hukumar Gassol, sai kuma gadar Famfatir da ke karamar Hukumar Ardo-Kola.

A yanzu haka dai motoci na bin hannu daya ne da ke kan gadar saboda kasancewar daya hannun gadojin uku ruwa ya kwashe.

Wadansu daga cikin direbobin da ke bin hanyar sun nuna matukar damuwa dangane da lalacewar gadojin, inda suka ce gadojin na iya karyewa a kowane lokaci.

Wani direba mai suna Malam Yahaya Murtala ya bayyana wa wakilinmu cewa ba wai yawan ruwan sama ne ya haifar da bacin gadojin ba, har ma da dadewar da gadojin suka yi ba tare da an gudanar da gyara a kansu ba. Ya ce an gina hanyarWukari zuwa Jalingo ne a  1980, yau shekara 38 ke nan amma ba wata gyara da aka gudanar a kan gadojin.

Ya ce Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta dauki mataki cikin gaggawa don gyara gadojin domin a kauce wa asarar rayuka da dukiyoyi, da karyewarsu ka iya haifarwa.

Shugaban Karamar Hukumar Gassol, Alhaji Yahuza Ya’u ya nuna damuwarsa kan lalacewar gadojin. Ya bayyana cewa tuni aka kai rahoton wannan matsala ga Hukumar da Kula da Hanyoyin Gwamnatin Tarayya (FERMA).

Shi ma da yake magana dangane da matsalar, Mai martaba Sarkin Mutum Biyu, Alhaji Suleiman Duna ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gyara gadojin don guje wa asarar rayuka da karyewar gadojin ka iya haifarwa.